← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 5 OF 70

Sashe 5

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Lalalaaaa......lallai zahra.....wannan ba kwanukan da naga yaa xahra nata fadin tashin hadawa yaa haidar abinci bane?" Sai data kai lomar qarshe na hannunta sannan ta daga kai ta dubeta
"Sune mana....kema idan xakici bismillah,zoki zuba iya zubunki" kamar wadda ta danawa wuta a jiki salma ta janye gefe da sauri tana kada hannu gami da fidda ido
"Lalala,bada ni ba saa lallen karya,inason lafiyata wallahi,haka kawai ina lallaba jikina kisa amin shaidar da xanje kabari da ita,kedai da kika shirya tarar aradu daka"
"Ba zakuci bama,kema wanda kikaci shi kadaine rabonki,tunda kika hanashi ci kema baki ci,yarinya ta zauna ta bata lokacinta saboda yaro amma a qarshe kuta yiwa aikin,to baku isa ba,ko ruwan lipto yace ku dafa masa sai kunyi qorafi,kada ma ke inna wuro kiji labari" cewar hajja,tana kaiwa qarshe ta soma qwalawa gaje kira,zahra ta mele baki
"Ko iya haka ma alhmdlh" dai dai lokacin gaje ta qaraso,hajja ta sanyata ta debe kwanukan tana ci gaba da mita,xahra ta miqe tana kakkabe jikinta
"Da蓷ina dake hajja baki iya samun magana daya ba.....muje sister ki bani labarin daxu"
"Zakici 茩aniyarki,zaki dawo ki sameni,nasan da wanda zan hadaki" ta fuskanci sarai me take nufi,amma tasan ba iyawa zatayi ba,don idanma ta hadata dashin 茩arshe sai tafi kowa mita da jin ciwon hukuncin da za'a matan.

Saman carfet din dakin suka zauna,salma tadan dubi hafsat dake baccinta haiqan
"Shegiya kasa,bata da aiki sai bacci" ta fada tana zungurarta,idanu tadan bude kadan,ta gane salma
"Ki saurara min 'yar baqincikin baccin mutum" daga haka ta cusa kanta qasan filo tana gyara kwanciyarta su kuma suka shiga hirarsu
"Wai kinsan meke faruwa kuwa?"
"A'ah saikin fada" inji zahra
"Sabon kamu fa nayi" sosai zahra ta maida kallonta ga salma
"Kamar yaya?,sabon kamu bayan sulaiman din?" Farr tayi da idanunta
"Wallahi,kuma a yadda nake jinsa a raina zan iya hada matsayinsa dana sulaiman" idanu dukka zahra ta fiddo waje
"Keee salma.....kiji tsoron Allah,sulaiman din?" Kai ta gyada kai tsaye itama tana dubanta
"Shi dinfa,meye abun naji tsoron Allah a ciki?,igiyar aurensa ce a kaina koko yaya?,don kawai na zabawa raina shi a matsayin wanda raina ya amince na nuna duk lokacin da aka buqaci na nuna wanda na tsayar?" Kai zahra ke kadawa kawai dama da hagu cikin nuna zallar jimami
"Gaskiya nidai bazan iya ba,haba amana ai bata ce haka ba".

Dariya sosai salma ta saki har tana toshe baki kana daga bisani ta tsagaita tana duban zahra
"Amma inna wuro na yadda lallai boarding ta dakusar da duk wani wayo da basirar da muka sanki dashi,wai ce miki akayi su samarin yanzun tsoron Allahn sukeyi?,ko ce miki akayi idan don saurayin yanzu yana gaya miki da nuna miki daga ke babu wata.....idan bake ba sai rijiya,kece rayuwarsa da sauransu yana nufin hakanne da gaske har a badininsa?,bance miki fau fau ba'a samun wanda hakan bane.....amma sunyi qaranci qwarai,da yansu maqaryata ne,maha'inta ne,basu da *AL茦IBLA* qila kece ta bakwai kota goma a wajensu,hakan yasanya nima bazanyi saki na dafe ba,na laru dashi shi daya ina masa son gaskiya da dukkan zuciyata da gangar jikina ba.....na shafa rana guda naji wayam" ta qarasa maganar tana bugun cinyarta.

Shuru zahra tayi nadan wasu sakanni tana nazari a zuciyarta,sam maganar salma bata samu mazauni a zuciyarta ba,hasashene kawai irin nata da kuma son baiwa kai mafaka,banda haka ita shekararta nawa da nuraddeen bata taba ganin wani abu tattareshi dashi koda sau daya bane makamancin wanda salma ke hasashe?,a kullum soyayyarsu qara gaba take,kishinta yake kiyaye bacin ranta yake,don me zata yarda da zancan salma 'yar tamore
"Nikam bazan iya wannan kwamacalar ba" zahran ta amsa mata bayan takai qarshen nazarinta tana tanqwashe qafafunta waje daya,qaramar dariya salma tayi
"Eh....kekam taki zuciyar na da蓷e da sanin cewa daban take,kinayin soyayya ne dakkan yaqini da amannarki,wanda a yanzun samun hakan yayi qaranci daga wajen mazan har matan" kusan hirar da suka dinga yi kenan a tsakaninsu,wanda har ya kusa kaisu ga musu.

Saidai basu ja da yawa ba dakin ya soma cika da 'yammata,hakan ya sauya akalar hira suka shiga hirar sabgogin da suka shafesu,kamar qawayensu na unguwar dana islamiyya wadanda aka kawowa kudi da wadanda aka sawa rana,jarrabawar qualifying da suke fuskantarta,candy da zasuyi nan gaba da kuma aurensu da sauran hirarraki da ba'a raba 'yammata dasu.

Duk da wannan hirar da ake amma hankalinta nakan wayarta lokaci lokaci,tana tsumayin nuraddeen kowanne lokaci,amma saidai har suka tasamma watsewa saboda lokacin 蓷ora girkin dare yayi a kowanne sashe,kasancewar kowaccensu duk da akwai masu aiki 蓷ai 蓷ai a kowanne sashe amma ba'a barsu sun zauna sun ta'allaqa komai a kansu ba,babu nuradden ba duriyarsa,don haka ta jawo wayarta ta miqe da ita tana tunanin zuwa wajen yaa zahra ta tura mata updated watsapp,don nata yayi expair.

Ci gaba da hayaniyarsu ta hira suke har suka zo zasu gifta ta ma'ajiyar motocin gidan.

Dukkaninsu sun hangeshi,duk da cewa bayanshi kawai suka hango amma babu wanda bai ganeshi ba cikinsu,saboda haka kowacce taja bakinta ta saisatashi gami da rage sautin muryarta.

Sanye yake da wata farar riga 茩al me gajeran hannu,wanda hakan ya baiwa mur蓷a蓷蓷en dantsensa damar bayyana,sai dogon wando shima fari gamida wani farin booth dake qafarsa,daga inda kake wucewa kana iya jiyo qamshin lallausan turarensa da iska ke kwasowa tana bazashi ko ina,ba kayan dazun bane a jikinsa,da alamu ma wanka yaje ya sake ya sauyasu saboda miyar data batashi,waya yake amsawa,kallo daya zaka masa kasan cewa yes!,aikin da yake yayi matuqar dacewa dashi,ko shafawa kayi kasan cewa shi din SOJA NE.

茩asa 茩asa zahra taja tsaki cikin ranta
"Da wannan kayan yafi kamata ma ace jikinsa ya 蓳aci dazu naga ta qaryar gayu da 茩yan茩yami" ta qarashe maganar tana fitar da tsakinta a sarari dai dai sanda ta hangi ya musty na qarasawa inda yake tsayen bayan ya baro wajen me gadi wanda da alama wani saqo ya bashi.

Suna gab da rabuwa kowa ta shige sashensu ba tare da sun ankara ba sukaji muryar ya musty na nufosu yana fadin
"Yaa haidar na magana fa 'yammata" dukkansu babu wadda cikinta bai mur蓷a mata ba,yusra da tafi kowa tsoro cikinsu cikin rawar murya tace
"Wa yake kira a cikinmu?"
"Dukanku" ya bata amsa yana qunshe dariyarsa,don basu ba,hatta su da suke maza ba kasafai kiran haidar ke musu da蓷i ba.

Junansu suka kalla,yusra ta sake cewa cikin qas qas da murya don kada ya jisu
"Amma me kuma muka yi masa ya musty don Allah?"
"Idan kunzo kwaji" daga haka shima ya juya abinsa don kada yayi laifi.

"Kome zai mana ai bazai rabamu da numfashinmu ba ko?,kuzo muje" inji hafsat qanwarsa wadda suke uwa daya uba daya,zahra ko tabe baki tayi,duk da cewa ita dinma a tsorace take,haka suka nufeshi sum sum kamar wa蓷anda suka 蓷auko gawa.

Gaba daya su bakwai din suka zube gabanshi,yayin dashi kuma ke tsaye abinsa yana latsa waya kamar baisan An haliccesu wajen ba.

Saida suka tsammaci ya manta dasu a wajen,sannan ya buda baki kamar wani saraki ya jefo musu tambaya yana ci gaba da latsa wayarsa
"Wace inna wuro a cikinku?" Tambayar duk saita zo musu wani banbarakwai,tunda sunsan dai duk wanda ya kwana ya tashi cikin gidan ya san me sunan,hakan yasa suka kasa amsashi suka hau kallon kallo.
23/10/2021, 08:36 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 04

*KIJI TSORON ALLAH鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆,KADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BA,BA KUMA MALLAKINKI BANE*
___________________________

*Assalamu alaikum warahmatullah, shin kintaba amfani da turaren gashi a matsayinki na mace data amsa sunanta idan amsarki aa toga dama tasamu *awwaba scent* *tazomaku* *da turaren fesawa a gashi natural 100% organic *wanda akahada rose water da essential oils tripped action gashi yy kamshi yay kyali kuma moisturiser at *the same time ba anan abun yatsayaba duk wanda yy order zaahada masa da freshener kala hudu ta daki *ta bandaki ta Mopping da turaren wanka a kan kudi 3,000 kacal indai q cikin watan September dinnna ne daganan kuma zasukoma *normal price dinsu, hakanan turarukqn wuta da humra dinmu anyi masu ragi duk me bukata se nememu a 08034236800 ta what's app kokuma ya ziyarci shafinmu a instagram* *@turare_by_awwaba mungode*
_______________________________

Sake maimaita tambayar yayi a karo na biyu dai ba tare daya kallesu ba,sanin hali yasa suka fara yunqurin nunata kawai,saidai basu kai ga aikata hakan ba tsawarsa ta mamayesu wanda ta rudasu,ba shiri kuma suka nuna zahra dake tsakiyarsu.

A hankali ya dora birkitattun idanunsa dake cike da kwarjini irin na cikakkun maza a kanta na sakan daya kana ya janye yana cewa
"Itace ta dawo yau daga boarding ba?" Haushi tambayar tasa ta bata fiye data dazun,baqo ne shi,ko yau ya soma zuwa gidan nasu,tuni suka amsa masa da eh
"Good" ya fada yana kashe wayarsa ya zurata a aljihun wandonsa na baya,idanunsa dake ladabtar da mutum na bisa kanta.

"Daga dawowarki yau shine kikeson maida mana qofar gida tasha?" Ya jefa mata tambayar da batasan amsarta ba,hakan yasa tayi shuru tana nazari,tare dason gane me yake nufi da hakan
"Am asking you!" Ya kuma fada cikin tsawar data dan razanata,wannan karon bai jira amsarta ba ya dora da
"Wato kaiko boarding da akayi baisa komai ya canza ba ko?,su samarin da sukazo suna son mana tumasanci qofar gida duka ina kika sansu kina kulle cikin makaranta?,koko malaman naki ne soma biyo sawunki?,duka duka shekarunki nawa?tun baki tafasa ba zaki qone?,to i wil deal with u,bazan dauki wannan iskancin ba tun baki riqa ba,ba zaki fi qarfinmu ba,ki gayawa kowanne shashasha duk randa ya sake zuwa qofar gida ya mana fada saina masa daurin da za'a kasa ganeshi,ba gidan 'yan iska bane nan,hope kin haddace abinda nace?" Tuni hawaye ya soma ambaliya saman fuskarta saboda tsabar bacin rai,hakanne yasa ta kasa amsa mishi,har sai daya maimaita mata cikin tsawa
"Kinji ko bakiji ba?"
"Naji" ta amsa cikin muryar kuka
"Ku bacemin a wajen sakarkaru kawai!" Ya kuma fada cikin tsawar.
Chapter 5 · 0% Book details