← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 57 OF 70

Sashe 57

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dukkansu suna falo harda me jego,suwaiba da badi'a,saisu anty aliya da suka zo suyar nama,idanun da sukayo kansu gaba daya sai taji kamar zata zube a qasa,kunya kamar ta kasheta,saita dinga mammazewa,ta qarasa cikinsu ta gaidasu,hajja ce dai sai data tura mata qeya sannan ta amsa.

Bayan sun gaisa haidar din yadan zauna a cikinsu anty aliyan,abinda yakan jima baiyi ba kenan,ba kasafai suke samun damar zamansa cikinsu ayi hira sosai ba,sai lokaci lokaci,hakan ya sanya zahra barin falon ta shige dakin hajja,don nata dakin su suwaiba su shige ciki.

Tana nan kwance hajja ta shigo dakin yakai sau uku,a fakaice take mata habaici a waqe anaso ana kaiwa kasuwa,irin salon waqoqin mutan da din nan,dadai ta gaji da habaicin hajja saita miqe ta fice tabar mata dakin.

Har yanzu yana falon shida anty aliya da anty nusaiba,zata wuce kitchen ta samu abinda zataci taji suna masa godiya,da alama ya musu irin alkhairin daya saba ne.

Inna gaje ce kawai a kitchen din,sai tayi zamanta kawai a ciki,ta hada mata abincin ta soma ci suna hira,ita dinma zancan haidar din take mata
"Ai gaskiya uwar masu gida kin dace,kinyi dace da mijin qwarai mai hannun alkhairi,inda ace shidin wani hamshaqin attajiri ne Allah ne yasan mutum nawa me zasuyi kudi ta sanadinsa,ko a yanzun ma ya zama inuwa ga mutane da yawa,saidai addu'ar Allah ya qara arziqi" murmushi ta yiwa inna gajen kawai,ta can qasan ranta sai taji zuciyarta na amsawa da amin............
23/10/2021, 08:48 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 37

*KIJI TSORON ALLAH,鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆綤ADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*

Washegari kuwa qaryar ciwo ta yiwa hajja bayan ta gama hada kayan da xata koma makaranta dasu a washegari,tayi kwanciyarta da wuri,duk da baccin bai dauketa ba amma tasha chart dinta,har daga bisani baccin gaske yayi gaba da ita.

Tunda ilham ta kawo masa abincin yace ta ajiye a nan,tsahon wani lokaci yana zaune,shi baici abincin ba,bai kuma ce a fita dashi ba,haka kawai duk yaji baya cikin sukuni,abincin ma baya sha'awa ci,xuwa wani lokaci sai gashi ya miqe,ya saka hannu ya bude dakin,ya leqa farfajiyar waje kamar me neman wani abu,daga baya kuma ya rufe qofan ya dawo ciki yana jan tsaki.

Gaban kwanukan abincin ya dawo ya soma saving kanshi,abinda ya jima rabon da yayi,tsakula kawai yayi yaji cikinsa ya cushe,saiya tura abincin gefe ya miqe ya nufi bakin fridge don dauko abin sha.

******** ***** ********

Tsaye take dakin hajjan rataye da qaramar jakarta,tana tsayen amma sai faman duba agogo take,tana so ta isa akan lokaci ne,akwai lecturer din dake nemansu,kuma tasan halinsa sarai,mtuqar ta wuce lokacin tofa ba shakka ko dawa take yawo ba zai bari ta shiga ba.

"Don Allah hajja ki sauri....zan makara fa" ta fada a shagwabe,saita rufe akwatin data bude din,ta miqa mata baqar leda
"Gashinan,ki tabbtar komai dake ciki kin shanyeshi kafin dawowarki gidan nan,Allah ya tsare....ina shi haidar din?"
"Munyi sallama fa,bacci yake,mustapha zai kaini" idanu hajjan ta tsareta dashi,bata yarda da zancanta ba,don tun jiya taga tana aiken yara suna siyo mata abubuwan da bata dashi a kantin layinsu da 蓷ai da 蓷ai,ta mata shuru ne kawai tayi kamar bata gani ba
"Motarsa kam dama ai wajen mustapha ta kwana,don ya aikeshi gidan innarku da safe zaije yakai mata saqo" qafa ta bubbuga
"Wai hajja yarda ne bakiyi dani ba"
"Na yarda dake,Allah ya kiyaye hanya" ta fada tana tattare kayanta data fito dasu,sanadin daukowa zahran abinda ta batan,ta san sarai indai baisan da tafiyarta ba bazai qyale ba,don baya daukan irin wadan nan abubuwan.

Sai data shiga ta yiwa duk mutanen gidan sallama,bata tarda mama ba ta fita tun sassafe dubiya,umminta dubu biyu ta bata,sai taqi karba,duk da ta yiwa account dinta tas saboda siyayyar data yiwa kanta da kanta,don kada ta tambayi haidar din,wanda tunda take bata taba yiwa kan nata siyayya ba sai wannan karon.

Gaban motar ta shige sanda mustapha ke kunna motar,ya tasheta suka fice daga gidan.

Tun basuyi nisa ba suka soma hirarsu yadda suka saba,cikin raha da zolaya,gab da zasu shiga farawa wayar mustaphan tayi tsuwwa,sai zahran ta xolayeshi
"Tun daxu ake faman kiranka,hala wata mai rabon wahalarce" ta fada tana sheqe masa da dariya
"Allah kinga makwancina da yawa.....ki zuba ido,sai nafi mijinki kudi,kibar ganin aikinmu har yanzu baizo hannu ba,hausawa suka ce gayawa wanda ya tara ya kiyayi me nema.....kai shine ma ke kira" ya fada yana zaro ido,sai zahran ta qyalqyale da dariya
"Qaryar kawai,ashema cika bakin naka bai kai ba,tunda gashi daga ganin sunansa kawai ya saka fargaba" hannunsa daya ya daga
"Na yarda wallahi....ke....kinsan soja kuwa....hmmmm" daga haka ya daga wayar,ya sanyata a handsfree.

Husky voice dinsa ce ta cika wayar,kamar bai jima da tashi a barci ba
"Kai kana ina?" Ya tambayeshi a dake,cikin girmamawa yace
"Gamu a hanya zan maida inna wuro makaranta"
"Waye ya baka izini?" Ya jefa masa tambayar data saka mustapha ware idanu yana duban zahra,wadda itama shi take kallo,dukkansu gabansu na faduwa,bai iya amsa mishi ba ya tsintoshi yana cewa
"Duk inda kuke ku dawo yanzu yanzun nan" daga haka 蓷if ya katse wayar,saiya soma neman wajen tsayawa,ya gangara gefan titi zaiyi reverse.

Kallonsa zahran tayi
"Wai komawa zakayi?" Girarsa ya dage duka yana kallonta sannan yace
"Eh mana....au so kike nace masa a'ah,tab....wallahi bazan iya ba,ke da kike matarsa ma bakice komai ba saini"
"To gaskiya malam tsaya na fita,na tari wata ta kaini,saboda indai banyi attending class ba daganan zuwa lokacin da lecturer din yace ba da wuya bai zame min matsala ba" lock yayi sauri ya sanyawa qofofin sannan ya fara reverse yana cewa
"Kinsan Allah ba xaki jawomin ba,ai kiyi haquri kawai na miqa masa ke da motar sa".

Kafin su isa gida kuwa mita da qorafi mustapha ya shata,kamar ma shine haidar din,shidai dariya yake sheqa mata
"Sai dana tambayeki ya san zan kaiki kika ce eh,to ashe ma ko sallama bakiyi masa ba,bayan kinsan halin guy din nan,ba'a canza masa ko take masa doka,nidai na kaiki lafiya shine kawai mafitata a wajensa" .

Suna shiga harabar gidan ya sake kiransa
"Ok" kawai taji yace,ya kashe wayar sanda xahra ke tambayarsa
"Me yace?"
"Yace nakai masa key din" haushi takaici da baqinciki ya cika,wato ita bata ga tsuntsu bata ga tarko,saita balle murfin motar ta shige sassan hajja.

A falo ta sameta zaune tana karyawa,ta dinga kumbure kumburenta da qunquni amma hajjan bata ce mata ci kanki ba,a haka har kusan awa daya,wanda tuni ta fara qwalla,sai ga husna ta shigo,tace wai ta fito inji ya haidar,jakarta ta figa tafita kamar jakarce tayi mata laifi,ko magana bata yiwa hajjan ba,ita kuwa hajja sam bata damu ba,murmushi kawai ta saka,saboda hango tarin nasarori daga wajen haidar,wanda ta tabbatar nasarar da zata samu akan haidar,ita zata kai har kan zahran.

Yana zaune gaban motar ya kamo sashen labari na bbc hausa yana sauraron labaransu na ranar,yayi masifar kyau cika da kwarjini cikin qananun kaya,idanunsa saye cikin wani sunglasses mai azabar kyau qirar wannan shekarar,wanda glass din ya qara masa kwarjini qwarai,jikinsa ba abinda yake fitarwa sai qamshi mai sanyi,wanda yacakuda da qamshin freshner na motar da sanyin ac dai wadda baya rabo da ita.

Tana shiga motar sanyin daya cikawa motar ya sanyata yin gulmarsa a ranta,taja murfin motar ta rufe,sannan ta waiwaya kadan tana gaisheshi,ko kallonta baiyi ba ya tada motar,ya jata da gudu suka fice daga gidan,saita lafe jikin murfin motar kawai,tana jin bugun zuciyarta yana sauyawa.

Shuru ne ya ratsa motar sanda yake tsala gudu dasu saman hanya,duk da suna cikin gari basu fita wajen gari ba,ta karanci shima gwanin gudu ne sosai a mota.

"Kin rainani ko?" Ta tsinci muryarsa yana fada a taqaice,dan waiwaya tayi ta dubeshi kafin ta dauke kai,kansa da idanunsa suka suna kallon titi ne,kasa amsawa tayi,sai tayi shuru tana murxa yatsunta kamar yadda shima yayi shurun,kamar bazaice komai ba kuma saiya bude bakinsa gently yace mata
"Ko auren uwaka ubaka mukayi dake auren tasha nidin mijinki ne,kinda da haqqi wuyana kamar yadda nima nake da haqqi wuyanki,bare ma aurenmu yafi gaban nan,koda bakiso bani so,koda babu shaquwa a tsakaninmu,tunda iyayenmu mutane mafi daraja a rayuwarmu su suka daurashi,fita babu izinin miji haramunne kuma ba dai dai bane....sannan komai niya kamata na zama a sahun gaba wajen sani kafin kowa.....so please.....please kada ki sake,idan ba haka ba saina daure qafafunki a inda ake daure qafafun marasa ji irinki" maganganunsa sunsa jikinta yayi sanyi,saita tsinci kanta da furta
"Kayi haquri" softly,wanda hakan ya bashi mamaki,sai kuma yaji dadi har cikin ransa,kamar yadda itama mamaki ya kamata,tayi tunanin zai balbaleta da fada ne har yayi ma kamar zaya daketa,kamar yadda yake musu acan baya idan sukayi laifi,ko kuma zai gaggaya mata magana,ko yace ta tafi a motar haya,a haya suke hangen halinsa,mutum mai kushin hali fushi da fada,kafiya da taurin kai,amma sai taga duka baiyi ko daya ba,ya gaya mata magana ce ta hankali,wanda duk me hankali ta isheshi ya fahimta cikin ruwan sanyi,basai an qara masa da wani abun daban ba.

Bata yanke daga wannan tunanin ba taga ya tsaya qofar wani babban kanti,wanda ya hada komai da komai,kusan komai.na buqatar yau da kullum da amfanin rayuwa suna saidashi
"Wait" kawai yace yana cre set belt din jikinsa ya bude motar ya fita ya nufi shagon,saita bi bayansa da kallo,yana yin yadda yake taku cike da nutsuwa qasaita da ginshira,sai daya shige sannan ta dauke idanunta a hankali tana sauke ajiyar zuciya,yaushe ya haidar ya sauya?,yaushe yayi laushi,to amma ita game da yadda yake mu'amalarsa da yaran gidansu bataga sauyi ba,donko ranar suna sai daya yiwa su salma fata fata kan sunkai dare,kuma mazansu sunzo daukarsu kowacce ta shanya mijinta,har kusan kuka sukayi.

Babu jimawa taji an bude set din baya,shine riqe da babbar leda ya sakata a bayan motar ya rufe,sannan ya dawo set dinsa ya shiga ya sake tada motar.
Chapter 57 · 0% Book details