← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 70

Sashe 38

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har zata wuce hajjan ta kirata ta miqa mata key din,wanda dama can hajjan nada shi,daya a wajensa daya a wajenta,daya kuma a wajen mamarshi,ta amsa ta wuce tana fadi qasa qasa
"Kya ci gaba da share masa idan na komawata makaranta"
"Idan na barkin kin koma ba" hajjan ta bata amsa,sai tayi turus ta dakata da tafiyar da take tana dubanta kamar zata saki kuka
"Haba hajja,bafa haka mukayi dake ba"
"Zaki wuce ko saina iskeki?" Kamar zata dora hannu aka haka ta juya ta fice.

Kamar waccar ranar dakin ba wani dauda yayi ba,sai squeezing da beadsheet din yayi alamun an kwanta akai ne,mayafin ta daura saman kanta sannan ta fara kauda kayayyakin da suke ba'a muhallinsu ba.

Ta isa gefan gadon bayan ta gama gyara qasan,tasa hannu tana janye zanin gadon wasu frames masu kyau suka fado,cikin fargaba ta zagaya inda suka fadin,tana addu ar Allah yasa basu fashe ba,ta tsugunna ta soma daukesu.

Hotunan yaa zahra ne dukka guda ukun,kowanne sanye da hijabi take,fuskarta dauke da murmushi,kamar idan ka kirata zata amsa maka
"Margayiya" ta fada cikin zuciyarta,dan tsurawa hoton idanu tayi,sai kuma ta miqe tana jan tsaki data tuna daga inda hoton ya fado
"Aikin banza....har wani kwana da hoto yake waishi baban soyayya,aisai ka bita can shine ka burge,inda wani ne da yaji magana a wajenka" ta fada tana tuna yadda ya dinga treating din issue dinta dasu nuraddeen,locker din gefan gadon ta jawo ta watsa frames din,duk da tana iya hangen wasu pics din wanda da alama na yaa zahran ne,saita koma gadon taci gaba da gyarawa,kafin ta gama ta shiga toilet dinsa don wankewa.

Sai data kalli bandakin ta tabbatar komai ya fita fes sannan ta murda qofar ta fito.

Bata tsammaci ganinsa ko dawowarsa ba a sannan,bayanshi kawai ta hanga yana tsaye gaban gadonsa ya baje wasu takardu yana zaba,da alama daukarsu ne ya dawo dashi.

Jin taku ya sanyashi juyawa a hankali,sai suka hada ido na sakanni kafin ya dauke idanunsa ya maida ga abinda yakeyi ba tare daya ce komai ba,sai tabi ta bayansa itama ta fice daga dakin.

Batafi minti biyu da fita ba ya shiga wajen hajjan yana hadiye zuciya riqe da envalope a hannunsa
"Hajja....me yarinyar can kemin cikin daki bayan bana nan?"
"Sata ubana" ta amsa masa itama tana tsareshi da idanu,saiya lumshe idanunsa,tsohuwar tana bashi ciwon kai yadda ya kamata,ita kadai duk duniya ta isa tayi masa karen tsayen da take masa,saiya juya kawai ba tare daya sake cewa komai ba ya fice daga sashen
"Zanyi maganinku" ta fada a ranta,tana dauke idanunta saiga zahra
"Wai hajja ma tuhumata yake da shigar masa daki?,nidai wallahi hajja kina jamin ina zaman zamana" ta fada kamar zata saki kuka
"Yanzu ma na fara jaza miki" tuni ta tara qwalla a idanunta
"Bazan sake masa shara ba Allah,ayiwa mutum aiki sannan ya rasa me zai sakamin dashi?,to dakin nasa dakin wa yafi cikin gidan nan?"
"Idan bakije kinyi ba nida kaina kuwa zan dauki tsintsiya naje na share masa,idan kuma banje ba zansa daya daga cikin iyayenki yayi"saroro zahra tayi kafin ta juya zuwa cikin dakinta da sauri.

Mita take ita daya kamar zataci kanta,tana qissima sauran kwanakin daya rage tayi tafiyarta makaranta,ita gobe ma gidan salma ko hafsat zata,sai kuma ta tuna idan tace zata din sai hajjan nan tace saita tambaya,ita kuwa data tambaya gwara haqura da zuwan.

*BAYAN KWANA BIYU*

Ana ya gobe zata koma makarantarta,tana falo tana sake goge wasu kayan da zata tafi dasu atamfofinta,musaddiq jikan gidan yayi sallama shi da nurain,hannunsu dauke da leda suka zubw gaban hajja
"Gashi inji yaa zaki,na yaya zahra ne"
"Shi yana ina?" Hajja ta tambaya
"Yana waje yana sallamar wasu baqi ne" inji nurain yana hayewa saman kujera
"Jeka kace min idan ya gama yazo ina son magana dashi".

Jin haka ya sanya zahra a gurguje ta gama goge kayan nata ta miqe zata shige daki
"Ke....dawo ki kwashe wadan nan kayan daga gabana" tana zumbura baki tana fushinta haka ta dawo ta kwashe ledojin ta jasu har cikin daki,ta musu waje ta jibge ta shiga sabgarta.

A gurguje ya leqo saboda kiran da hajjan tace tana masa,bayan sun gama gaisawa tace dashi
"Qarfe nawa zaka miqata makarantar a gobe?,don inason na qarasa hada mata abinda yayi shaura" kansa ya daga ya kalli hajjan
"Oh....ai dama bani ke kaita ba ko?"
"A sanda take babu igiyar kowa a kanta kuma ba matar wani bace ba ba...banason dogon magana,ka shirya gobe da wuri ka maidata makaranta" yasani cewa koda ya fada wani abun ma babu abinda zai janyo masa sai bala'en hajjan,wanda ya lura da cewa yanzun wani bala'i ta koya,motsi kadan zata ce anemo mata tsoho da tsohuwarshi.

******* *WASHEGARI********

K'arfe takwas da wasu mintuna ta gama shirinta tsaf,ta shiga tayi sallama da umminta sannan ta shiga sashen abba babba shima tayi masa sallama,sannan ta wuce dakin mama,maman haidar ta mata sallama
"Allah ya kiyaye hanya,ya bada ilimi me amfani" ta miqa mata wata baqar leda da batasan meye a ciki ba,hannu biyu tasa ta karba tayi mata godiya sannan ta fito.

Tana takowa zuwa bakin motar tana kallon yadda ake sanya mata kayanta bayan motar tashi,shi yana zaune daga ciki ba tare da ya ko motsa ba,tana tsaye har aka gama sanyawa sannan ta matsa ta bude gaban motar ta shiga a hankali.

"Ina kwana" ta furta domin bin umarnin umminta,bata ji ya amsa ba duk da taji alamun motsin fitar sauti,dama kuma ba damuwarta bace ya amsa din ko kada ya amsa,illa iyaka tasan cewa ta fita haqqi,ta kuma cikasa nasiha.

A hankali ya tada motar kana ya saitata ya fice daga gidan,kafin subar layin ya sanya hannunshi gaban motar ya dauko wayarsa yayi kira ya sata handsfree ya aje,bugu biyu aka daga
"Ka sameni a nasarawa sardauna cresent" daga haka ya katse kiran ba tare daya jira amsar da za'a bashi ba.

Tafiyar kurame da takura daga wajen zahra ta mintuna ba dasu gaza ashirin ba ya tsaya qofar wani gini wanda ake gab da kammalashi,kashe motar yayi ya zare key din ya fita daga cikinta y kulle sannan ya jingina da murfin,ita dai batace komai ba tana kalloshi ta cikin glass din har zuwa sanda ta hangi shigowar ya musty a napep na haya,bataji me suka tattauna ba,saidai taga ya miqa masa.key din,kana ya matsa daga jikin motar zuwa ginin gidan dake gabansu,shi kuma mustapha ya bude motar ya shigo.

Sai daya rufe sannan yace da ita cikin tsokana
"Sai matar babban yaya....Allah dai ya biya,matar soja marmari daga nesa" harara ta watsa masa
"Kaga ya musty bama haka dakai,dadai ya shamsu ne nasan zaiyi abinda yafi haka,don Allah ja muje,ni hakan ma yafimin dai dai" ta fada tana yatsina,yayin da mustapha ya qyalqyale da dariya.

Ko kadan hakan bai bata haushi ba,saboda tasan cewa inda shine zai kaita babu komai cikin tafiyar face zallar takura har su isa,wala'alla ma sai yayi ko ya gaya mata abinda ranta zai baci a banza.

Sanda ta shiga dakinsu kamar hadin baki duka roommate din nata suna nan,har da sauran ma,ihu suka saka suna kiran ga amarya ga amarya,bata tanka su ba saima harara data watsa musu
"Duk ku iya bakinku wallahi" don har ga Allah har cikin zuciyarta tana jin sune sila,su suka jaza mata komai,saidai ko kadan basuji gargadin nata ba,saima ci gaba da zolayarta da suke,hindu tace
"Erhmmm....erhmmm...ashe ashe dai....yayan dai da aketa nunamin sam baida kirki.....ashe dai kece zaki wufffff da abinki akemin hannunka me sanda" kicin kicin zahra tayi da ranta sanda take aje jakankunanta saman katifarta
"Kinga hindatu....idan baso kike aji kanmu ba ki aje wannan maganar....am seriouse bana sonta" saida suka gama kidansu da rawarsu sannan suka qyaleta.

Zuwa washegari ta gama gyara komai nata,batayi qasa a gwiwa ba ta koma lactures cike da hazaqa karsashi da qwarin gwiwa,saidai haka nan ta samu kanta da takatsantsan da mu'amalarta da mazan ajinsu,duk da cewa dama can duk wanda ya sa ta yasan tana da wannan zarrar,amma a yanzun takatsantsan da kamewan ya qaru,tunda ada issue din karatu yakan hadasu,amma a yanzun mawuyacine idan ba ya zama dolen dole ba.
23/10/2021, 08:45 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 24
*_Are you guys looking for where to buy ur skincare product @ mg's skincare is the best plug for you馃_*
*_Do you wish to have that flawless skin that's free of all skin prblm_*
*_Do you wnt to achieve that milky skin that turn heads wherever you go馃槈_*
*_Try mg's product nd I assure you you'll never use any other product except mg's product鉁卂*
*_Mg's will gv you the best out of all_*

*_With mg's product ur skin is 馃挴 clear,fresh,smooth nd ur skin will absolutely glow all day馃拑_*
*_We have herbal whitening black soap now nd beauty set available_*
*_Nd both the soap nd the beauty set is for all skin type everyone can use it馃_*
*_Just gv it a try now nd see wonders鉁卂*

Chat:08062991549
Call:08064532391
Soap price:3k
set:11k

Follow us on
Instagram@glow_with_mgs
Facebook:mg's skincare

*_Nd guess wht馃_*

*Duk Wanda zesiya Kaya daga yau Alhamis 30-9-21 zuwa Nanda 5days that is ranar talata there will be 20% off discount a soap nd the set馃槏so what are you guys waiting for hurry nd grab urs馃拑 now is the time to glow馃鈥嶁檧锔*
*Pamper ur skin馃Φ*
*Shine like a bride 馃懓*
*be part of the glow* *team karkubari abaku lbr*

Just chat 08062991549 to plc ur orders馃槝

Do not forget to follow us馃憜
Like nd comment pls dearies馃槝
Patronize us馃檹
mg's always serve you the best鉁呪潳锔
______________________________

*_BAYAN SATI BIYU_*

karfe biyu na rana suka fito daga aji,sauri take tana Allah Allah ta isa daki ta cire kayan jikinta ta samu ta watsa ruwa saboda zafi da rana,tuni ruwan sama ya fara samuwa a wasu garuruwan kamar legos abuja da sauransu,ya zuwa sannan kano da kaduna suma suna saka ran samun nasu ruwan saman na farko.
Chapter 38 · 0% Book details