Sashe 40
Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kafin ta gama sallar umma tuni ta gama,saita tattara abun sallar ta fita daga dakin,da alama itama nauyi takeji,hakan ya baiwa hajjan damar tsigale zahra tasss,saidai tayi kunnen uwar shegu da hajjan,charting dinta ma take abunta,harta gaji ta haqura.
Kafin sauran suyi wanka su huta tuni an cika teburin gidan da nau'in abinci kala kala,cikin girmamawa da gurbatattar hausarsa yake shaida musu an gama komai,su abincin ke jira
"To....to sannu da qoqari yaro kaji" abba babba ya fada,sai yayi murmushi cikin girmamawa yace babu komai.
Ganin an kusa sallar la'asar sai suka yanke suyi sallah dukkansu a jam'i sannan su zauna cin abincin,don basuga masallaci nan kusa ba,haka kuwa akayi,abban tsakiya ya jasu sallar,suka idar sannan suka hallara kan dining din,ita dai hajja mita ta soma kan ba zataci abinci kan teburi ba,don haka zahra ta diba mata nata ta shimfida mata ledar cin abinci a qasa sannan ta aje mata
"Yauwa,yanzu naji batu....ke ya kika samu waje kika zauna?" Tace da zahra wadda ta koma saman kujera ta zauna maimakon ta koma wajen cin abincin
"Na qoshi" ta amsa mata ciki ciki
"Ungo nan" ta fada tana watsa mata daquwa
"Sauko kici tun banci mutuncinki ba" soma saukowa tayi dai dai sanda qarar bude gate din gidan ta riskesu,ba jimawa saiga biyu cikin yaran gidan suna shigowa da kayayyakin amfani na gida suna jibgewa,suna kammalawa muryar sallamarshi ta cika falon,hakan ya sanya zahra janye yatsunta daga abincin da take ci din,saboda ji take kamar zai mata kallon makwadaiciya,saboda zuwa gayyar sodin da hajja ta jawo mata,bugu da qari ta tilasta mata cin abincin gidansa,wanda ita sam bataso hakan ba.
Saidai yadda suka gaisa a tsaitsaye ma ya nuna akan uzuri yake,don ko nuna ya ganta cikin falon bata ga alamunsa ba akan fuskarsa,ya tambayesu zai koma sai wajen dare zai sake shigowa,yanzu ma ya tsaida wasu abubuwanne yazo yaga isowarsu lafiya,idan da abunda suke buqata suyi magana,addu'a sukayi masa da fatan alkhairi ya miqe yana musu sallama cikin kuzari da hanzari irin na namijin soja,taku bibbiyu ya juya ya fice daga falon.
Zahra ita ta gyara komai da suka bata,su abba babba suka buqaci fita gari wajen wasu daga cikin mutanensu da suke harka dasu,saiga driver ya taso da hanzari,motar da aka kawosu cikin gidan ya bude musu yace su shiga,oga yace duk inda zasu ya kaisu,hakan ya musu dadi da kuma sauqi.
Cikin gida suma hirarsu suke abunsu,zahra ce kawai ta shiga daki ta kwanta saboda gajiyar da takeji a jikinta,bata farka ba sai ana gab da sallar magariba,koda ta leqa falo duka suna can sun daura alwalar salla,da alama su abban ma sun dawo,ga mamakinta sai taga ya musty,idanu ta fiddo
"Kai,yaushe kazo?"
"Sanda kikayi nisa a duniyar bacci,yarinya taji hadadden gida" ya amsa yana dariya gami da sauke hannun rigarsa dake tattare,shima da alama alwala ya daura,da idanu ta masa nuni da mama dake wajen,dariyarsa ya gumtse yadan matso inda take
"Yaushe aka fara kunyar mama wai haka?,anya kuwa?,ba'a fara yi da danta ba?" Tabbas da zata iya duka zata kai masa,to amma saboda ba halin hakan saita bishi da harara shi kuma ya fice yana dariya,yayin data koma ciki itama ta soma haramar sallar.
Sai bayan sallar isha'i sannan ta shiga tayi wanka,ta dawo ta jawo jakar kayanta ta buda.
Da 蓷aya da 蓷aya take duba kayan da ilham ta hada mata,gaba daya haushin duniya ya cikata,tabbas da ilham na kusa saita mammaketa,gaba daya riga da skert dinta wanda bata sakasu saita dora after dress akai,sannan babu bra ko pant a ciki sai qwara daya,gefe daya taje ta debo mata kayan bacci cikin wadanda ta fara tarawa a baya,sanda take saka ran aurenta tare da 'yan uwanta
"Lallai yarinyar nan ta rainani....Allah saita raina kanta,bari muje gida" ta fada tana cire daya daga cikin kayan baccin doguwar riga ce wadda kadan ya rage ta isa idon sahunta,ita kadaice me dama dama,saita dauki aron hijabi daya cikin hijaban hajja ta zumbula bayan ta shafe jikinta da turaruka kamar yadda ta saba duk sanda zatayi shirin bacci.
Falo ta dawo ta iskesu suna hira,mama da umma su suka fara tashi,dama tuni abba babba suna waje,da suka shigo kuma sai suka musu sallama,don abba babba yace ya kama musu masauki acan zasu kwana,ya rage a falon daga hajja sai zahra sai musty,sai a sannan zahran ta samu sukunin zubo abinci ta zauna tanaci suna kwasar dariya,saboda wata drama da ake haskawa,hajja ta dage saita fahinta abinda akeyi,musty na fassara mata yana hadawa da yi mata tsiya suna kwasar dariya abunsu harta gama,ta maida farantin ta dawo sukaci gaba da hirarsu.
Qarfe goma na dare aka sake bude gate din mota ta shigo,zahra dake zaune daura hajja sai taji tasha jinin jikinta,dukkansu sunji shigowar motar,saboda haka babu damar tace zata waske ta tashi,tilas taci gaba da zama a wajen,har zuwa sanda muryarsa ta fara ratso falon yana amsa waya kafin isowar gangar jikinsa,hannunsa daya dafe da waya,dayar kuma baqar leda ce dauke da tambarin wani wajen saida abinciccika.
Musty ne ya miqe ya amsa ledar yana masa sannu da zuwa,da hannu ya amsa masa yana qarasowa,ya samu waje ya zauna yana yin sallama da wanda suke wayar ya kashe ya maidata aljuhun gefan wandonsa yana duban hajja bayan yadan sauke ajiyar zuciya,da alamu a gajiye yake sosai
"Sannu da gida....ya naji gidan shuru?"
"Duk sun kwanta saura mu,babanka kuma yaqi kwana,yaa kama musu masauki sun tafi can" goshinsa ya dafe
"Ya Allah....daya fadi hakan yakeso ai da nayi waya an basu daki"
"Wallahi....sun jima aida tafiya".
"Ina wuni" ta furta idanunta na kallon qasa,don ta fuskanci hajja ta sanya musu idanu sosai,saiya waiwaya kadan ya dubi inda take ya dauke kai kana ya amsa tare da cewa mustapha ya bawa hajja ledar,wanda ke ido biyu suyi amfani dashi,karba tayi tana masa godiya,saiya miqe yana wucewa zuwa ciki
"Inajin sai da asuba zamu hadu,am very tired hajja....mustapha.....idan ka tashi da asuba ka nemi ni,don zan fita da wurwuri akwai kuma aikin da zan baka"
"To yaya" ya amsa masa.
Bai rufe minti goma da shiga ba hajja ta dubi zahra tana hade rai
"Ke inna wuro....hada abinci ki kai masa" kamar zata musa saita fasa,ta miqe tana jin kamar ta bace hajjan ta daina ganinta,ta isa bakin dining din ta hada komai saman wani qawataccen babban tray ta durfafi dakin.
A hankali kamar wadda ta shigo sata ta tura qofar dakin,tana saka qafarta cikin dakin ta lume cikin wani kallausan carfet daya rine da sanyi,baya ga qamshi na musamman daya ziyarci kafofin hancinta,zata iya cewa dakinsa nacan gida kango ne akan wannan,duk da bata da nutsuwar da zata iya tsaiwa qarewa dakin kallo amma a kallo daya kawai idanunta sun kaiwa qwaqwalwarta saqo da dama game da kyau da tsaruwar dakin,qarar ruwa da takeji daga wata qofa dake hannun hagu na dakin ya tabbatar mata yana bandaki,kamar an mata rahama haka taji,don haka da dan sassarfa ta isa ga wani dunqulallen qawataccen table ta dora plate din,ta koma da baya tana ficewa daga dakin da sauri.
Sanda ta koma tana ankare da irin kallon da hajjan ta bita dashi,amma batace da ita komai ba,itama saita share kamar bata gani ba,hajjan bata jima ba ta tashi ta barsu ita da musty sukaci gaba da hirarsu,ba'a jima ba itana taji bacci ya soma daure mata idanu saita miqe tana masa sallama,shima kayan kallon ya nufa yana kashewa gami da cewa
"Nima kwanciyar zanyi,saboda gobe na tashi fresh,kinsan goben nan fa babu sauqi,zamu hadu da manyan mutane....Allah yasa nayi babban kamu nima...." Harararsa tayi
"Ai anan kuka fi kauri"
"Kinga laifina?" Saita saki dariya tana yin gaba,sau tari sai ta dinga ganun mustapha kamar ba cikinsu daya da haidar ba,saboda tsananin sauqin kansa.
Da sallama ta tura qofar,sai taga duhu,qwayayen dakin a kashe,lalube ta soma yi don kunna qwan,taji muryar hajja na fadin
"Waye anan?"
"Hajja nice fa" ta fada dai dai sanda tayi nasarar ganin makunnin ta kunna,haske ya gauraye dakin
"Me kikazo yi kuma?,salon ki hana jama'a bacci ku da baku gajiya da surutu" saita miqe ta zauna sosai tana kallon zahra,mamaki maganar hajjan ta bata,don haka tace
"Nima kwanciyar zanyi ai,bacci nakeji sosai wlh"
"A ina zaki kwanta din?,badai a nan dakin ba" saroro tayi tana duban hajja,murya qasa qasa saboda karsu tashi sauran tace
"To a ina hajja?,akwai wani dakinne bayan wannan?"
"Eh....dakin mijinki me yake?,ko ce miki nayi na daukoki ne kizo ki kwanta gotai gotai a gabana?,ko kuma kiji dadin jirgi ki koma?" Idanu ta zaro,wato hajja da manufarta kenan a ranta tasa aka daukota takanas daga makaranta?,kwanan dakin haidar dai dai yake da kwana kusa da maqabarta,ta inama zatace wai taje su kwana daki daya?,saita karyar da murya kamar zata saki kuka
"Haba hajja....haba hajja don Allah"
"Au ba zaki fita ki tafi ba dogon bayani kikeso kenan?,toni bari na baki nawa makwancin naje mu kwan tare dashi" ta fada tana qoqarin miqewa duk da ciwon qafar da take fama dashi.
Abun saiya girmami kan zahran,da mugun sauri ta juya ta fice daga dakin,don tasan indai hajjan ta miqe to taja mata jagwal,don sai ansha daga kafin a sha kanta.
23/10/2021, 08:45 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 25
_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_
_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_
_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE..*_
_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA 鈥榊AYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.*._
_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61*_