← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 64 OF 70

Sashe 64

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Kuka take sosai amma shi murmushi ne ke fita saman fuskarsa duk da yana jin kukan yana sukar zuciyarsa sosai,ya sani akaran kansa cewa bai raga mata ba ko dis,amma ya ya iya da ranshi,zai iya cewa ba laifinsa bane,tana maqale da ita kamar wanda aka ce masa za'a qwaceta,zallar sonta sabo fil yake kwarara cikin ranshi,kamar ya ciro zuciyar tasa gaba daya ya bata kyautarta,ba irin lallashin da baiyi mata ba,gashi har sha biyu da rabi na dare ta hanasu barci,shi da kansa ya gasata sosai,sannan ya barta tayi wankan,data gama shiya taimaka mata ta fito,amma wajen shiryawa fir taqi yarda,sai baya ya juya mata yana dariya ciki ciki yabarta ta shirya da kanta,ko a yanzunma da take kwance cikin jikinsa sai daya mata fin qarfi tukunna,baisan me zai sanyata tayi shuru ba,duk da ya lura irin shagwabar da takema hajja yau take sauke masa,shagwabar da abaya idan yaga tanayi yake aike mata da saqon harara ko tsawa,sai gashi yau yasa hannu bibbiyu ya amsa
"Kona kira miki hajjan?" Ya fada qasa qasa,da sauri ta maqale kafada,saita cusa kanta cikin qirjinsa tana sassauta kukan nata,ita kam waya aiketa da wata hajja?,tazo ta tijarasu kota titsiyesu da tambayoyi?.

Cikin salon qwarewa da dabara hannunsa saman sumar kanta ya dinga kashe mata jiki,har wani bacci mai nauyi yayi awon gaba da ita,wanda cikin baccin ajiyar zuciya ta dinga saki,sai daya tabbatar baccinta yayi nisa sannan ya sauketa a hankali,ya dora mata kanta saman pillow ya rufa mata duvet,sannan ya soma gyara mata sumar kanta yana kallon fuskarta,fuskar zahransa,murmushi ya subuce masa daya tuna tsiwa irin ta zahran,amma yau bakinta yayi laushi sosai,duk da cewa dama ta jima da canzawa,abubuwan da suka faru dazun suka dawo masa,rakin data dinga yi,magiyarta da ban hanqurin data dinga masa tana cewa ba zata qara ba,shi kuma yana tambayarta ba zata qara me ba,dukkansu shida ita ya tabbatar mahaukata suka zama tuburan,ita ciwo ya isheta,shi kuma duniyar data jefashi ne yasa ya kasa fahimtar komai.

Sallah ya sauka yayi yana miqa godiyarsa ga Allah,ya sani cewa ubangiji ya gama masa komai,sai kuma neman taimakonsa kan bauta masa da tsare haqqoqinsa,sannan ya kuma ya shiga lamarin xamantakewar aurensu,ya bashi ikon da zai riqeta bisa doron shari'a,kan gaskiya amana tausayi da kyautatawa.

Tana bude idanunta dashi ta soma tozali,ya sanyata a gaba yana qare mata kallo,saitayi rub da ciki da sauri tana boye fuskarta,yana murmushi shima ya haye bayanta,ya aza mata nauyinsa yana cewa
"Good morning zahraty amarya" sosai ya bata kunya bayan wadda takeji,nauyinsa takeji sosai,musamman idan ta tuna waye ya haidar a wajensu,amma gashi dare daya ya sauya komai a tsakaninsu,kamar bashi ba,kamar wani aka canza musu dashi,bata taba ganin fuskarsa a yanayin data ganta ba tsakanin jiya da yau.

Sai da yayi da gaske sannan ta miqe ta fuskanceshi,ya dinga tsokanarta,ya hanata sakat,ita kuma kunyarsa kamar qasa ta tsage ta shige ciki haka ta dinga ji,bai qyaleta ba yaci gaba da bibiyarta duk inda ta saka qafa cikin dakin,saidai bai fiya magana ba,amma ayyukansa na gaya mata komai,shi ya hada mata ruwa ta sake wanka,ya gyara dakin da kansa,don yace harsu tafi babu masu sharar da zasu sake shiga musu dakin,tayi mamakin yadda ya iya aiki da kansa,ashe dama a baya rashin ganin dama ne?,ko kuma sune basu fuskanceshi ba,itakam mamakin sauqin hali irin nasa take,komai nashi a sauqaqe yake yinsa,babu zafin nan,babu izzar nan da suke zatan masa ita.

Wayarsa ce tayi qara,ya qaraso ya daga,hajja ce take kira,bayan sun gaisa sai tace
"Lafiya na jiku shuru yau?"
"Eh...itace bata jin dadi sosai,ta sha magani ne,tana kwance" duk da ranta ya bata wani abu amma sai bata nuna ba,kawai tace
"Ayyah,qila tafiyar jiya ce da haka kawai ka kwasa mutane....ni dinma qafata ciwo take sai dana shafa magani,to Allah ua sawwaqe,ya bada lafiya"
"Amin amin" yana dubawa yaga harta kashe wayar ma,sai ya saki murmushi suka hada ido da zahra,itama murmushin kawai tayi,addu'a dama take kada Allah yasa asirinsu ya tonu wajen hajjan,sai gashi bata gane ba
"Ko zakije ku gaisa?" Ya fada yana kashe mata ido,kafada ta maqale,tasan bata isa taje ta fito ba hajja bata gano komai ba,don ko tafiyarta tasan ta sauya.

Wuni sukayi sur cikin dakin ba tare da shi ko ita sun fita ba,sai yayi amfani da wannan damar,ya dinga lura da ita tare da dasa mata sabuwar qaunarta cikin zuciyarta,bai yarda sunyi nisa da juna ko raba mazauni ba,ya sanya nata sabo dashi da saboda jikinsa,tun tana kakkaucewa harta sallama.

Washegari shi da ita kadai suka fita wani waje,bayan sun biya sun gaida su hajja,yadda ta dinga sussunne kai da jin nauyinsu su duka ya alamtawa hajja me afkuwa ta afku,duk da ba haka taso ba,taso sai bayan anyi taron biki an kaita amma ba abun damuwa bane,tunda already matarsa ce.....da fatan alkhairi ta bisu sanda suke ficewa,saita lura mama ma idanunta yana kansu fuskarta na nuna farincikin dake qasan zuciyarta.

Karo kusan na hudu kenan tana hada ido dashi sanda suke zaune saman table din daga ita saishi,waje ne me kyau,wanda kallonshi kawai ya isa ya sanya zuciya ta debe kewar dake damunta,gabanshi shi babu komai face ruwan roba,sanda aka kawo menu ita ya zabarwa abubuwan da za'a kawo mata,wanda kusan duk abubuwan kwadayi ne,yatsunsa ya sarqafe kawai cikin na juna ya zuba mata idanu yana kallon duk wani motsi nata,kyau take qara yi masa,qaunarta yakeji har babu iyaka.

Karo na qarshe da suka hada idanu tadan kwabe fuska kamar mai shirin yin kuka,murmushi ya sakar mata yana girgiza kansa,gyara zamansa yayi still dai baibar kallonta ba,a hankali yace
"U r my first love" cikin mamakin furucinsa ta dakata daga kai ice cream din data debo bakinta ta zuba masa idanu alamun son qarin bayani,kai ya gyada mata
"Yes u r"Saita samu kanta da tattara dukkan hankalinta a kanshi,cike da mamaki take dubanshi
"Tun lokacin da aka haifeki na fara sonki,a lokacin da nike tamkar 蓷a a wajen ummi,duk da na fara samun qanne a lokacin,amma sanda aka haifeki ji nayi sai a lokacin na samu qanwa,a sannan ni kadai kike yarda dani baya ga ummi kaf fadin gidan" yana fadin haka saita tuna sanda hajja ke bata wannan labarin,amma a lokacin ta zata hajjan na fada ne kawai saboda taji dadi a ranta,kota rage kaifin jin haushinsa da rashin jituwar dake tsakaninsu
"Sannu a hankali kina qara gama inajinki cikin zuciyata da gangar jikina,hakan yana yiwa ummi dadi,amma takan kwabeni kan...nayi a hankali,kada kulawar da nake baki tasa ki sangarce,saina fara sanya lura da nutsuwa,a sannan sai na lura da kin fara tabara saboda gata da kike samu daga wajen hajja itama,duk gidan kece ta gaban goshinta fiye da kowa,saboda sunanta da kikaci,sannan kuma cikin jikokinta kinfi kowa wuni wajenta,tunda jima sashenta shine wajen zamana a yawancin lokuta.
Chapter 64 · 0% Book details