Sashe 33
Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Iska haisam ya kaiwa naushi,me ya yiwa guy din nan tun karon farko ne haka suke samun sabani?,amma koma meye zai lallaba su bashi auren zahra,kome zaiyi masa zai iya shanyewa indai zasu bashi zahran,saboda ta gama yi masa a rayuwa,bai taba ganin macen data masa dari bisa dari ba irin zahra'un.
A hankali yake tuqin kamar wanda baida lafiyayyen injin mota,da hannu daya yake murza sitiyarin motar,daya hannun kuma ya aza yatsunsa saman labbansa yana dan shafasu a hankali,yayi nisa cikin tunani da kuma lissafin yadda abubuwa zasu kasance da yadda zai tunkari su abba da maganar haisam,shi a karan kansa cikin idanunsu yaga gasken gasken son qulla lamarin daga garesu,amma kuma ta wani fannin yana da hope na cewa zasu karbi zancan haisam din.
Shawara ta qarshe da zuciyarsa ta bashi itace,ya tunkari yarinyar kai tsaye yayi mata tayin amsar haisam din koda baiyi mata ba matuqar dukkansu suna son zame kansu daga al'amarin,idan yaso daga baya sayi dukkan mai yiwuwa su warware zancan haisam din,da wannan shawarar ya qara gudun motarsa,tafiya kadan ya sanya signal yahau club road bayan ya baro titin gidan general.
Bai dawo gida ba sai bayan sallar isha'i,sai daya fara sauke abu sufyan da suka wuni tare a gida sannan yayo gida.
Kai tsaye sassansa ya nufa,yana shiga ya zaro wayarsa ya kira musty yace ya sameshi daki,babu jimawa ya iso,order din abinda zaici ya bashi yayo masa a wani gidan cin abinci dake kusa da tasu unguwar ya hada masa da key din motarsa,yana murna ya fice kuwa da sauri,don yana masifar son aiken ya haidar din,ko banza akwai qaruwa,baya amsar canji da sauransu.
Kayan jikinsa ya fara cirewa ya zubasu a ma'ajiyar kayan datti,duk yadda wasu mazan keda aqidar watsa daki sam haidar din ba haka yake ba,da wahala ki samu dakinsa a wargaje da kaya,komai nashi tsaf tsf kamar wata mace,yana fitowa musty na dawowa,yace ya jirashi zai fito yanzu,saiya zira jallabiya golden colour mai gajeran hannu,bayan ya feshe jikinsa da turarukansa masu sanyin qamshin sai ya dawo falon.
Sai daya zauna gaban ledan da mustaphan ya aje sannan yace
"Idan ka fita....ka turomin yarinyar nan" dubanshi mustapha yayi
"Wace yaya?" Tsaki ya danja yana bude ledar
"Fatima"
"Ohk to" ya fada yana miqewa da sauri gamida aje masa muqullin ya fice.
Wani tunani da yayi shi ya sanyashi daukan wayarsa dake ajiye ya kira mustaphan
"Ka kiratanne?"
"No yaya....yanzu dai zan shiga"
"Manta kawai,bar kiran"
"Ok to" saiya datse kiran ya ajiye wayar ya jawo tarkacen takeaway din ya soma ci,saidai sam abincin bai masa test a baki,saboda ba sabonshi bane cin abincin waje matuqar yana gida,don haka cin abincin bai wani nisa ba ya aje ya wanke hannunsa ya sake daukar wayarsa ya fice zuwa sassan mahaifiyarsa.
Yana tafe zuwa sassan hajja bayan ya baro sashen mahaifiyarsa yana tuna maganganun da suka kusa kwashe awa guda sunayi da ita,wai da gasken kenan hajja take?,har maganar takai kunnen mamanshi?,har tana jaddada masa matsayi da girman hajjan a idanunsu?,da cewa hukuncinta dai dai yake da hukuncinta kona mahaifinsa?,da ire iren wannan tunanin ya isa sassan hajjan.
Sai daya jirata ta fito daga daki yana zaune yana kallon labarai a gidan tv,fuskarta babu yabo ba fallasa ta zauna daura dashi,shima saiya bar dukkan abinda yakeyi din ya tattara hankalinsa kanta
"Kince kina nema na,gani....amma kafin naji abinda zakice,bari na sauke nauyin saqo da alqawarin dana dauka" ya fada yana gyara zamansa sosai cikin kujerar yana duban hajja
"Nasan kinsan boss general hamza ko?" Kai ta gyada a nutse,idanunta kyam akan aliyyun,saiya lumshe ido ganin ta fahimta da wuri
"Yaronsa ko ince dansa....yaga fatima yana so....dazun naje wajen mahaifin nasa,yace na roqa masa alfarma wajenku kan a bawa dan nashi dama" daga haka ya tsagaita yana kallon hajjan.
Ga mamakinsa saita saki wani dan qaramin murmushi
"Wannan wasan kwaikwayon kuma ka shiryo?....kana tsammanin saboda ka sanya sunan general a ciki na kasa aiwatar da abinda nayi niyya na bawa dansa?" Kai ya kada
"Bazan miki qarya ba hajja....kinfi kowa sanin waye ni" kai ta gyada
"To naji....shikenan,aje a haka....baka shaida masa cewa mun mata miji ba,kuma kaine mijin?,gida bata qoshi ba ai bazamu baiwa dawa ba ko?,ba zamu zaka kyandir ba....mu haska wasu mu qona kanmu" sosai yake kallonta yana jin rudani nason lullubeshi,ya tabbata dai da gasken tsohuwar nan take,tanason hautsina masa dukkan lissafinsa da wani zaman lafiyarsa
"Amma hajja....for god sake yarinya tayi laifi ita kadai za'a hada harda ni cikin hukuncin?....me nawa ni a ciki?,hukunci ma irin wannan na aure?....kiyi haquri hajja,amma gaskiya bazan iya karbar wannan tsarin ba,babban kuskure ne ka yankewa kanka hukuncin amsar wani abu da bai dace da tsarin rayuwarka ba saboda wani matsantawa daga familynka,saboda zaka rayu ne tare da sakamakon wannan hukuncin daka yanke....bawai tare da familyn naka ba....,idan ma kin yanke hukuncin nan ne saboda ki faranta ran wasu....babu wani dalili da zai sanya ace saikin gamsar da kowa kin farantawa kowa rai cikin lokaci qanqani....azo kuma a rasa manufar abinda aka yanke hukuncin a kansa rasa manufa ta har abada....".
" ka gama soki burutsun naka?"ta tambayi haidar kai tsaye tana duban tsakiyar idanunsa,shuru yayi yana dubanta shima ba tare da yace komai ba,yana karantar yadda al'amarin keda qarfi da girma a zuciyarta
"Ni fatima dabo.....na isa na sanya ubanka ma ya auri duk wadda naga dama ba tare d wani dalili ba bare kai,saboda haka ka fita daga idanuna....ka kiyaye ni haidar,zaka hadu da fushina irin wanda baka taba ganin irinsa ba,aure ne babu fashi,ruwanku kaida ita ku shirya,ruwanku kada ku shirya,dani da ku shege ka fasa!" Ta fada da qarfin murya.
Kusan tare suka runtse idanu shi da zahra dake tsaye bayan labulen daya raba dakunansu da falon
"Ya salam!" Ya furta yana jin wani ciwo a qirjinsa,ko kusa ko alama babu wani abu da ya taba hadashi da hajja makamancin hakan,sai kawai ya miqe ya nufo qofar fita,yayin da xahra take daki itama ta zube a qasa tana sakin sabon kuka.
Da kallo anty uwani tabi haidar sanda ya fice daga sashen hajjan,saita saka kai ita kuma,tana ji a jikinta akwai wani abu da yake faruwa,kuma koma meye saita jishi.
Sanda ta shiga hajjan na waya da wani dan uwanta daga can garinsu,saita samu daya daga cikin kujerun ta zauna tana jiran hajjan ta gama
"Eh saura kwana bakwai daurin auren haidar da zahra ne......wallahi abunne ya taso bagatatan,don Allah ashaida musu.....daurin aure ne kawai....biki sai daga baya idan sun gama shirinsu za'ayi,don haka karsu damu,da lokacin bikin yayi za'a sanar saiku shaida musu".
Idanu dukka anty uwani ta fidda tana zare ido,da tasan wannan mummunan labarin zataji da babu abinda zai shigo ma da ita sassan,ai bata bari hajja dake qoqarin kashe wayar ta kashe ba ta jefa mata tambaya
"Hajja....wai da gaske ne abinda naji yanzu kina gayawa su kawu inusa?"ajiyar zuciya ta saki
"Wallahi uwani....na gaji da ganinsu suna yawo a gabanmu,shi babu sa'ansa....ita babu sa'anta,naga gwara kawai ayi me gaba daya haihuwa da hanji"wani bacin rai ne ya tasowa uwanin,da gaske dai halima ita da diyoyinta masu gata da babbar fada ce a wajen hajja da babu wanda ke kaiwa matsayinsu?,daure ranta tayi sannan ta sake cewa
"Hakan yayi kyau....amma hajja suna son junansu kuwa?,kinsan zamanin nan.....ba'a tilastawa yara auren da babu son ransu,suna soma ya aka kaya bare basaso" isashen murmushin hajja ta saki tana miqe qafarta dake damunta da ciwo yau kusan kwanaki uku kenan,bata gayawa kowa bama bare su dameta da batun zuwa asibiti a hadata da tarin qwayoyi
"Uwani kenan.....har yanzun suna dana gaba dasu aiko?,kuma idan kasan irin tarbiyyar daka bawa naka baka shakkar komai" kai kawai take gyadawa tana kallon center carfet din da take kai.
Suwaiba keson haidar tamkar tayi me,hakan ya sanya anty uwani shigewa mama sosai tsahon lokaci donta sama musu fada ta yadda komai zaizo da sauqi,tunda shi din me son iyaye ne da qoqarin kyautata musu,sai gashi hajja ta yanke musu hanzari,inda tasan hakan zata faru takan hajjan zata fara neman fadar,shaf ta mance da cewa iyalin na matuqar qaunar tsohuwar,kuma suna a shirye kowanne lokaci domin bin umarninta kamar yadda take iyakar qoqarinta itama ko yaushe don ganin farincikin iyalin nata,tabbas ba zata bari,zata qoqarta,mai rai ai baya rasa motsi,don haka tace
"To Allah yasa ayi damu"
"Amin amin uwani" yunqurin miqewa ta soma yi hajjan ta dubeta
"A'ah,ina kuma zaki,ki shiga ki debi abinci kici mana"
"Ina zuwa hajja,nayi mantuwa me sashen babban yaya,zan dawo yanzu naci"
"Au to....idan kin shiga kicewa hadiza(maman haidar)ta baki saqon ki kawomin"
"Toh...toh" ta fada tana ficewa daga falon da sauri.
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN 鈥楧AI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234聽803聽081聽1300/+234聽808聽540聽5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:43 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 21
馃挮馃挜馃挮馃挜馃挮馃挜馃挮馃挜馃挮馃挜馃挮