← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 13 OF 70

Sashe 13

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna tsaka da wannan hirar abban ya shigo,kowacce ta masa sannu da zuwa suka fara qoqarin fita bayan hajja data fito daga daki yanzun ta iso falon,dakatar da zahra yayi,ta qaraso gabansa ta durqusa
"Ya akayi yayanku yace ki koma makaranta amma baki koma ba?" Marairaicewa ta sakeyi
"Abba bani da lafiya ne shi yasa ban koma ba"
"Amma kuma aikin warware ko?,yace ya tambayi hajja?" Bata da ikon musawa tunda ya taddasu ana wasa da dariya da ita,da alama boarding ta aureta kenan har sai ta gama,don haka saita gyada masa kai
"Shikenan,zuwa gobe da safe ki sake gyara abinda baki gyara ba.....nasa ya maidaki" batasan sanda ta daga kanta ba tace
"Wa?"dan kallonta yayi sai kuma yace
"Yayan naku" sai kuma taji nauyin hakan,don haka bata sake cewa komai ba ta amsa da to,sannan kamar kazar da qwai ya fashewa a ciki ta wuce zuwa daki,yayin da hajja ta bita da kallo harta shige.

"Har yanzu uwata batason makarantar nan hajja" nannauyar ajiyar zuciya hajja ta saki sannan tace
"Damuwar data shiga na jin cewa Aliyyu ne zai maidata.....yafi damuwar komawarta makarantar yawa.....bansan wanne irin nau'in rashin jituwa bane tsakanin inna wuro da haidar ba" shima ajiyar zuciyar ya saki a boye yadda ba zata jishi ba,sam basu son abinda zai taba ran tsohuwar ko ya bata ranta sam sam,don haka cikin salon son kwantar da hankali yace da ita
"Quruciya ce ke dawainiya da dukkaninsu,wataran zai zama labari" dan qaramin murmushi ta saki tana kada kai
"Haba muhammadu.....idan kace innawuro quruciya ce na yarda shi kuma haidar fa?"
"Sai muyi addu'ar samun jituwa tsakaninsu ai hajja" kai ta gyada
"Hakane....don babu abinda ya gagari addu'a"
"Wannan haka yake" ya fada yana janyo ledar daya bawa xahra ta shigo masa da ita.

Washegari qarfe shida na safe ta gama shirinta gaba daya,saidai tana ta faman kumburi saboda wanda zai kaita,qarfe bakwai tana falon hajja tana karyawa da kayan karin da hajjan ta tashi da wuri ta hada mata don kada ta tafi da yunwa.

Shamsuddeen ne yayi sallama falon hannunsa riqe da maqullin mota
"Baki gama shiryawa bane?" Ya tambaya bayan ya gama gaida hajja
"Kai zaka kaini?" Ta tambayeshi itama
"Eh....ya haidar yace na kaiki" baki ta tabe,ita hakanma yayi mata dadi,don haka ta qarasa abinda bata qarasa din ba cikin hanzari,tayi sallama da duk wanda ya dace sannan suka wuce.

Komawarta makaranta duk data koma da tabon nuraddeen cikin zuciyarta amma hakan bata bari yayi mata tasiri ko ya hanata karatu ba,ta tattara hankalinta kacokam kan karatunta,musamman da suke shirye shiryen fara zana jarabawar qualifying,duk da cewa batason makarantar amma shima bata bari ya hanata karatu ba.

Wata iriyar baiwa da basirar karatu Allah ya bata,tana da qwaqwalwa sosai,wanda hakan yasanya tayi tasiri sosai a zuciyar malamai da kuma daliban makarantar ma gaba daya.

Sannu a hankali lokaci ya dinga juyawa yana tafiya da wani sauri da kuma hanzari,wanda yakan fauci abubuwa masu muhimmanci a rayuwar bayi yayi awon gaba dasu,wasu tare da saninmu wasunsu kuma ba tare da saninmu ba.

'Yan kwanaki ya rage musu su fara zana jarabawar suka samu baquncin sabbin malamai da aka sauyasu da wasu malaman dake koyar dasu wasu darussan,ciki kuwa harda malamin da zai dinga koya musu yaren turanci wato english,saidai su dinma na wucin gadi ne,sunzo ne sakamakon horaswa ta musamman da wadancan malaman suka samu damar zuwa suyi na wasu watanni.

*_AL茦IBLARSU_*

Malam nasir,matashin saurayi,ma'abocin iya ado gayu da kuma jan aji,uwa una qwarewa da gogewa wajen iya yaren turanci,wanda tun farkon zuwansa shine abu na farko daya soma jan hankali dalibai mata da dama dake cikin makarantar a kansa,yadda yake da gwalli ya hade da qwarewarsa wajen iya turanci,sai hakan ya zame masa tamkar ado,yana da jan hankali da kuma daukar hankalin kamar mace,da dama daga cikin 'yammatan makarantar yana burgesu,yayin da shi kuma izzar sa tasa bai duban kowacce mace cikin makarantar,har zuwa ranar da Allah ya qaddara haduwarsa da zahra,shigarsa a jinsu na farko,a lokacin da suka fara extra lesson saboda jarabawar dake gabansu.

A ranar ta tashi da ciwon mara,wanda a baya ita sam bata sanshi ba,bata taba yi bama sai a lokacin,haka ta dinga daurewa saboda nacinta da karatun,da kuma burin samun sakamako mai kyau,duk da cewa hasina tace da ita ta zauna,bata da matsala tunda ita zata je amma ga qiya.

Zuwanta ajin saita kasa hasala komai,hakanan ta kifa kanta saman table din da take kai tana jin yadda mararta ke zugi.

Tana iya jiyo sautin sallamar malamin,tashinsu da gaidashi da sukayi,yadda ajin yayi dif sanda yake zagaya daliban,ya tsaya gefan table dinta yana tambayar wacece wannan?,bata jin zata iya dagowa bare ta amsa mishi,tana jin sanda hasina dake gefanta ke masa bayani
"Allah ya sawwaqe" ya fada yana barin wajen bayan ya basu umarnin zama,sannan ya isa gaban allo ya fara aiwatar da abinda ya tarasu.

Rabi da rabi takejin komai,har zuwa sanda jin da zaman saman teburin ya gagareta,ta fara nishi saboda ciwo,wanda ya fara jan hankalin hasina kafin kuma sauran daliban zuwa malamin su ankara,shi ya bada umarnin hasina da wata hasana jibril su dagata su kaita a bata magani,sai a sannan da suka dagata yaga fuskarta,ya kauda kai bayan sun fice yaci gaba da yiwa sauran daliban karatu.

Kwananta uku kafin ta samu sauqi,ranar da zata koma shiga lesson din,da yammacin ranar suna shirin tafiya,ta fuskanci yadda daliban kowa keta qoqarin hada wani assigment wanda batasan na meye ba,saita dubi hasina dake zaune gefan gadonta riqe da nata assigent din tana sake dubawa
"Wai aikin me aka baku,naga kowa hankalinsa a tashe?" Rufe littafin tayi tana murmushi,ta daga kai ta dubi zahra
"Wallahi malamin nan zahra ya hadu tako ina,mugun kaine dashi,da alama yana ja sosai,ga gayu ga iya koyarwa" baki zahra ta tabe tana saka hijabinta
"Nifa ba wannan na tambayeki ba hasina" murmushi ta sakeyi
"Ko baki tambayeni ba ai dole na gaya miki,aikin daya bamu yace zamu iya cin karo dashi a jarabawarmu,zai gani ya zamuyi dashi idan mukaci karo da tambaya makamanciyarta,shine ya bamu yace mu gwada,bari ki gani" bude mata tambayar tayi tana mata bayani iya yanda ta fahimta tsahon wasu mintuna,murmushi zahra tayi bayan ta gama bayanin,saita koma ta zauna,ta jawo jakar litattafanta ta ciro littafi da biro,dai dai sanda hasina ta miqe
"Mu wuce zahra,naga an fara tafiya"
"Jeki kawai zan taho" ido ta fidda
"Kai...wallahi ya hana,yace kowa ya tabbatar yana rigashi shigowa"
"Kije yanzu zan qaraso"
"Idan ya hanaki shiga ke kika jawa kanki,nidai nayi gaba" ta fada tana qarasawa cikin wadanda basu kai ga tafiya ba suka rankaya suka fice tare.

Da sallama ta shiga ajin wanda ya cika da dalibai,malamin dake gaban dan tebur da kujerar zama ta malamai,saidai shi yana tsaye ne bai zauna ba ya waiwayo yana amsawa,dubanta yake ganin tana qoqarin shigowa,fuskarsa a hade yace
"Dakata....ina zaki?,ban hanaku zuwa a irin wannan lokacin ba?"
"Malam kayi haquri.....saida na tsaya nasha magani ne"
"Baki da lafiya?" Ya tambayeta yana dubanta,kanta a qasa ta gyadashi
"Eh,yau kwana uku ban taba samun lesson dinka ba,sai yau na samu sauqi" a sannan ya gane itace,ya tuna fuskarta,don haka yace
"Allah ya qara afuwa.....wuce"
"Na gode sir" ta fada cikin farinciki sannan ta wuce zuwa mazauninta.

Karatu suka ci gaba dayi,ta bada dukkanin attention dinta ga malamin,shi dinma ya fuskanci hakan,don haka saiya zamana karatun kamar da ita yakeyi,saboda kusan dabi'ar malami ce,bada hankalinsa ga dalibin daya fuskanci yana fahimtarsa yadda ya kamata.

Eh tabbas hasina batayi qarya ba,ya iya karatu ya iya koyarwa kamar yadda tace,hakanan taji dadin karatun na yau sosai,ta kuma qaru sosai.

Sai daya gama ya fara amsar aikin daya basu din,da kansan yake bin teburin kowacce daliba ya amsa littafin,ya tsaya a wajen ya duba sannan yayi mata marking ya wuce na gaba har ya qaraso nata teburin,ganin zai wuceta saboda tsammanin batayi aikin ba yasa tayi saurin miqa masa nata littafin,sai daya kalleta sannan ya amsa littafin,ya dawo da baya zuwa wajen mazauninta ya bude ya fara dubawa.

Lokaci lokaci yana daga kai daga littafin ya dubeta harya gama karantawa,saiya rufe littafin kawai ya riqeshi a hannunsa ya wuce teburi na gaba,hakanan taji babu dadi,ko bata rubuta dai dai bane?,tasan iya bakin qoqari tayi wajen ganin tayi assigment din daidai duk da bata zo ba a sannan,mutum ce ita da bata bari assigment sam ya wuceta,saboda tasan hanya ce ta sake samun wani sabon ilimi ga dalibi,hasina dake gefanta qasa qasa tace
"Hala baki rubuta dai dai bane?" Kafada ta daga cikin damuwa
"Ban sani ba nima,ina jin dai hakane" daga haka suka bar maganar harya gama duba na kowacce daliba ya koma gaban allo ya tsaya.

"Fatima sa'id dabo" ya fada yana karanta sunan daga jikin bangon littafin nata
"Yes sir" ta fada tana miqewa,ya kalleta sosai sannan ya mata umarni ta fito gaban aji.

Littafin ya bata yace ta karanta abinda ta rubuta ta kuma yiwa 'yan aji explanation,cikin sanyi jiki ta karba,tana nauyin kada ace shirme tayi,hakanan ta baiwa kanta qwarin gwiwa ta soma karantawa tanayin bayanin kamar yadda ya umarceta,yayin da shi kuma yaja gefe daya ya tsaya jingine da bango yana qare mata kallo,yanajin tana wani birgeshi haka kawai.

"Sauran qarin bayani ga wanda bai gane ba kuma....saiya tambayi sir" ta gama bayanin nata da fadin haka,kana ta maida idanunta kansa,sai suka hada idanu,janye idanunta tayi sanda yake sakar mata murmushi ya tako a hankali ya soma tafa mata yana fadin
"Very good fatima.....every body clap for her" take ajin ya rude da tafi,saida suka tsagaita sannan yace
"Wannan shine karatunmu nayau gaba daya fatima ta gamashi,assigment dinta koni iya abinda zan rubuta kenan,ta dace da class captain....kuma itace headgirl dinku da zarar kun shiga ss 3" da wannan bayanin nasa aka tashi daga aji ranar.

Tun daga lokacin sai ya zamana ya ganeta sosai fiye da zatonta,yakan kama sunanta sau tari idan suna karatu,hakanan itama takanyi tambaya har kan abinda bashi suke karantawa bama saboda qaruwarta,hakan yasa sabo yadan soma shiga tsakaninsu,hakan yasa ta soma samun abokan adawa daga ajinsu dama ajin sama dasu wato 'yan ss 3,wadanda keda muradin nasir din.
Chapter 13 · 0% Book details