← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 70

Sashe 16

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ringin uku aka daga,habibune ya soma magana
"Ango ango,ka sha qamshi"
"Chief tailor....yaya akayi?"
"An gama dinkin babbar rigar daurin auren fa"
"Kai amma naji dadi daka cika alqawari,don inason na kaita bugu ne"
"Yaushe to zaka shigo ka karba?"
"Zuwa anjima haka zanje gidansu amaryar,zankai mata invitation lokaci ya qure bata fara rabo da wuri ba,zan qaraso nan wajenka saina amsa din"
"Shikenan,a tahomin da nawa IV din,saura kwana nawa ne?"
"Rana ita yau in sha Allah"
"Ango ango,to Allah ya nuna mana"
"Amin amin,na gode" daga haka ya yanke wayar yana duban salim.

Tuni zahra ta dora hannayenta a fuskarta tana kiran sunan Allah,wai da gaske nasir shima ya yaudareta?,da gaske shima nasir aure zaiyi?,yarinyar da aka bashi zai aura ko wata daban,idan wadda aka bashi ce ai ba garin take ba,to amma yanzun cewa yake zaije gidansu amarya....me hakan ke nufi?,wai meke faruwa da ita ne?"saita miqe kawai ga nufi dakin hasina tana jin jiri yana dibanta,tana shiga ta maida qofar ta rufe don kada ma wani ya biyota,ta samu gefan gadon hasinan ta zauna,saita saki kuka a hankali hade da sheshsheqa.

Kamar wasa sai gashi a ranar kwanan gidan abban gwammaja ya kamasu saboda wani matsanancin ciwon kai daya saukar mata,umma ce ta dinga aikin bata maganganu,da kuma kwatanta mata cewa matar mutum kabarinsa,tayi addu'a idan har ya zalunceta Allah ya fidda mata haqqinta,tana jinsu sanda suke waya da umminta,sai kuma washegari bayan sallar magariba abubukar yayanta yazo da kanshi ya daukesu ya maidosu gida.

Saidai suna shiga bangaren umminta yace ta wuce,ta sameta a falo a zaune,suna hada idanu ta fahimci akwai damuwa qasan ran ummin da take boyewa,saita qarasa a hankali ta zauna gefanta tana gaidata,ta amsa sannan ta dora da cewa
"Ki tsananta addu'a,duk abinda kaso Allah kuma bai baka ba tabbas ba rabonka bane,qila ma ba alkhairi bane a rayuwarka,tashi ki tafi,Allah ya kiyaye"
"Na gode" tafada tana miqewa zuwa sassan hajjan.

Data shiga bata samu hajja ba,saita wuce dakinta,saboda yadda kanta yake sara mata,har yanzu kunnuwanta na jiye mata sanda habibu ya kira nasir din,yake gaya masa saura sati daya daurin aurensa,tana iya jiyo kamar wani sauti mai kama da zumudi zumudi cikin muryarsa,babu alamun bacin rai ko damuwa tattare da sautinsa,saidai bata jima ba hajjan ta shigo cikin jimami,inda ta takura mata sai data tattara ta zuwa dakinta,tace gwara su zauna tare har ta samu sassauci.

Saidai kuma abinda ya bata mamaki shine,a daren ranar saiga nasir ya kirata,kamar ba zata daga ba sai kuma ta daga,don tunda abun ya faru tsakanin jiya da yau bai kira ba sai yanzun,tana son taji da wacce kalma shi kuma zaiyi amfani?,me zaya fada?,zai kare kanshi ne kamar yadda nuradden ya kare?,ko kuwa zai tabbatarwa da kansa laifinsa?.

A yanayin sallamarsa kawai ta fahimci baisan mai afkuwa ta afku ba,da irin salon daya saba yi mata magana yayi mata,sai daya gama sannan a hankali tace
"Ango" dif yayi na wasu sakanni sannan yace
"Wanne irin wasa ne wannan zahra?,waye kuma angon?" Wani bacin rai ne ya taso mata,wato ita zaya ninke a baibai kenan?ya shirya saidai kawai taji an daura aurensa?,saita miqe ta zauna tana tuna irin kalaman daya jima yana amfani dasu a kanta,tana tuna yadda yake nuna kaffa kaffa da zallar kishi a kanta,tana tuna yadda koda yaushe yana tafe da kyaututuka domin ta,wanda koda taqi amsa zai tilastata ta karba din,zaice tukuicin soyayya kenan kyauta,ashe babban tukuici yana tafe
"Nasir....bude kunnenka da kyau!,idan zaluntata kasoyi to ubangiji yamin kariya da katanga dakai saboda ya bayyana min gaskiyar abinda kake boyewa,ka zalunceni nasir!,kaso ka yadaureni kaje kayi aurenka ba tare da na sani ba?,to na godewa Allah daya bayyanamin shirinka" cikin wata rudewa da dirircewa yake cewa
"Calm down fatima....ki tsaya kiji mana,wallahi Allah ba haka bane,yarinyar nan auren hadi akayi mana da ita.....zabin hajiya da alhaji ce....."
"Watanni nawa?,kwanaki nawa?,amma kullum nuna min kake bata da muhimmanci a wajenka?,hakanan maganar itama bamai muhimmanci bace?,ka gayamin cewa ka gamsar da hajiya ta aminta da naka zabin,amma abun mamaki saiga sauti farinciki daga maqogwaronka kana sanarwa da duniya daurin aurenka,a hakan zakace baka ita akayi?,ahaka kakeso na yarda dakai,bayan an ganemin babu wani damuwa ko kadan tattare dakai?"
"To naji,amma fatima....ina sonki ki yarda dani.....kuma in sha Allah zan aureki a matsayin matata ta biy....."
"Allah ya tsareni da hada hanya da mayaudari....har abada ni dakai nasir na barka kenan,kaje....ina roqon ubangiji yayimin sakayyar abinda kayimin,Allah ya isarmin" daga haka ta kife layin ta sake sakin kuka.

Kuka tayi mai yawan gaske,wanda kafin tayi controlling kanta fa sassauta kukan nasir ya hada mata massages da kiraye kiraye babu adadi har ta kasa irga yawansu,sai kawai ta kashe wayar baki daya ta cusata qasan filo.

A ranar ta balla layin shima kamar yadda ta yiwa nuraddeen,hakanan ta kawar da duk wani abu da tasan zai tuna mata dashi,ta baiwa kanta qwarin gwiwar ci gaba da rayuwa,da kuma fuskantarta,tana mai burin haduwa da kyawawan sakamako a nan gaba

_saidai ina!,kowanne babi na rayuwa tafe yake da qaddararsa,saidai kuma DUKKAN TSANANI YANA TARE DA SAUQI!_

Duk da ta cinyewa ranta komai amma hakan bai hana rama bayyana a jikinta ba,saboda ita damuwa tana da tasirin bayyana gangar jiki koda an danneta a ruhi,hakan yasa ta fa蓷a sosai kafin komawarta makaranta.

Wannan karon hajja da kanta tayi mata tayin zama a gida ta qara koda sati daya ne ta qara murmurewa kafin sannan amma tace a'ah,saboda jarabawar qarshe ta wa'ec da neco da suka fara jiyo qamshinta,gwra ta tattara hankalinta ta samu sakamako me kyau,don yadda qaddararta ta fara zuwa mata a hagunce ya sanyaya mata jiki.

Da yammacin ranar ana ya gobe zasu tafin haidar ya iso gidan,tana falon hajja tana goge sauran kayanta da zata wuce dasu yayi sallama falon ya shigo.

Kai ta daga ta dubeshi na sakan daya kana ta amsa tana maida kanya ga gugar,har yanzu yana nan da gayunshi kwarjini izza da isa,saima cika da 'yar qiba da kuma murjewa daya sakeyi,hakan ya qara masa kyau sosai,kusan watansa biyu baya nan,sai yau ya dawo.

A sanyaye ta gaidashi,sannan ta tattare gugarta ta wuce ciki tabar falon,duk da haka sai data fara biyawa ta dakin hajja ta gaya mata isowarshi sannan ta fito ta koma dakinta ta barta tana ta murna da zumudin dawowar jikan nata,wanda babu yashi cikin jikokin nata,kasancewarsa jika na farko a wajenta,mai kuma yawan kula da ita da damuwarta,tamkar shita haifa ba mahaifinsa ba.

Wannan karon ma ta fito zata sha ruwa a kitchen taji hajjan na gaya masa abinda ya faru da ita,itakam bataso harga Allah hajjan na gaya masa
"Allah ya sawwaqe" kawai taji yace,qwafa taja a ranta tana cewa maganin hajjan da take gaya masan,aiba matsalar data shafeshi bace dama.

Basu jima da komawa ba lokacin visiting yayi,wanda su shine na qarshe d za'a musu saboda jarrabawa da zasu fara gab da lokacin ziyarar ko kuma bayan lokacin,sun wuni cikin farinciki,kamar yadda aka sani cewa rana ce ta farinciki ga kowanne dan makarantar kwana,wannan karon 'yan gidansu da iyalan abban gwammaja da wuri suka koma,don haka ta dawo hostel abinta.

Gab da zata isa gadonta ta hangi ladifa hamza zaune riqe da takarda cikin hannunta,gefanta kuma maryam mustapha ce riqe da hannun ladifar dake digar hawaye.

Ba laifi suna zaman mutunci sosai dasu,kasancewar zahran mai faran faran da jama'a yasa take da yawan jama'a,banda yanzun da walwalarta taja baya ba kamar da ba,don ko da take shugabar dalibai kusan iya mu'amalarta yasa dalibai ke sonta,musamman juniors da bata yadda a zaluncesu ba don suna qasa dasu,hakanan suma basu isa su raina na sama dasu ba dole su basu girma.

"Allah dai yasa lafiya ladifa"
Maryam ce ta buda hannun ladifan ta ciro takardar ta miqawa zahra,ba bata lokaci zahran ta bude ta soma karantawa.

A hankali ta koma gefansu itama ta zauna tana fidda murmushi mai ciwo,wanda iyakarsa saman labbanta,ta ninke takardar sannan tace
"Ashe bani kadai bace ba?,bani daya keda irin wannan matsalar ba,gayamin ya kuke dashi" muryarta da sautin kuka take bata labarin yadda yake nuna mata soyayya,amma sai gashi tashi guda ya yaudareta,yayi aurensa ba tare ma data sani ba,sannan kuma saboda tsabar qwarewa yaci gaba da soyayya da ita,sai a yanzu data kusa tonashi ya bayyana mata yayi aure a sanda suke tare,ya tsallaketa ya auri wata,bayan ta kori kowa a kansa,bata sauraron kowa saishi,wannan wanne irin yaudara ce?,wanne irin cin amana ce?.

Kai zahra ke gyadawa sannan ta basu nata labarin,shuru koqacce tayi,a hankali maryam tace
"Bansan me samarin yanzu suka koma ba,sam.basu da wata AL茦IBLA ko manufa a rayuwarsu,ya kamata muma 'yammata muyi karatun ta nutsu,mu daina basu yarda amanna da dukka soyayyarmu,da wahala ka tara yammata goma baka samu takwas a cikinsu suna da tabon yaudarar namiji ba,yaudara taban haushi,imma yaqi aurenki haka kawai saboda ranshi ya raya masa haka,ko kuma ya gujeki saboda ya nemi ki bashi kanki kinqi" kai zahra take gyadawa kawai,duk sanda ta tuna nuraddeen da nasir sai taji ranta ya sosu,abu daya data sani shine,a koda yaushe daka cuci mutum gwara shi ya cuceka,kuma sakayya yanzu tun a duniya Allah yake yinta.

*_IBRAHEEM_*

Bayan dawowarsu hutu babu jimawa suka zana jarrabawar fita daga makaranta,cikin iko da taimakon ubangiji,duk da irin qalubalen da suka dinga kawo mata tarnaqi amma hakan bai dakushe karsashi da karatunta ba.

Ranar da suka kammala aka kuma hada taro na yayewa da kuma sallamarsu,ranar ta zama ta musamman kuma me dimbin tarihi a wajen zahran.

Ranar da sai da tayi kuka na farinciki,saboda tarin kyaututtuka da kuma yabo data samu,kyaututtukan da wasu ma bata zacesu ba.

Kyauta ta qarshe data samu itace wadda daliban makarantar suka hada mata,saboda yadda sukaji dadin shugabancinta,da yadda ta tsaya tsayin daka akansu wajen kwatanta adalci da gaskiya.

Tana rungume da kyautar suka sake hada ido dashi,wannan shine kusan karo na biyar,duk sanda ta hau step din ta amsa kyauta tazo saukowa saita tsinci idanunshi a kanta,qaramin tsaki taja tana jin haushi har cikin ranta,ita sam ta tsani dabi'ar kallo,bama kuma kamar yanzun data yanke tsammani wa maza,tayi musu kudin goro.
Chapter 16 · 0% Book details