← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 42 OF 70

Sashe 42

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Bayan gama gabatar da komai,abu na kusa da qarshe daya rage shine saka musu igiyoyi da stars daga commanders dinsu,hakan yasa wajen ya sake nutsuwa kowa ya sanya idanu yaga nashi wanda yazo dominsa.

Daki daki aka dinga bi ana saka musu alamun qarin girmansu,cike da ban sha'awa karramawa da kuma girmamawa kan yadda suka sadaukarwa da qasarsu rai da lafiyarsu.

Aliyyu mas'ud dabo shine mutum na biyar bisa layi,general hamza shine zai saka mishi nashi,ya matso kusa da haidar din,saidai tsahonsa bazai iya kaiwa ba ga haidar din ba,cikin barkwanci yayi maganar a nemo masa abunda zai taka wanda hakan ya baiwa mutane dariya,murmusawa aliyyun yayi ya duqa dai dai yadda hannun general zaikai ya saka masan sannan akaci gaba.

Duka sai da aka gama sanya musu da sauran jawabe jawabe,sannan akayi sanarwa ta musamman akwai mutum biyar a cikinsu da za'a karrama da wasu lambobi masu siffar kwabo da za'a rataya musu,saboda sadaukantaka gaskiya riqon amana da kuma qwazon aiki,bayan wajen ya nutsu aka fara kiran sunayensu,mutum na farko ya isa wajen,saiya nema alfarmar iyalinshi ce zata sanya masa,duk da cewa shekarunsa sun kusa arba'in da wani abu hakan ya burge mutane,cikin nutsuwa ta taso ta rataya masa sannan ta tsaya aka musu hoto ta wuce,hakan ya sanya aka maida rataya abun wuyan ga iyalan sauran,marasa matan aure a ciki kuma mahaifi ko mahaifiya,abun saiya dinga bada qawa da burgewa,saboda kowacce mata in a romantic way take sanyawa mijinta,tana jin yusra na cewa
"Gaskiya ne,ban sake yarda soja akwaishi da son matarshi ba sai yau....jiba don Allah abun sha'awa,sun sadaukar da farincikinsu ga qasarsu...ma sha Allah,Allah ya dafawa sojojinmu".

Lieutenant jafar wanda a yanzu ya koma captain jafar aka kira,dr nasreen ta damqi hannun zahra cikin farinciki ba tare dama ta sani ba
"Ma sha Allah my happiness....lallai yau ranarmu ce" ta fada tana duban zahra,itama zahra dubanta tayi,tana mamaki cikin ranta wannan wacce irin soyayya ce?wadda bata boyuwa,saita sakarwa dr nasreen murmushi kawai na qarfafa gwiwa,ta gyada kai
"Thanks" ta cewa zahra tana miqewa a nutse ta sauka daga wajen zuwa inda yake tsaye yana jiranta.

Kafin ta qaraso tuni ya miqa mata hannunshi,tana murmushi itama ta isa ta dora hannunta cikin nashi,kamar sun manta da tarin jama'ar dake wajen,ta amsa abun wuyan,tadan rusuna kana ta miqe ta zira masa fuskokinsu dauke da murmushi ta juya tana maqale a kafadarsa aka musu nasu hoton,tana jin salma na fadin
"Wow....matar nan ta hadu wlh"

Sam zahra bata damu ba bata kuma kawo komai ba,don bata tsammaci zuwan sunan Aliyyu ba,sannan tunda daga mama har abba babba na wajen,sun kuma fita cancanta,saidai me?,cikin sakanni sunan aliyyu dabo ya karade abun maganar,wanda kamar qiftawa da bismillah duk sojan daya kasance junior dinsa dake wajen saida suka miqe,sukayi salute nashi sanda yake takowa zuwa inda kowa yake tsaiwa cikin nuna zallar girmamawa,da alama akwai akwai alaqa mai matuqar kyau a tsakaninsu
"Ma sha Allah" 'yan uwa dake kusa taji suna furtawa,lumshe idanunta tayi tana duban wajen yadda suke tsaye,abun ya qayatar da duk wanda yake wajen
"Get up mrs aliyyu dabo" dr nasreen ta soma fadawa zahra cikin fara'a,yayin da dukka su salma suka waiwayo suka sanya mata ido,kai ta kadawa dr nasreen
"Mama tana nan....haka abba ma"
"Tashi kije inna wuro" ta jiyo muryar mama,wanda sam bata zaci taji ba,saita miqe a hankali tana jin wani nauyi na saukar mata,qafafunta sukayi sanyi kamar ba zata iya tafiya ba,wanda wannan ya qarawa tafiyar tata zama slow,hakan saiya qarawa yanayin takun nata ado,da wani salo na daban mai qayatarwa.

Tunda ta taho ya zuba mata idanu da wani salon kallo,wanda ba lallai kowa ya fahimta ba,saif dake tsaye daga gefansa ya soma masa magana qasa qasa
"Smiling please....,just once" banza yayi dashi,saidai idanunsa yana kanta sanda take ci gaba da takowa,taqi kallon koda saitin inda yake,saidai tana sauraren salma dake bayanta tada n tako mata tana mata magiyar karsu bada 'yan uwansu.

Sai data fara amsar abun wuyan sannan ta juya zuwa direction din da yake tsaye,saif ne cikin zaquwa yace
"Please zaki....i beg you mana,kaga fuskarka?,don't behave like......." Qafarsa yasa ya take gefan qafar saif da qarfi,wanda hakan ya sanyashi yin shuru tare da runtse ido
"Mugu" ya fada yana cije lebe,dai dai lokacin da zahran ta qaraso gaban haidar din,sai a sannan idanunsu suka shiga cikin na juna,kowannensu na iya ganin qwayar idanun dan uwansa kai tsaye.....
23/10/2021, 08:45 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 26

Taku biyu ta sakeyi zuwa gabansa,wanda hakan ya qara adadin kusancin dake tsakaninsu,a hankali ta daga hannunta da niyyar zira masa abun,saidai kuma ina,tsahonta bazai taba kaiwa ba,don kanta a dai dai qirjinsa ya tsaya
"Madam kina buqatar qara motsawa kadan,don maigidan naki sadauki ne da gaske tako ina" dukka sai aka sanya dariya,taku daya ta qara ta mannu da jikinsa,qamshin turarukansu suka soma gauraya da juna,gaba daya numfashinta yaso daukewa,sosai bugun zuciyarta ya qaru,ta lumshe idanu tana daga hannunta zuwa saman kansa.

Hucin numfashi taji sosai na sauka saman fuskarta,hakan ya sanya ta bude idanunta,gaba qwayar idanunta ta shige cikin tasa saboda ranqwafowa da yayi da kansa yadda zata samu damar saka masan,saiya lumshe idanunsa gami da budesu lokaci guda still akan fuskarta sanda ta janye nata idanun daga kanshi,karo na farko da yaga abinda mutane suka sha fadi,wanda bai taba gasgatawa ba sai yau,qwayar idanunta irin tasa ce,mai wata irin zaiba da walqiya,har cikin jinin dake zagayawa a jikinsa yake jin yadda tsigar jikinsa na tashi saboda yadda ta mannu sosai da jikinsa sanda take sanya masa abun,saita soma janyewa baya a hankali tana qara tazarar dake tsakaninsu sanda ta gama sanya masa,saidai da baya da baya take takawa tana jin kamar ba zata iya juyawa ba saboda bugun zuciyarta
"Madam....kada dai ki koma,baki gama sakawa sadaukin naki ba,saboda lambobin yabon nashi da saura" taji mc yana fada,tare da qarasowa daura dasu,ta waiwaya tana duban wanda ke miqo mata wani abun shigen irin wancan,saidai bambancin rubutu,hannu biyu tasa ta karba,sannan ta juyo ta dubi haidar dake tsaye,hannunsa saman abunda ta saka masan yanzu,saita sake komawa zuwa inda yaken kamar mai sanda.

Tana isa gabanshi idanuwa suka mata yawa saita fara qoqarin durqushewa a gaban nasa,da hanzari yasa hannu ya dagota,wanda hakan ya sabbaba mata fadawa jikinsa gaba daya,so yake tayi ta gama ta sauka daga wajen,saboda yadda ya fuskanci sunyi calling attention din mutane da yawa,tsintsiyar hannayenta dake riqe da igiyar ya kama,yanajin yadda tsigar jikinsa ta zuba har gefan fuskarsa,saiya ranqwafo kaman dazu,wanda hakan yasa yayiwa fuskarta rumfa fiye da dazun,ya daga hannunta har zuwa wuyansa sannan ya barta ta zura.

Gaba daya jin jikinta take yana rawa,tayi baya kamar daxu zatabar wajen,sai qafafunta suka lanqwashe,ta tafi luu kaman zata fadi,da sauri yakai mata cafka,ya samu nasarar riqo qugunta,ya tsaidata ta tsaya sosai,idanunta a nashi tasa hannunta tadan zame hannunshi daga qugunta da taga kamar baya da niyyar sakinta,sannan ta juya ta soma sauka daga wajen,wanda tuni tafi ya karade wajen,ita kuwa ji take kamar tayi tsuntsuwa ta isa mazauninta,saboda yadda duk inda ta gifta ake binta da idanu,haka duk inda ta gifta sai taji anyi magana akansu qasa qasa
"Beautiful couples"
"Ma sha Allah perfect match"
"Wow ma sha Allah" da dai sauransu,bata iya waiwayawa bare taga wanda ya furta maganar,harta isa mazauninta ta zauna tana fidda ajiyar zuciya me qarfi,tana jin yadda jikinta tacan ciki ya jiqe da gumi
"See love don Allah.....no wonder mata ke macewa murus kan Aliyyu,madam kin musu zarra fa da kikayi wufff dashi,anan wajen naga fuskokin abokan adawa da yawa" caa din dasu salma suka juyo sukayi mata ma yasa bata samu amsa maganar dr nasreen ba,duk da tanajin bata da amsar da zata bata din,sai kawai ta miqe ta soma ratsawa tana fita daga wajen,saboda wani iri da takejin kanta yayi,har yanzu kuma mode dinta bataji ya koma dai dai ba.

Tafiya tayi kadan tabar wajen dake da hayaniyar,gurin akwai qarancin zirga zirga da hayaniyar jama'a sosai,saita samu bayan wata qaramar mota ta hau samanta ta zauna saboda bata da wani tudu sosai motar.

Idanunta ta rufe dukka,ta shaqi iska sosai takai har cikin huhunta sannan ta fesar,a hankali ta soma bita na abinda ya faru yanzu a wajen.
(Ba lallai haka suke gudanar da taron qarin girmansu ba,na tsarashi a hakkane saboda yafi dacewa da abinda zai qayatar dame karatu,ya kuma tafi da salon labarin,ya alaqantu da abinda zaizo a gaba,so pls idan akwai soja ko sojanniya 馃槀,ko matar soja sai ku karba a hakan馃檹馃徑)

Sam batasan lokaci yaja haka ba tana zaune a wajen,har aka tashi taron,sai a sannan 'yan gida suka fara neman inda tayi,saidai har suka gaji da neman babu wanda ya ganta,ga kuma wayarta na wajen dr nasreen bare su kirata suji inda tayin,dole wadanda zasu koma a ranar sukayi gaba,su hajja ma daga baya suka bisu,akabar mustapha ya lalubota tunda haidar din ma bai tafi ba

Tare suka jero shida abokin aikin nasa,suna tafe a hankali da alama tattaunawa sukeyi,hannunsa zube cikin aljihun wandonsa,ya zuwa yanzu babu hula a kanshi,da alama cireta yayi.

A hankali idanunsa ya sauka a kanta,saiya dan zuba mata idanu,yanason tabbatarwa itace,a haka abokin tafiyar tasa ya lura da inda yake kallon,shima sai yabi wajen da kallo
"Lafiya dabo?" Ya tambaya yana dubansa
"Ba komai" ya amsa masa yana dage kafadunsa
"Ina zuwa" ya sake fadi yana nufar inda take din.

Sam batasan da zuwanshi ba,kamar yadda bata tsammaci zuwan nashi ba,kallonta yayi na sakan biyu sannan ya hada yatsunsa ya murza suka bada 蓷as 蓷as.
Chapter 42 · 0% Book details