Sashe 36
Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ta sameta harta soma brush din,saita jingina da qofa tace
"Wai zahra me kike yine haka?,nida salma ta bani labari na zaci iskancinki ne kawai,ai koda za'a miki auren da bakiso yanzun ai an daina wannan duhun kan,da iliminki fa?,barema miji irin Aliyyu....hmmm wallahi kukan dadi ma kike,hadadden mutum gentle man irinsa?,tsada fa irinsu suke wallahi" kamar jiran hasinan itama zahran take,saita hau kuskure bakinta sannan ta waiwayo ta dubeta
"Tunda ya miki me yasa baki magantu ba tun wuri ke an baki shi ba?"dariya hasinan ta saki tana daga hannayenta sama alamun surrender
"Kai ina....babban goro ai sai magogin qarfe,wallahi yafi qarfina tako ta ina,ya haidar ai sai irinku....yanzu dai ki maida wuqar....don Allah zahra,kodon ki farantawa umminki rai ki saki ranki kiyi abinda ya kamata,wallahi wallahi tun shigowata gidan nan na fara ganin fuskokin 'yan baqinciki muraran,ko a dakinkin nan ma yanzu akwai yan baqinciki da yan saka idanu zaune suna aikinsu,don Allah karki fito sai kinyi wanka....na roqeki" ta fada tana hada hannayenta waje guda,harara zahran ta jefa mata sannan tace
"Naji....ki bani waje,ko kuma a gabanki zanyi wankan" dariya ta saki tana girgiza kai,haka kawai ta zama wata rigimammiya ta gaske,fita tayi gami da ja mata qofa.
Tana zama saiga anty alawiyya ta shigo itama dauke da qaramin yaronta
"Ina amaryar?" Ta tambaya suwaiba,saita yatsina fuska ba tare data amsa ba,hasina dake danna waya ta dago kai
"Tana wanka anty alawiyya"
"Toh....bari ina zuwa" ta fadi tana fita.
Kusan minti ashirin sannan zahran ta fito,wanda yayi dai dai da dawowar anty alawiyya,ta nema duka mutanen dakin su bata waje,sai hasina ce kawai ta rage.
Fada ta soma yiwa zahran sosai kan yadda ta maida kanta,ta kuma tilasta mata ta shirya,hakanan tana baqin rai da dacin rai ta shirya din,abinda yadan rage mata baqincikin shine zuwan hindatu,wanda bata tsammaci zuwan nata ba,tana bata labarin yadda suke kula da komai nata na makaranta,harda su CA da suke mata,wanda taji dadin hakan,saidai hindatun ta tambayeta dama zahran tasan aure zatayi shi yasa bata kula kowanne namiji,amma kuma koda wasa bata taba gayawa wani ko bashi labarin auren nata ba,harda ita karan kanta,duk da yadda suke?
"Uhmmm" kawai ta iya cewa hindatun ba tare data bata amsa ba.
Su ukune rak cikin katafaren dakin hotel din da suka sauka a daren jiya,haidar dake kwance rigingine hannunsa riqe da waya yana dannawa,sai Fahad dake zaune a gefansa yana latsa system din dake gabanshi.
Turo qofar akayi aka shigo,saif ne dauke da wata baqar leda dake dauke da tambarin wani kamfanin dinke dinke daya shahara a nigeria,inda suke saida kaya ready made kowanne iri.
Fahad ne ya amsa sallamar,ya qaraso ya cilla ledar gefan haidar yana dubanshi
"Ga kaya nan ka tashi ka shirya" ya fada yana zare sau cikin qafarsa,tsaki haidar din yayi yana sake dora qafarshi daya kan daya
"Ka qyaleni haka saif please,already na gaya musu ban shigo kano ba,ba lallai na samu zuwa daurin auren ba"
"Idan baka je ba kuma kayi yaya da sauran abokananmu da su zasu halarta" wani irin zabura yayi ya miqe ya zauna sosai saman gadon,da qarfi ya furta
"What!....waye ya gayyacesu?,waya gaya musu?" Ba tare daya ce masa komai ba ya nuna masa fahad da yatsa wanda keta latse latsensa ba tare daya tankasu ba.
Wani mugun kallo ya jefa masa sannan yace
"Waya saka?,waya aikeka?" Sai sannan fahad ya kalleshi
"Ra'ayi da radin kaina....waikai malam ma tsaya,duk fa wannan botsare botsaren da kake na banza ne da banga amfaninsu ba....qarya ma kake kace tun da can baka son yarinyar nan,in kuma kasan hakane me ya hana ka bamu dama mu da muke muradi?,da munyi magana sai kace mu kama girmanmu kai bakason raini,to yanzu ga qarshen tika tika nan,idan zaka tashi ka shirya kawai ka shirya bamason gulma da pretending"sosai saif keta qoqarin danne dariyarsa saboda ganin yadda haidar din ya zuciyo,ai kuwa basu ankara ba ya kaiwa bayan fahad harbi da qafarsa,Allah ya taimakesa ya goce yana dariya.
Ganin fahad xai jiqa musu aiki yasa saif ya koreshi waje
"Ka bamu waje da Allah malam" ya fada yana hade rai,saiya tattara tarkacensa ya fita yana fadin
"Ana so ana kaiwa kasuwa"
"Ka gaya masa....ni ba abokin wasansa bane wallahi ya shiga hankalinsa....if not zai raina kansa"
"Calm down mana aboki"cewar saif yana zama kusa dashi
"Ni ina mamakin wannan abun da kakeyi....banda abunka ai an wuce wannan qarnin,kada fa ka manta koda baka so kana da right na qara auren wadda kakeso,a yanzu bayan ita akwai uku a gaba ba zata tare maka komai ba,sannan kome zakayi kada ka duba hajja mana,ka duba iyayenka da aljannarka ke qafarsu,kada kayi abinda zaka watsa musu qasa a ido,wannan nasarar qarin girma daka samu duka sirrinta shine yadda kake kyautata musu da binsu,kada ka watsa albarkarka akan wannan minor issue din mana...and mamar zahran,ko yaya uwa uwace,haka 蓷a 蓷a ne,ko yaya tana son diyarta,ko yaya wani abu mara dadi ya bullo akan diyarta koda ta boye a fuskarta lallai tana jin ciwo a zuciyarta,da kanka ka gayamin matar she mean alort to you....."
"Ya isa" ya dakatar da saif,tsahon mintuna biyar sannan ya aje wayar hannunsa ya miqe kana ya wuce bandaki kai tsaye.
****** *BAYAN WASU WANNI**********
Shudewar wasu qididdgaggun awanni da basu da tsaho unguwar tayi wani irin cikar kwari na ban mamaki,dimbin jama'a masu tarin yawa suka shaida daurin auren ALIYYU MAS'OD DABO da FATIMA SA'ID DABO bisa sadaki naira dubu dari,wanda abban tsakiya shi ya biya lakadan.
Dashi da zahra dake cikin gida dukkansu jin sanarwar daurin auren suke kamar a labarin tatsuniyoyi,kamar wani mafarki suke da babu dadewa zasu farka suga ba gaske bane,don haka shi haidar dinma ana gama dauraws maimakon ya shiga cikin gidan saiya shiga mota kawai,ya umarci drivern daya fara yawo dashi ya kaishi wani masaukin baqi na musamman ya kama daki na kwana biyu,babu irin nema da duban da ba'ayi masa ba babu shi babu dalilinsa,koda aka gayawa hajja cewa tayi
"Da ita data kwanta ciwo,dashi daya gudu duk ku qyale 'yan kan uba,duk zasuyi su ware,拼a拼an yau ne fa?,muna nan daku zasu baku mamaki,munafukan banza" haka suka gaji suka haqura da neman nasa,tunda sunsan koma ina yaje yana sane ya tafi din kamar yadda hajjan tace.
***** *_BAYAN KWANA BIYU_*********
Tuni gidan ya zamana babu kowa sai mutanen gidan,kai kace ba'ayi wani taro bama daya danganci biki,ta bangaren zahra tuni ta tattara auren da aka daura mata ta aje lamarinsa gefe,ta auna ta auno bata ga ta inda zai takura ta koya zame mata matsala ba,saidai dama da zai bata ko kuma ya zame mata tsani ko matattakala da zata taka ta cimma burinta na qarasa karatunta da take kan gaba,baya ga haka kuma sasan yadda zasuyi da sauran matsalolin,don dai bata manta da maganar hajja wadda ta sake sanya mata relief a rai ba,indai har haidar din ya kasa shiga zuciyarta to ta mata alqawarin amsar mata takardarta,maganar ma dariya take bata,don bataga ta wata hanya da haidar din zai shiga zuciyarta ba,ta yaya ma?,yadda yake jin kanshin nan,saidai kuma an samu arashin yadda yakeji da kansa itama dai dai take dashi,da ire iren wadan nan tunanukan yasanya ta sawa auren nata suna MATACCE,ta kuma fara tsara yadda zata koma makaranta abinta ba tare da wata damuwa ba.
******************
Kimanin qarfe takwas da wasu mintuna na dare,ita da hajja zaune a falon hajjan suna taba jira,ta tanqwashe qafafunta saman kujera tana yankan farcenta da nail cutter,ilham da husna na zaune daga gefe sun bada himma a kallo.
Kadan kadan kuma kamar daga dan nesa kadan da qofar shigowa sassan hajjan take jiyo muryarsa,tayi tsam da ranta,tabbas shine,don haka ba tare da kowa ya lura da abinda ta jiyo din ba ta miqe ta nufi dakinta,hajja da batasan wainar da ake toyawa ba ta dubeta
"Ke kuma meye haka?,wanne irin tashine haka kamar wadda ake kira?"
"Ina zuwa hajja" ta bata amsa tana shigewa dakin gami da turo qofar.
Ajiyar zuciya ta sauke ta samu waje tana zama,ita sam bataso ma su hadu,saboda idan ta tuna cewa yana amsa sunan miji ne a gareta ita kadai tasan me takeji,ta kuma sha jan kunne wajen umminta kan kada ta qara yarda tayi wani abu akan haidar din da zai sosa ran hajjan,shi yasa tayi gaggawar barin wajen ma tun kan hajjan ta ankara da dalilin da yasata barin falon.
Ko minti uku batayi ba kuwa ta jiyo muryar nan tasa yana sallama cikin falon,a dake muryar take wanda hakan zai alamta maka fuskarsa na nan yadda kowa ya santa koma fiye da haka,babu digon fara'a ko walwala kenan,saita lumshe idanunta tana sakin tsaki,ta koma ta kwanta rigingine tana jin yadda zuciyarta ke daka.