← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 7 OF 70

Sashe 7

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Bakiga mutane bane da zaki shigo ki samu waje kizauna kanki tsaye baki gaidasu ba?" Ummintata ta jefa mata tambayar da tafi kama da akwai wata a qasa kenan,a sanyaye tace
"Aina gaisheshi tun dazun?"
"Ok,shi yasa yanzu ba zaki qara ba kenan?" Kaita girgiza kawai dolenta a sanyaye tace
"Ina wuni?"sai daya sha qamshi sannan yace
"Riqe abarki kawai,tunda sai kinyi jayayya da na gaba dake sannan zakiyi abinda aka saki" wani 蓳acin rai ne taji ya riqe mata wuya,cikin ranta tace
"Wato ko dakin mamarka munafiki ya rigaka shiga sai kaga sauyin fuska,yanzu gashi babu gaira ba dalili daga zuwa ganin mamarta zai hadasu,bayan shi babu wanda ya hadashi da tashi mamar.

Miqewa tayi kawai tace
"Zuwa nayi yi miki saida safe"
"Allah ya bamu alkhairi" ta amsa mata ciki ciki,jikinta ya bata akwai abinda ke faruwa,akwai abinda ta yiwa ummin,saidai kanta ya kasa kawo komai,tubda ita dai tasan awanni kadan duka duka da dawowarta gia,don haka sawunta a likkafa ta fita a sashen.

A falo ta sami hajja ita da mariya da halima yaran wajen umma matar abba abu suna kallo,dubanta hajja tayi
"Kin dawo kenan?"
"Eh wlh....yunwa bari na samo abinci" tayi gaba da sauri zuwa cikin kitchen
"Ahto tun dazu nace ki tsaya kici ai" hajja ta fada tana gyara kashingidarta,ita dai zahra tuni tayi kitchen,ta samu faranti ta zuba abincin,sannan ta dawo falon ta zauna sosai saman carfet.

Kafin tayi lomar farko ta soma da bude data dinta sannan ta aje wayar gefanta ta soma cin abincin tana kallon wayar tare da jiran saqonnin su gama shigowa,duk da wasu sun yayyanke,wasu kuma waiting suke nuna mata,don haka basu jima ba suka gama shigowa tsaf,sai tasa hannun hagunta ta dauki wayar,daya hannun kuma tana diban abinci dashi.

Duk yawan sa茩onnin dake kan wayar bata bi ta kansu ba,sunan data sanyawa nuraddeen taje ta lalubo ta shiga inbox din tana qoqarin duba last seen dinshi ko kuma yana online.

Ga mamakinta saita ganshi online,dole tayi mamaki,don bata taba ganinsa online ba ba tare da ta tarda saqonshi ba koda kuwa na sallama ne.

Ba jinkiri ta rubuta slm ta tura mishi,yayi mata tick guda biyu alamun yaje,saita tsaya ta zubawa sallamar data tura din idanu kamar ba ita ta rubuta ba,tana jiran taga ta sauya launi zuwa blue,saidai kafin hakan ta faru ta lura daya sauka.

Goshinta ta dafe,sam sai takeji banbarakwai,wannan karon kamar nuradden din ya canza,tunda sam basu saba haka ba dashi,zama tayi sosai ta tura masa saqon cewa tayi fushi dashi,daga haka ta kashe data gaba daya ta maida hankalinta ga abincin,tana son ta gama ta wuce daki kawai ta kwanta gaba daya.

Da wayar da kwanon ta miqe gaba daya a hannunta,hajja ta dubeta
"Yau babu hirar dare kenan?" Fuskarta tadan yamutsa
"Wai so nake nadan huta,tun dazu nasoyin bacci ban samu dama ba" kai hajjan ta gyada
"Ya kamata.....yau banji duriyar nuraddeen ba?" Sai data dubi wayar hannunta sannan ta maida dubanta kan hajjan
"Nima yau na rasa me ya riqeshi haka,kwata kwata bamuyi waya ba"
"Ai yau da gobe sai Allah" bata ce komai ba ta juya ta wuce kitchen ta aje farantin sannan ta wuce dakinta,tasan me yiwuwa su salma nacan na jiranta zaman hirar dare yadda suka saba,idan kuwa basu jita ba zasu biyota ne sassan hajja ayi a nan yadda sukanyi mafi yawancin lokutta,ita kuwa yau sam bata jin wani karsashi.

Kaman jira yake ta gama gyara kwanciyarta saiga kiranshi ya shigo,murmushi ta sake cikin zumudi ta daga kiran
"Kimin afuwa ranki ya dade tuba nake" cikin shagwabar nan tata tace
"Aini tuni nayi fushi ma"
"Kimin rai,karkisa cikin daren nan na kamo hanya"
"Na yi maka" ta fada murmushi na qwace mata,yayin dashi kuma ya saki ajiyar zuciya yana cewa
"Kinsan duk duniya ke daya ce fushinta ke daga min hankali,gwara ran kowa ya baci,hankalin kowa ya tashi indai naki yana a kwance"

Farr tayi da idanunta cikin jin dadin yadda take da girma da matsayi cikin zuciyarsa,kullum kwanan duniya sake nuna mata matsayinta yake a wajensa,hakan yana mata dadi qwarai,tana jinta cewa itama takai mace,ba kamar yadda ko yaushe ya haidar ke nuna musu suna mata bane.

"Baby ina zuwa,minti biyu,mama tayi kirana zan kiraki"
"Kace ina gaisheta" ta fadi,bata ji amsarsa ba amma taji qit wayar ta katse,saita sauke wayar daga kunnenta tana murmushi,soyayyarsu da nuraddeen koda yaushe ta dabance a zuciyarta,gyara kwanciyarta tayi ta bude inbox nashi tana bitar saqonninshi da ita,fuskarta wadace da murmushi,ta jima a haka sannan taji hayaniyar 'yammatan gidan,tasan zuwan zasuyi su dasa hira,wala'alla ma idan nuraddeen ya kirata su hanata dagawa,don haka ta cusa wayar qasan filo ta runtse idonta ta gyara kwanciyarta kamar me bacci,tana jinsu suka shigo suka qaraci nacin tashinta suka haqura suka shiga hirarsu.

Tun tana jinsu sama sama har har bacci ya kwasheta.

Bata tashi farkawa ba sai da aka kirayi sallar asuba.

Misalin sha daya da rabi na safe ta gama dukkan abinda zatayi,tana gaban madubi tana qarasa kwalliyar fuskarta,bayan ta shirya kanta cikin wasu riga da skert na atamfa da suka yi mata cif a jikinta,abu na qarshe datayi gaban mudubin shine feshe jikinta da turare,ta kalli kanta ta tabbatar komai yayi,saita sakarwa kanta murmushi,saboda ita kanta tasan tayi kyau.

Hankalinta ta maida kan wayarta dake gefanta,tun daxun take trying number nuraddeen,tana son gaya mishi xata fita,don kada yace zayazo kuma bata nan,gwadawa ta sakeyi tana fatan ta sameshi,tun jiya da yace zaya kira bai biyo din ba,amma ta masa uzuri,mai yiwuwa basu gama magana da maman nashi da wuri bane.

Cikin sa'a wannan karon ta sameshi,sai daf da zata tsinke aka daga,muryarshi can qasa kamar mai bacci suka soma gaisawa
"Zan je gidan abban gwammaja ne nace bari na gaya maka kada kazo gida baka sameni ba"
"Ok,babu matsala,na tarad dake acan kawai"taji dadin hakan don tana da muradin ganinsa,amma saita boye murnar tata da cewa
"Ok fine,yayi" daga haka sukayi sallama ta aje wayar tana sakin murmushi tare da sake duban kanta sosai,nufar ma'ajiyar sarqoqinta tayita cire dan kunnen kunnenta ta saka sarqar da dan kunne harda abun hannu,wanda ada batayi niyyar sanyawa ba,data sake duban kanta sai taga kwalliyar ta sake qawatuwa fiye da daxun.

"Kince karna bata mana lokaci,kuma naga kamar kedin xaki bata mana" ta jiyo mitar salma daga can falon hajja
"Ina zuwa" ta fada da sauri tana daukar mayafinta dake saman katifa ta yafashi saman kafadunta,ta maqala hand bag dinta a hannu ta zura takalmi ta fito.

"Wannan mayafin fa salma?" Zahra ta fada tana duban salma
"Hmmmm...kin manta yaa zaki yana nan,baki nan ranar daya kora mana warning kan saka irin wadan nan mayafan,wai bama ganin zahransa,ita bata ishemu darasi ba" baki zahra ta tabe,zata ce wani abu hajja ta fito
"Ma sha Allah..." Ta fada tana duban kyawawan jikokin nata
"Amma innawuro ki koma ki canza mayafi" baki ta tabe kamar xata saki kuka tace
"Ni bani da wani babba irinsa da zai shiga da kaya na,don Allah hajja ki barni"
"Ni ina dashi,kije kibude adaka ta ki dauka nawa" dariya sosai zahra ta qyalqyale da ita,salma na dan tayata,sai data tsagaita sannan tace
"Haba hajja,haba don Allah,mayafinki fa?ai sai a nannademu duka nida salma a ciki,ki qyaleni don Allah,wannan ma meye aibunsa tunda ya rufemin duka baya na,kuma ba mai shara shara bane"
"To Allah ya baki sa'a,idan kuka hadu dashi ai kya dawo ki dauka ko ba don Allah ba" daga haka tayi gaba ta barsu
"Muje don Allah salma,su na fuskanci kowa ma bin dokarsa da tsoron fushinsa yake,kamar shine uban gidan gaba daya" ta qarashe xancan tana barin falon,salma tabi bayanta tana dariyar zancan hajja na zahra ta yafa aron mayafinta.

Sassan umminta ta nufa don gaya mata zata wuce,sai data tsaya daga baya ta bawa salma riqon mayafinta sannan ta shiga ta mata sallama ta fito suka wuce,salma nata tsokanarta Allah yasa su hadu da ya haidar,ita kuma tana ramawa
"拼ar baqinciki,bakinki ya sari 蓷anyen kashi" suna hira kadan kadan har suka isa bakin titi suka tsaya don samun abun hawa.

Tun daga nesa salma ta hangi motarshi,damqe hannun zahra tayi
"Xahra,ya haidar" ta furta idanunta na kan motar dake qara kusanto inda suke tsaye,duban wajen tayi,tabbas motarshi ce,to amma su ina ruwansu dashi,don haka ta zame hannunta daga na salma
"Ina ruwanmu dashi?,share kawai,karma ki nuna kin ganshi" daga haka taci mur ta maida fuskarta wani sashe,saidai kuma zuciyarta na dan bugawa saboda tsoro.
23/10/2021, 08:37 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 05

Masoya ga abdulrahamaan鉂わ笍
K鈥檃ramin yaro masoyi kuma mahaddaccin alqur鈥檃ni mai girma
Yana matuk鈥檃r son karatun alqur鈥檃ni duk kankancin shekarun sa, Ya haddace surorin alqur鈥檃ni da dama hizb biyu na ammah.

Dan Allah a shiga a danna masa subscribe, Aunties, uncles 馃グ馃グ A saurara a kalla a kuma sanyawa channel dinsa albarka 鉂わ笍鉂わ笍

Yaro k鈥檃rami yataso da zuciar son karatun Al鈥橯ur鈥檃ni mai girma. Kullum burin sa bai wuce a kyalla shi a camera yana rangada karatu cikin kira鈥檃rsa mai dadi, 馃憦馃徎馃憦馃徎
Toh yan uwa dan Allah a hanzarta a danna kararrawar subscribe ta tashar YouTube na ABDUL-RAHMAAN... 鉂わ笍鉂わ笍Domin samun sabon karatun da yai a duk sanda Aka dora 馃挐馃挐

Mungode kwarai da zab鈥檌n zafafa biyar..馃憦馃徎馃憦馃徎

https://youtu.be/NgqdCTVKOF8

Channel name Abdul-rahmaan.

He's a very young boy who's passionate about becoming one among the huffaz, he loves reciting the Holy Qur'an even at his younger age. He has memorized so many surahs within juz ammah.

please help him grow his channel fisabilillah and also pray for him to be come a Hafiz in future in sha Allah. Jazakumullah khair..

*KIJI TSORON ALLAH鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆綤ARKI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*

5

Cikin nutsatsen tuqi motar tazo ta giftasu,wata ajiyar zuciya zahra ta saki,can qasa muryarta tace
"Thank god....Allah ya tsaremu daga masifar wannan masifaffen" tayi maganar a afili sanda tasa hannu tana tsayar musu da dan adaidaita sahu,ba tare da tsayawa dogon ciniki ba ta shiga salma ta bita a baya tana cewa
"Addu'arki taci bai ganmu ba,Allah ya tsallakar dake".
Chapter 7 · 0% Book details