Sashe 43
Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Da sauri ta bude idanun nata,sai ta zubesu saman tashi fuskar,take suka hada ido,sai kowa ya janye tashi qwayar idanun,saita kuma ta soma yuqurin saukowa daga saman motar,a lokacin dashi kuma ya juya baya kamar wanda baison ganin saukowar tata ya zaro waya daga aljihunsa
"Kazo maza ina ta baya" ya fada kawai yana kashe wayar,sannan har ta soma takawa zata bar wajen
"Karki dara ko ina....don idan kika batan da gaske babu wanda zaki kuma wahalarwa" iya abinda ya fada kenan,saita waiwayo ta dubeshi ta watsa masa harara,saidai ta makara,don tuni ya sake juyawa ya bada baya,don haka ta dauke kanta ta samu wata motar daban ta jingina,yayin dashi kuma ya koma wajen abokin aikin nasa da suka taho tare,suka jera har zuwa bakin motar haidar din,ya budeta ya shiga ciki duk da qafafunsa na waje,da alama akwai abinda yake daukowa.
Zamansa ba dadewa ta hangi mustapha ya iso wajen,sai haidar din ya fito,ya miqawa drivernsa key,suka shiga shida mustapha,sannan suka taho da motar inda take tsaye.
Cikin salon barkwanci mustaphan yace
"Sojiya yallabiya...yallabai yace a kaiki gida" ko motsa fuskarta batayi ba bare tayi murmushi,ta taka ta isa gaban motar,ta bude murfin baya ta shiga.
Duk yadda mustapha ya qware wajen tuburata da zolayarta wannan karon baici nasara ba,don bata kulashi ba,wani iri takeji cikin jikinta,mutuwar jiki da muguwar kasala,gaba daya bata marmarin komai sai xaman kadaici,kana kuma ta zauna shuru ba tare da magana da kowa ba,a haka suka qarasa gidan.
Hanyar da motar tabi har yanzu idanunsa suna kai,saida major inusa ya taba kafadarshi sannan ya dauke idanunsa ya maida kansa
"U r lucky dabo....komai naka na zuwa cikin nasara da kyawun yanayi,ka godewa Allah,ka samu muqamin da an jima ba'a samu matashi kamarka daya riqeshi ba,ka fito daga babban family masu sonka da qaunarka,masu tarbiyya da kuma hadin kai,lastly ka auri princess charm,she captured all the people's......" Kallon da haidar din ya masa yasa bai qarasa ba,saiya cike zantukan bakinsa da murmushi kawai ya waske zancan,shi kam baima san ya masa kallon ba,kawai abinda ya sani major din ya qware sosai wajen bin mata,abinda yasa sam basa shiri ko jituwa shida haidar din,duk da yadda haidar ke sonshi,saboda mutum ne shi da baya jituwa da duk wani wanda ya kaucewa hanya ko yake ba dai dai ba,matuqar bazai gaya masa gaskiya ya yarda ya dauka ba,idan ka gansu tare da major inusa to sabgar aiki ce,saiya soma takawa yabar major din tsaye a wajen yana bin aliyyun da kallo.
"Shegen yaro......kana ganinsa haka kullum idanunsa a qasa kamar bai kallon kowa,amma yasan takun kowa,the worst part dinma....matan da ake gani bai kallo kuma basa gabansa,yayita yarfasu su kuma da shegen nacin son mai kyau da aji suyita binsa,ashe yana qare musu kallo a fakaice,banda haka ina yaga wannan har yayi wuffff da ita....gaskiya yasha kwana yaron nan" major inusa yake fada shi kadai kamar wani zautacce.
A tsaye ta samesu a falo,tana sallama umminta ta fara gani,sam batasan tazo ba,bata kuma bawa ranta zatazo din ba,saboda batajin dadi ance mata kusan sati guda kenan,duk da ita bata gaya mata ba.
Qarasawa tayi ta gaidata,sannan ta dubi salma dake riqe da jakar hajja,tana ta zuba zance ita dasu yasira wadda itama yau tazo din,duk an fito da jakankunan kayansu maman,wani sanyi ya ratsa zuciyarta,itakam dama ta gaji,so take kawai ayi a gama su wuce ko ta samu sa'ida hajja ta sakar mata mara tayi fitsari.
Data wuwwulga idanunta bata ga jakarta ba,sai tabi bayan salma data koma dauko jakar hannun hajja,ta isketa tana neman jakar a inda hajjan tace mata tana nan
"Don wulaqanci a dauki jakar kowa amma banda tawa,saboda ni bani da gata da galihu?"
"Ai an debi kayan da za'a koma miki dasu,an kawo miki wasu" duban salman tayi sanda take zuge zip din jakar
"Kamar yaya?"girarta ta daga
"Eh to....bari na tsegunta miki,kamar naji hajja tana fadin anan ke za'a barki,zaku taho tare da ya haidar ko?"
"Kambun bala'i!.....ni!,wallahi bazan zauna ba,tabdijan,ai itama hajjan ba haka mukayi da ita ba" ta fada tana jin wani tashin hankali yana ratsata,dafata salma tayi tana boye dariyarta
"Easy mana zuhra."
"Anqi easy din.....naga alama hajja wani abu daban takemin ba so ba,in banda haka ta yaya zata ce na zauna da wannan mutumin a cikin gidansa?,ya kasheni kenan akai musu gawata ko?,dama haka takeso".
"eh haka nakeso don 茩aniyarki....indai wannan shine rashin son to bana qaunarki fadi ki qara fada,ke salma tsaiwar me kikeyi ke kuma daga daukomi jaka?,miqomin driver yazo,ko mu wuce mu barki anan ki tayata zama" wani zillo salma tayi sai gata kusa da hajjan tana cewa
"Rufamin asiri kada ya zaki ya cillani ta window nayi kwanan qofar gida,a jawa yarona da mijina asara" kuka zahra ta saki harda dora hannu aka
"To wallahi nima bazan zauna ba,kowa tsoronsa yake amma haka kawai ni an hadani dashi?,saboda niba mutum bace?,idan ma cinyeni zaiyi ya cinyeni?"
"Eh haka nake nufi don gidanku,ja'irar yarinya" hajja ta sake cewa tana qwalalowa zahra idanu gamida tamke fuskarta kaman bada xahra'un tata take magana ba
"Wuce muje" ta fada tana nunawa salma hanya,tuni salman tayi gaba,tana danne dariyar dake taso mata,ita ta tseguntawa hajja cewa gobe zasuyi liyafar cin abincin dare dukka wadanda aka qarawa girma,kuma kowa da matarsa yake zuwa,idan ma akwai yara harda su,nan take hajjan tace dole haidar dinta shima asan ya zama babban mutum,dama a wajen taga idanun wata qabila yana haka haka akan jikan nata,duk inda yayi tana binsa da wani kallon yaudara na banza da wofi,tota Allah ba tataba,ba qaramin dariya akaci a motar ba da wannan ru蓷u da hajjan ta hada ba,tuni itama hajja tabi bayanta,ai kuwa itama zahran saita kwashi jakarta ta rufawa hajjan baya.
Kacibus sukayi da umminta wadda ta sake shigowa ta rage mararta kada fitsari ya dameta a mota,duk sai suka ja baya,ta dubi ummin itama ummin ta dubeta,kallon da tayi mata shi ya sanyayar mata da jiki,saita tsugunna saman jakartata a wajen,ita kuma ummin ta wuce ciki abinta.
Batafi minti biyu ba ta fito,a lokacin zahran ta dawo bakin qofa ta tsuguna kamar me neman gafara ko taimako
"Kiyi duk yadda zakiyi,kiyi duk qoqarin da zakiyi ki nunawa duniya ban baki tarbiyya ba,ki nunawa duniya na sama dake basu isa dake ba,nayi imanin kaf fadin duniya idan na mutu kika laluba daga farko zuwa qarshe baki da masoyiya kamar hajja har abada,hakanan ko yanzu na mutu zan kwanta cikin kabarina hankalina kwance game da aurenki,don nasan ba zaki tozarta a hannun haidar ba,bazai taba wulaqantaki ba,ba hannun gama garin mutum kike ba,shi din na musamman ne wanda yasan da daraja da mutuncin dan adam,wanda ya kulaa ya kuma girmama rayuwar mahaifiyarki,ruwanki kiga girma da mutucinsa saboda haka,ruwanki kisa qafa ki shure.....zakiga kamar ba'a sonki,tako ina an matsa miki.....soyayya ta gaskiya itace ka tsaya tsayin daka wajen ganin naka ya gyaru kafin kowa,sannan matsalar zamantakewa a hausance sunan mace ke fara fitowa kafin na da namiji....baki da hurumin yankewa haidar hukunci sabida tsohon tunaninki na ba *AL茦IBLARKU* daya ba,akwai banbancin ra'ayi tsakaninku ko?,wannan rusashshiyar hujja ce.....a yanzu ina miki magana da harshen uwa zuwa ga diyarta......ki nutsu ki fara dora komai kan muhallinsa da saitinsa.....sai angwada ake sanin na qwarai" daga haka ummin tayi gaba abinta ba tare data waiwayo ba,ita kadai tasan me takeji a cikin zuciyarta,ita kadai tasan wanne fata ke gareta,ita kadai tasan adadin sau nawa tana hana idanunta bacci don ingantar rayuwar yaranta.
Da qyar ta tashi daga wajen ba tare data dauke jakarta data janyo wajen ba,a hankali tana jin yadda hayaniya da surutunsu keyin nesa da gidan,da alamu ficewa sukeyi,da qyar takai kanta bakin katifar ta zube,duka zantukan ummin nata sun tsaye mata kamar qusa a qahon zuci,hakanan sun kashe mata duk wani qwari na jikinta.
23/10/2021, 08:46 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 27
Tsahon awa guda gidan ya dauki shuru,duk da lokaci zuwa lokaci tana dan jiyo motsi da maganganu sama sama daga falo zuwa kitchen,wanda ta tabbatar da ma'aikata ne.
Tun azahar take kwance bayan ta gama hawayenta son ranta ta godewa Allah,kota kan abinci bata biba,duk da karin safe ne kawai a cikinta,abu daya ke tada ita shine sallah,sai ruwa kawai data ke sha wanda shima cikin dakin yake jiya da dare suka shigo dashi basu shanye ba,haka ta dinga juyi ita kadai,har zuwa lokacin da duhun magarib ya sako kai,aka fara qwala kiran sallahr magariba,saita miqe tana jin yadda tsakiyar cikinta ya qulle,da alamu ulcer dinta tana son tashi kenan idan batayi wasa ba,hakan ya sanya sai data fara fitowa parlour ta bude fridge ta dauki fresh milk mai sanyi babban gora daya tana duban yadda falon ya koma fes,ko ina 蓷as 蓷as dashi yana fidda qamshi,kamar ba'a taba yin baqi ba,ba abinda ke fita sai wani samfurin qamshin freshner na musamman,ga abinci a jere a cikin tsari saman dining table,saita dauke kanta ta koma daki,ta zauna ta zuqe madarar tas sannan ta shiga bandaki,tana fitsari taji gefan mararta na qullewa
"Ya salam" ta fada,alamun period na iya zuwa anytime kenan,haka ta daura alwalarta ta dawo dakin ta tayar da sallar.
*Aliyyu Haidar*
Sosai yayi relax a bayan motar bayan ya aje hularsa a gefe yana furzar da iska daga bakinsa,yana jin yadda sanyin ac ke ratsashi tare da qara haifar masa da kasala da kuma tayar masa da gajiyarsa ta zirga zirgar wunin yau.
Zuciyarsa da qwaqwalwarsa tayi nisa wajen tuna abubuwan da suka faru yau wayarsa dake aje tare da hularsa ta dauki tsuwwa,dan qaramin tsaki yaja,ba kasafai ya fiya son kira ba,saidai yau yasha kiran har ya gode Allah,a hakama don yana kashewa ne baya amsa wani.