← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 70

Sashe 41

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

_*ZA鈥橝 FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU*._

_*GIRKE GIRKE GUDA 30馃槴馃槰AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI馃WATA DAYA CHAS ZA鈥橝YI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN.*_

_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN馃憞馃従RIGIJI GABJI*_

_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!*_

_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar*_

_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA*_
_____________________________

Tsayawa tayi a tsakanin dakunan da falo tana kalle kalle,tare da tunanin me ya kamata tayi,tabbas kome hajja zatayi mata saidai tayi mata amma ba zata taba yarda ta shiga dakinsa da sunan kwana ba,sai kace wadda ake neman kai da ita?,ko kuma itace mijin shine matar?,sam bazai yiwu ba,saita qarasa ficewa,ta isa wajen tvn da dazun musty ya kashe ta kunna,ta koma kan kujera ta zauna tana rungume pillow gami da sauya tasha.

Kusan a qalla awa daya ta kwashe a zauna,gidan ya dauki shuru,sai tsoro ya fara cikata,don haka ta kashe tvn ta miqe a hankali ta nufi dakin nasu.

Sadaf sadaf ta tura qofar dakin,yan nan da duhunsa da alama kashe qwan hajja ta sakeyi bayan fitarta,saita kunna fitilar wayarta ta haska a hankali ta isa bayan hajjan tayi kwanciyarta nesa kadan da ita,ta tofa addu'o'in baccinta ta rufe idanunta tana addu'ar kada Allah ya farkar da hajjan.

Washegari tana kallon yadda hajjan ke maka mata harara,saita maze ta kuma dauke kai kamar batasan abinda ke faruwa ba,tasan idan tayi fushinta ta gaji dole ta sauko,shirye shiryen tafiya wajen gabatar da taron ma saiya janye hankalinta zahran ta sake samun sukuni.

Fitowarta daga wanka sukaji ana kada qaraurawar qofar falon
"Kai wannan abu sam babu hikima a ciki,wai wannan iblishiyar abar ke gaya maka kayi baqo....ke zahra'u...jeki ki duba kiga waye" hijabinta ta zura saman zanin jikinta ta fita falon.

Samuel yaron gidan ne tsaye bakin qofar,gefansa wata matashiya ce wadda a qalla zasuyi sa'anni da zahran,saidai xata iya baiwa zahran shekara uku tazarar shekaru uku kenan a tsakaninsu,fara ce sol,hakanan a kallo daya zaka fahimci 'yar gayu ce,asalin gayu kuwa,ganin farko xaka fadi halinta na yawan fara'a,donko a yaxun ma fuskarta a washe take da fara'a,har haqorin makan dake bakinta yana bayyana,tayi ado sosai da wani irin lace,takalmi da jaka masu aji gami da mayafi daya dace da shigarta,hannu da wuyanta duka kayan qawa ne na mata,da alama bata wasa da kwalliya
"Madam....matar abokin yallabai ce,yace ayi mata iso" samuel ya fada da gurbatattar hausarsa,saita saki fuska tana matsawa gefe gami da cewa
"Bismillah,ki shigo,su hajjan suna ciki"
"To na gode"ta ambata cikin fara'a tana shigowa,zahran tayi gaba tana biye da ita a baya
"Bismillah....zauna,bari nayi musu magana" ta fada tana nuna mata wajen zama,cikin fara'a ta soma zama tana cewa
"Ok to....amma ba kece amaryar oga haidar ba?" Rasa amsar da zata bata tayi,bai kyautu tayi mata qarya ba tunda batasan matsayinta da kuma zancan da sukayi ba,sa'annan kuma hannu guda bata son amsa sunan matarsa sam,saita gyada kai cikin murmushi
"Eh"
"Ma sha Allah....hala kai ya dauki chargy bai gaya miki zuwa na ba....nazo ne zamu wuce tare daku can wajen taron,tare da yallabai zamu tafi,so kuma an kirasu babu damar su dawo gida su shirya din mu wuce tare,sai yace kawai nazo mu wuce tare daku....ni matar abokinsa ce kuma abokin aikinsa da za'a qara musu girma tare,sunana dr nasreen" dole ta dawo ta zauna cikin fara'a,tunda da alama su din basusan komai kan aurenta da haidar ba,bai kamata kuma ta nuna komai din ba
"Ni sunana zahra.....ya gida ya yara" murmushi ta sakeyi
"Gida lafiya lau,yara kuma tukunna"itama sai tayi murmushi
"To Allah ya kawo masu albarka"
"Amin summa amin na gode" dole ta miqe ta nufi kitchen da kanta,abinda bata gwada ba ko sau daya tunda sukazo gidan.

Tayi mamakin ganin kitchen din,ya hada komai da komai na buqatar girki,ta bude fridge ta debo ruwa da lemo ta hado da tea da aka dafa tun dazun a flask da sauran farfesun kayan ciki ta aje mata,sannan ta wuce ciki kiransu hajja.

Ta fito da kayan akwatinta duka tana duba wadanda zata saka,ranta a bace kawai yake,banda zuwan nasreen da kuma idanun hajja itafa babu inda zata je.

Hayaniya ta fara ji daga falon ta dadu,da kuma muryoyi kamar na 'yan gidansu,kafin tace wani abu hayaniyar taji ta doso dakin da take,hafsat ce kan gaba dauke da babynta,sai salma a bayanta itama da nata baby boy din da tuni ya soma tafiya sai yusra daga qarshe.

Rungume juna sukayi cike da murna,sosai taji dadin zuwansun,abinda yaso sasu su bata ma tsokanarta da suka fara yi,Allah ya yanke abun ta hanyar shigowar nasreen,wadda hajja tace taje wajensu sai tafi jin dadin zama.

Hira suka shiga yi inda ita kuma ta hau shiryawa cikin wani lace army green da yayi masifar haduwa,dinkin riga da skert daya zauna mata sosai a jiki,tana shiryawa tana sauraren hirar tasu,da alama itama dr nasreen 'yar hira ce,hakanan bata da wahalar sabo,don kuwa idan ka ganta a lokacin saika tsammaci ta dade da saninsu,cikin qanqanin lokaci suka saba da ita.

Tana gama shiryawa dukka suka rude da zolayarta kan irin kyan data yi,haushi ya cikata ta kasa magana,bugu da qari kuma ma da idanun nasreen dake wajen,wadda ke zaune gefe tana ta murmushi tana kallonsu,yanayin zamantakewarsu da hadin kansu,yadda suke haba haba da juna,da alama akwai saboda shaquwa mai qarfi a tsakaninsu.

Motoci uku masu tsananin kyau da tsari ne suka debesu daga gidan aliyyu haidar zuwa inda za'a gabatar da taron a babbar headquater sojoji dake garin abuja.

Tun daga waje xaka fahimta lallai babban taro ake,abu nasu maganin a kwabesu,ko ina jami'aine dake bawa wajen tsaro da kariya,tako ina komai na tafiya kan tsari,duk abun mutun idan yaga tsari da yanayin wajen sai yaji sun masa kwarjini,lallai soja ba wasa bane,dole ya haidar ya dinga yi mana kwarjini tanaji su salma suna fadin hakan,ita dai nata idanu ba tare da tace komai ba.

Babban wajene budadde wanda aka tanada saboda taro irin wannan,kujeru ne bisa tsari,wajen baqi da manyan baqi daban,wajen zaman sojojin dama wadanda za'a qarawa girma daban.

Suzo akan lokaci ne,hakan ya sanya suka samu waje mai kyau da zasu iya hangen dukkan yadda abubuwan zasu wakana,wanda hafsat ce ta haura ta hango musu ta jasu wajen suka zauna
"Da kyau hafsat,gaskiya kin iya zaben wajen xama,xanga dear da kyau wallahi" cewa dr nasreen tana gyara zaman hand bag dinta tare da gyara zamanta da kyau,wanda zamansu babu wuya wajen ya soma cika da jama'a,aka kuma fara gabatar da 'yan wasu abubuwan kafin a shiga muhimmin taron.

*_BAYAN SHUDEWAR WASU MINTUNA_*

Mai gabatarwa ne ya amsa abun magana ya tabbatar da wajen ya hau tsari bisa doka da yadda suke gabatar da tarukansu,take wajen ya dauki saiti,kowa ya bada hankalinsa kan abubuwan da aka soma gabatarwa.

An yiwa manyan baqi maraba da zuwa,sai parade na musamman ada aka shirya saboda su,sai da aka fara gudanar da parade din sannan zahra tadan dago daga danna wayar da takeyi ta dubi wajen.

Sai abun ya dauki hankalinta fiye da yadda ta zata,don wannan shine karo na farko da aka fara parade a gabanta,a nutse take binsu da ido,yadda suke komai a nutse sannan kuma a tare,duk wanda yake wajen sai abun ya bashi sha'awa ya kuma qawatar dashi,musamman idan shi din ba ahalin abun bane.

Suna kammalawa wadanda zasu karbi qarin girman suka soma shigowa da daya da daya,kusan inda ta zauna din yana kallon inda aka tanadar musu domin zama,sannan kuma daura da wajen qofa ce,hakan ya bata damar ganin duk wanda zai shigo din.

Mutum na shida ne ya shigo
"Oh god dear.....yau ka canza sosai" taji de nasreen na fada cikin wani irin exciting,tadan kalleta kadan sanda take daga yatsunta,saita maida hankalinta ga wanda ke shigowar,ga mamakinta ya hangi matar tasa,shima kuma yatsunsa yake daga mata a fakaice,sai taji ta aika masa da kisses ya kuma dawo mata da amsa sanda yake samun waje yana zama fuskarsa dauke da wani irin murmushi.

Murmushi tayi itama wanda ya tsaya iya cikin zuciyarta,ko ba'a fada mata ba tasan cewa dr nasreen da mijin nata narkakkun masoya ne,idanu kawai sun isa baka amsa,tana shirin dauke idanun nata daga wajen ta hangi shigowarsa,wanda shigowar tasa tayi dai dai da sakin wani take daya dauki hankalin jama'ar dake wajen.

Taso qaryata idanunta da suka nuna mata yadda shigar kakin dake jikinsa ta amsheshi fiye da duk wani wanda yake sanye da kaki dake wajen,hakanan taso qaryata kanta data hangi zallar kwarjini dake kwance saman daurarriyar fuskarsa da ayau tadan sassauta daga yadda aka santa zuwa matakin daurewa na qasa qasa,batasan kaki na yiwa mutum kyau ba sai a lokacin,saidai ta alaqanta hakan da cewa rashin taba ganinsa cikin shigar da bata taba yiba yasa dukka taga hakan,saita janye qwayar idanunta sanda shi kuma nashi idanun ya sauka a kanta ba tare daya shiryama hakan ba,ya lura da dr nasreen daketa aikawa lieutenant jafar kallo wanda a yanzu xai koma matsayin captain,saiya lumshe idanunsa gami da yin bismillah ya zauna a mazauninsa.

Yanayin yadda taron ke gudana kawai ya isa ya sanyawa mutum nutsuwa da sha'awar ganin dukkan abinda ake gudanarwa a wajen,hakan ya sanya ta jefa wayarta a jaka,ta tattara dukka hankalinta a kan abinda ke wakana.

Hakanan lokaci zuwa lokaci idanunta na sauka a kanshi,kusan tunda ta sanshi bata taba ganin fuskarsa a sake haka ba,duk da ba dariya ko murmushi yake ba,tana jin su salma na gulmarsa,itadai batace komai ba,ganin haka hafsat ta tabo ta
"Wai yau bakiga fuskar sojanki ta saki ba?" Harara ta watsa mata tana dauke idanunta,daidai sanda suka hada idanu,saiya dauke kansa gami da sake daure fuskarsa,yadan juya kadan yana yiwa lieutenant jafar magana qasa qasa.
Chapter 41 · 0% Book details