← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 70

Sashe 11

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"A kawo maka abinci ne?" Hajja ta tambayeshi,kai ya kada alamun a'ah,sannan a nutse ya furta
"Idan akwai fura kawai ta isa" sai ta waiwaya wajen zahra,wadda tana son barin falon,amma kuma tana son kallon programe din da ake yi a wani gidan tv,bata so ya wuceta don yayi mata
"Duba fridge wuro akwai damammiya....kayi sa'a kuwa nonon me kyau ne,wanda aka kawomin ne daga can gida adamawa" yunqurawa tayi ta miqe,ta isa fridge din ta ciro furar,saita miqawa hajjan tasa hannu biyu ta amsa silver da nonon ke ciki,wanda har tsatstsafa yake saboda tsabar sanyi ta miqa masa tana cewa
"Kanaji muna magana kan case din inna wuro baka ce komai ba?" Sai daya amsa furar ya bude yasa ludayin dake kai sannan ya daga shanyayyun idanunsa ya kalli hajjan
"Me zance......i dn't know what to say" duk da bata fahimta qarshen zancensa ba amma saita gyara zamanta
"Na zaci a matsayinka na babba zaka nema yaron kaji komai daga bakinsa....tunda a a zahirin gaskiya suna son junansu" kamar bazai amsa ba,don itakam zahra har tayi nisa da hanyar barin falon,tana ta zumbura baki,sam bataji dadi ba data tuntu eshi da zancan,zata zubda mata aji ne kawai,kuma ma ai yana ji akayi maganar da ya sadiq amma baice komai ba,sai daya dan kurbi furar sannan ya amsata
"Ana aure dole hajja?,kika sani ko batayi masa bane?".

Kamar saukar mashi haka zahra taji maganar a qahon zuciyarta,don sai data kasa jurewa ta waiwayo ta dubesu,shikam shan furarsa yake kamar ma baisan me ya fada ba,cikin bacin rai tayi gaba da sauri ta shige dakinta,batasan dai me hajjan tace masa ba,amma ta jiyo muryarta tana magana,saidai bata iya tantance me take ce masa.
23/10/2021, 08:38 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: *KIJI TSORON ALLAH鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆,karki taba kayan daba naki bane,ba kuma mallakinki bane*

7

Saman madubi ta samu ta zauna cikin fushi ranta na wani irin suya
"Shifa ya haidar din nan rainin wayonsa yawa ne dashi,ya rainama mutane ajawali,meya daukemu ne?,duk laifin hajja ne,ai tasan bana hada shirgina dashi me yasa zata masa zancan matsalata,aikin banza kawai,don yaga mata na hauka akanshi snine hake raina ajawalin mata,koya dauka kowa baka yake,baisan suna mata suka tara ba,mtsewww......aikin banza kawai" a sarari tayi maganarta,kamar da wani a dakin take magana,taja tsaki tana gyara zamanta saman madubin.

Ji tayi xaman dakin gaba daya baiyi mata bama,gwara ta shiga cikin 'yan uwanta ko zata samu sassauci,saita zaro gogagge cikin hijabanta ta saka ta zira silifas dinta ta fito.

Har yanzu yana zaune falon riqe da babbar abokiyarsa wato waya,ya wani miqe qafafunsa saman center table,gefansa furar da yace a kawo masa ce,ya ajjiyeta ba tare da yayi mata wani shan kirki ba.

Harta giftashi bai daga kai ba,sai data kusa qofar fita taji yace
"Ke!" Tasan da ita yake,dole ta dawo
"Ki tabbata gobe a makaranta kika kwana" abinda ya fada kenan a taqaice,dole ta amsashi da to,duk da kuwa ji take kamar ta rufeshi da duka saboda takaici,haka ta fita tana tura baki gaba,ita sam wallahi babu innamal din komawarta makaranta,so tayi ma ta la茩e da wannan ciwon taqi komawa gaba daya,don itakam gaskiya ta gaji,amma yana son rusa mata plan,to Allah yasa babu kowa a falon sanda ya fada bare a tilastata,shuru kawai zatayi da bakinta,suyita wasan buya harya koma hutunsa,tunda dak ai shima ba dawwama zaiyi ba,da wannan tunanin ta shiga sashensu salma.

A kitchen ta sameta tana kwabin doghnout,sosai taji dadin ganinta
"Gwara da kika fito ai,shi yana can wala'alla yana sha'aninsa keya barki kwance,dama yanzu nake cewa bari na gama kwabin nan naje na fiddoki,na kunna wayarki dazun naga kamar ma ya tura miki saqo" baki zahra ta tabe,tana jan daya robar kwabin ta tattare dogon hannun rigarta ta fara tayata tana cewa
"Can masa....gaba daya ma kamar Allah ya fidda minshi a raina,idan ma ya cuceni yaje shida Allah"
"Kawai yafi" daga haka suka shiga wata hirar,zahran na bata labarin abinda ya faru yanzu a falon hajjan,da kuma cewar da yayi lallai gobe ta koma makaranta
"Kinsan Allah ki rufawa kanki asiri ki tattara goben ki koma,kinfi kowa sanin halin ya haidar ko?" Salma ta fada tana dubanta
"Wallahi wannan karon saidai yaci kansa da kansa yasha baqin ruwa,don ni ko zan koma badai gobe ba ehe,ke saima anyi bikin huda dani" dariya salma ta danyi
"Zahra,zahra kafiya,to Allah ya kauda bacin rana"
"Amin" ta amsa mata,salman ta cire hannunta daga flower data gama kwabawar ta wanke a fanfo,tana goge ruwan a rigar jikinta tace
"Bari na dauko miki wayar" baki ta tabe ba tare data ce komai ba,salma ta juya ta fice.

Kafin ta dawo ta gama kwabin itama ta wanke hannunta,harta samu waje ta zauna,ta dawo ta miqa mata wayar tana cewa
"Ga saqon nan,duba ki gani",still baki ta tabe kana ta sanya hannu ta karba din,ta buda saqon ga fara duba tsahonsa kafin ta koma farko da niyyar karantawa hafsa tayi sallama cikin kitchen din riqe da plate din abinci
"Gawa taqi rami,yanzu hajja tacemin aikin fito" murmushi tayi tana maida idonta kan wayar kana ta amsawa hafsa
"Ke kyaso na mutu tun yanzu?" Kai ta girgiza itama tana neman wajen zama
"A'ah ina fa.....salame zubamin miya don Allah inji umma,haka kawai suka mana tuwo da rana"
"Kya samu wata salamen ta zuba miki kuwa amma bani ba" dariya ta saki,tasan sarai bata son sunan
"Afwa tuba nake"
"Kina da hannu ai sai kizo ki diba" tashi tayi ta isa gaban tukunyar ta bude ta zuba miyar,daidai sanda zahra ta fara karanta saqon a fili

_assalamu alaiki,ina me neman afuwa da gafara daga gareki,nasan cewa na miki ba dai dai ba,amma tuntuni naso na samu lokaci mu tattauna kafin zuwan rana irin wannan amma Allah bai nufa,duk da haka ina mai baki haquri,ki sani matar mutum kabarinsa,kuma Allaj yayi keba matata bace shi yasa ban aureki ba,amma idan da hali kuma zai yiwu ki bani dama ki zamto mata ta biyu a wajena,ina dakon amincewarki_

_nuraddeen_

Wani ashar salma taso zundumawa sai kuma ta katse
"Lallai gayen nan yakai qarshe a rainin wayo"
"Tayani gani don Allah" inji hafsa tana kama haba,yayin da zahra ta saki wani murmushi mai ciwo,da kuma nuni da rainin wayon nuraddeen din ya bata mamaki,don daga haka ta zare sim din wayar kawai ta ballashi biyu ta watsa cikin sink din dake kusa dashi,ta kunna famfo ruwa ya korashi
"Na dauki tarayya ta dashi kamar mafarki,kuma ku saka hakan a ranku,mu shiga next chapter da Allah" ta fada cikin dakiya.

Shigowar yusra kitchen din shi ya tada sabon hira,haka nan suke da wuya kaga mutun daya shi kadai,saidai idan dukka basa gidan
"Na zaci munafuntata kukayi ai kuka zauna kuna wainar fulawa aka rasa me kirana"
"To ba ita akeyi ba kwa蓷ai...." Dariya ta saki
"Allah qamshin manja na dinga ji,kuma naji kamar daga nan ne,kwanan nan sha'awar wainar fulawa nake wlh,mu kuma cikinmu an rasa me soyawa,kowacce sai tace idan ta soya ba zata iya ci ba,ai shikenan"
"Ni kinma tunamin" hafsa ta fada tana ane farantin data gama cin abinci
"Gidansu zainab ahmad din nan?" Tayi maganar da sigar tambaya tana side hannunta
"Eh" suka amsa a kusan tare
"Wallahi suna wainar fulawa da daddare,harda me qwai dame kifi,ke kinji dadinta kuwa?"
"Wayyo Allah,har kinsa yawuna tsinkewa,yaushe zamuje"
"Yauma idan da kudinki"
"Mu bari sai gobe,yau ya usama yamin alqawarin kyautar dubu daya gobe"
"To kuwa muna aljihunki" inji salma
"Allah ya kaimu" ta amsa musu,daga haka suka sake shiga wata hirar kafin kowa su watse.

Bata koma sassan hajja ba,saita wuce sassansu wajen umminta,tunda ta kwanta ciwon bata ganta ba.

A hankali tayi sallama falon nasu,ita daya ce zaune qasan carfet,gabanta da wata babbar baqar leda tana ta fiddo kayan dake cikinta,wanda suka hada dasu madara bournvita,Klein,corn flaks,sabulai,mayukan shafawa,turaruka,maclien,cream salad,suger na qananun jakankuna da sauran kayan amfanin gida na yau da kullum.

Kayan tabi da kallo sannan ta samu waje ta zauna
"Ummi ina yini?" Kai tadan daga ta kalleta kana ta maida ga abinda takeyi tare da amsa mata
"Lafiya lau,ya jikin naki?"
"Da sauqi alhmdlh"
"To Allah ya qara lafiya"
"Amin amin" ta amsa mata,sai shuru yadan biyo baya,wani lokaci ummin nata kaman tana mata halin fulani na kara da alkunya kamar na diyan fari,duk da cewa ba itace ta farin ba,amma itama abun ya shafeta.

"Haka abu kuma ya faru?,sai ki addu'a Allah yasa hakane yafi alkhairi" ta fada cikin yanayi na rashin bawa abun muhimmanci
"Amin" ta fada tana murxa yatsanta.

Bayan shudewar wasu sakanni ummin ta sake cewa
"Kinga irin hidimar yayanku,shi koda yaushe baya gajiya damu,kowanne lokaci alkhairinsa a tafe yake,ko iya hakan ya isa ya bayyanar da nagartarsa,fatana Allah yasa sauran 'yan uwanshi suyi halinsa"
"Ba amin ba,kura ce da fatar akuya" ta fada a ranta,amma a fili don ta farantawa ummin nata sai tace
"Amin" a taqaice.

Ita ta taimakawa ummin aka raba kayan zuwa ma'ajiyarsu,kowanne abu aka sashi a muhallinsa,tadan jima ranar wajenta,ita kuma a fakaice tana jan hankalinta tare da sake nuna mata girman haidar din,sai da suka gama komai sannan tayi mata sallama gab da za a kira magrib ta baro sashen.

Daga nesa ta hangoshi can inda masu gidan dake da mota ko babur suke ajiyesu,tsaye jikin motarsa,booth din a bude ana fidda kayan ciki zuwa sassa sassa na gidan,baki tadan tabe kana ta nufi sassan hajja.

Canma raba kayan ta tadda hajjan nayi,ita da shafa'atu husna da amira dukka jikokinta ne,sai tayi wucewarta cikin daki,bata tsaya ba ta zarce bandaki,ta daura alwala,saboda gab ake da akira sallah.

Kamar yadda taci alwashi kuwa a washegarin bata gayawa kowa yadda sukayi da yaa zaki ba,sai tayi kwanciyarta luf a daki,wuni guda,hajja tana ta mita da yawo tsakanin falon da dakin kan ta fito,ko kuma jikinne?,saitace lafiya lau take,tana ramuwar baccin da bata samu yi ba,har hajjan dai ta haqura ta qyaleta.
Chapter 11 · 0% Book details