← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 70

Sashe 62

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

"Wannan kadanne daga alkhairinsa,alkhairin nasa kuma da zaya shiga rayuwarki matuqar kika ci gaba da bin maganar magabatanki,matuqar kika ci gaba da daukar zancansu da muhimmanci,na taba gaya miki,haidar ba irin sauran maza bane gama gari,tun a shekarun quruciya na gama karantar halayyarsa tsaf,tun kafin na haifeki nake sha'awa inama ina da diya da idan ya girma zan bashi ita?,yana da boyayyun nagartattun halaye da dabi'u,yana da sauqin kai da sanyin hali,yana da tausayin mace.....amma dukka ba kowa ke iya karanta da gane hakan ba,saboda matuqar zaka mu'amalanceshi daga nesa,to tabbas zaka masa fassarar mai ra'ayin riqau,mai kakkausan hali,mara tausayi ne,mai zafi da saurin fushi,eh aliyyu yana da ra'ayin riqau akan gaskiya,yana da kafiya kan abinda yasan shine dai dai,yana da fushi idan yasan an sabawa dai dai ko doka,yana da rashin tausayi akan azzalumin mutum mara imani,amma matuqar baka da irin wadan nan siffofin,zakaji dadin zama da haidar fiye da kowane dan adam.....zan baki tips na zama da haidar din,a matsayinki na diyata,ni kuma uwa a gareshi da tasan halayyarsa,ba don ki mallakeshi ba,sai don ki masa biyayya ku samu zaman lafiya da qauna me dorewa" wadan nan sune lafuzzan umminta a sanda take shaida mata batun tafiya da ita bayab ta miqa mata passport dinta ta sanya masa albarka,zama ummin tayi ta dinga zayyana mata abubuwa masu matuqar amfani a rayuwarsu,har zahran ta dinga mamaki da kunyar hakan,saidai ta lura ummin ko a jikinta,saboda ta sani tana gyara rayuwar diyarta ne,tana kuma inganta rayuwar haidar dinta,aikine da takejin ya wajaba a kanta a matsayinta na uwa

*_AMINU KANO INTERNATIONAL AIRPORT KANO_*

Da motoci hudu duka aka dunguma aka tafi rakiyarsu filin jirgin saman don wucewa qasa me tsarki,suna ajesu sukayi bankwana dasu aka maida motar gida,dama daya ta abba yusuf ce,daya ta abban tsakiya,zasu wuce kuma kasuwa ne abinsu,sauran biyunne na haidar,mustapha yaja daya,ya shamsu da suke tare da ya sadiq sukaja daya suka koma gida da sauran yaran gidan da aka taho dasu.

Gaba daya wani irin nauyi takeji,surukutar abba babba da mama takeji tana mamayarta,ko hira ake bata iya magana cikinsu,dama shi haidar din ba wani gwanin magana bane,sau tari wayarsa tana hannunsa ne yana faman danne danne,wanda baya wuce duba labarai,ko duba saqonni da suka shafi aikinsu.

Yana ankare da yadda ta kasa sakewa din,nutsuwar data sakeyi ta bashi mamaki,kusan tun tale tale yasan zahra cikin yaran gidan,tayi shuhura wajen aikata laifi da samun kariya daga wajen hajja da a wancan lokacin yake ganin daure mata qarqashi kawai takeyi,abinda ya janyo rashin jituwarsu kenan,yaci alwashin shi bazai bari ta buwayi kowa ba,duk da girma ya sake canzata qwarai,amma a yau din ta sake canzawa,wata kamala ta musamman ke kwaranya tun daga fuskarta zuwa jikinta.

Qafarshi daya dora daya kan daya ya sauke bayan ya gama karantarta,ya duba agogon hannunsa,akwai sauran lokaci kafin a nemi passingers din,don haka ya miqa a nutse yana daukar hularsa dake ajjiye gefe ya soma takowa inda suke.

Ita ta fara ganinsa,a sace take kallonsa,tunda suke da shi ba zata iya tuna sau nawa ta taba ganinsa da qananun kaya ba,yau sai gashi sanye da wata dakakkiyar shadda gezner gray colour,sabuwar dal,sai maiqo take da daukar idanu,wani irin annurin kyau yake fitarwa na musamman,gaba daya kamanninsa sun canza kamar ba Aliyyu haidar sojan nan ba,batasan yaganta,batasan tunda ta fara kallonshin ya ganta ba sai da yazo dab da ita,ba tare da su abba suna gani ba yadan ranqwafa ta gefan kunnenta kamar xai dauki wani abu
"Idan kinaso kawai kice kinaso,kada ki wani damu da jan ajin nan naki" saiya miqe ya barta daskare cikin tsananin jin kunya da nauyi,yayin daya bar mata sauran turarensa tana shaqa wanda ke qara sanyata cikin wani yanayi nason kasancewa dab dashi
"Waini babu inda zan samu ruwa ne,ishirwa fa nake ji tunda muka fito daga gida" hajja ta fada,sai haidar din yace
"Akwai.....muje a duba mata" yayi maganar yana duban zahra,a hankali ta miqe,tayi gaba yabi bayanta.

Slow ta fara tafiya bayan sun fito daga wajen,don a jikinta takejin qare mata kallo yake tsaiwar da yayi daga baya,rage hanzarinta da tayi yasa ya cimmata,saiya jera da ita,suka ci gaba da takawa a hankali kuma tare,saidai kamar wadansu masu shirin film,lokaci lokaci saisu waiga kallon juna,kowanne saiya kama dan uwansa,sai kuma kowa ya dauke kansa,saidai shi haidar yana maida kansa gefe daya ne ya murmusa,komai nata ya gama fallasa kanshi,wai amma dole saita ja masa aji?,saiya samu kansa da wassafa yadda zai qure jan ajinta da kuma kunyarta,qaramar dariya ta kubce masa.

Kafin su qarasa provision din haushi duka ya cikata,ta dinga jin ba dadi saboda yadda ake binsu da kallo,abun haushinma yadda duk 'yammatan da zasu gifta sai taga sun bishi da kallo,yau aiport din a dan cike take,alamun akwai yawan matafiya kenan a ranar.

"Kai....nasma,kinga sojan nan,wanda ke zuwa gidan general hamza" daya daga cikin fararen 'yammata uku sanye da baqar abaya ta fada qasa qasa tana tabo ta kusa da ita,wanda hakan ya faru a kunnen zahra wadda ke tsaye daga qofar provision din tana jiran fitowar haidar da ya tsaya biyan kudin ruwa da lemon da suka siya,wani abu ne ya takore wuyanta,ta juya a hankali tadan kallesu,dogaye ne don sun fita tsaho,hakanan farare ne ba kamar ita da take chocolate ba,hannun kowacce tsadaddar waya ce,wadda aka kira da nasma ta bada attention dinta inda haidar din yake tsaye,saita fidda ido
"Wow....wallahi shine,don Allah heedaya,yau ko ya za'ayi mu samu number dinsa please" daya ce ta zaro idanu
"Waye zai tunkari wannan?,ban taba gaya miki yadda muka taba yi dashi ba,tsinannen girman kai ne dashi,kulashi shine great mistake da zakuyi,ku nema number dinsa dai ta wata hanyar daban,koda cikin gidan general ne"
"Gidan general ba kowa sai matarsa,duka yaransa sunyi aure,ita kuwa ban tsammanin tana da number dinsa"
"Quiet sis....gashinan fitowa fa" dayar ta fada,duk sai sukayi shuru har zuwa sanda ya fito din,ya qaraso inda zahra take,wadda kishi ya cikawa qirji,ranta ya dinga suya.

Jerawa yayi da ita,kuma ta tabbatar yammatan nan sun bisu da kallo,a hankali ta saka hannunta ta lalubo nashi,saita hade tafukan hannunsu waje daya ta matse gam,taqi kuma duban fuskarsa.

Mamaki ya kamashi dajin faruwar hakan,saiya bi hannuwan nasu da kallo,laushi da dumin tafin hannunta yana ratsashi,ya dinga qoqarin lalubar qwayar idanunsa taqi bashi dama,har sai da sukaje kusa da inda su hajja suke sannan ta fara qoqarin zame hannunta,shi kuma yace baisan zance ba,hakan yasanya ta dakata da tafiyar da sukeyi,ta juyo tana dubansa,matsowa yayi gab da ita zai hade tazarar dake tsakaninsu,taja baya da sauri,cikin salon marairaicewa ta shagwabe masa tana masa inkiya dasu hajja da ido
"Idan kika sake lasa min zuma a baki ko?hmmmm....." Saiya gyada kao ya zare hannun nasa a hankali,ya soma yarfar dashi,kamar wanda wani abu ya maqale masa.

Cikin jirgi ta kasa ta tsare,saboda ta lura ashe jirginsu daya da 'yanmatan,number din set dinsu dama daga nashi sai nata,don haka harda qirqirar baccin qarya saman kafadarshi.

Bai fahimta meke faruwa ba sai daga baya,cikin ranshi ya dinga dariya sosai,shikam zuwan yammatan ma kamar taimakonsa yayi,saiya tallafeta sanda take kwance kafadar tasa yana tayata,ta dinga zare ido a boye tana tsoron kada fa ta wuce gona da iri.

Hotel me kyau suka sauka,dab da harami,don daga window dinsu suna iya hango masallaci,su shida harda wata 'yar qawar hajjan da suka hadu a jirgi,itama umara ta kawota
"Daki daya mas'ud da halima su zauna daki daya,daki daya kaida zahra,nida rabi mu zauna a daki daya" hajja ta tsara yadda zasu zauna,duk da mama najin nauyi amma haka suka amsa,hakanan itama zahran nauyinsu takeji,ga haidar kuwa sai yaji nutsuwa,yaji har ransa hakan yayi masa,amma saiya basar bai nuna ba saboda yasan tsiyar hajjan,don haka kowa shida kayanshi ya wuce dakinsu.

Dakine madai daici mai kyau,wanda yake dauke da duk abinda xasu iya buqata a kwanakinsu,itace qarshen shigowa don tuni haidar shi ya shigo,tana ajjiye qaramar jakar hannunta taji ya riqe mata hannu,dubansa tayi,ya kafeta da idanunsa har wani lumshewa sukeyi,saiya matsa hannun da qarfi har sai data dan saki qara
"Badon hajja tace haka ba,da bazaki ce komai ba kenan ko?,saiki bita gotai gotai ki dinga kwana a bayanta?" Kasa amsa masa tayi,saboda wani nauyinsa kunya da qimarsa data dadu a idanunta,da kansa ya sakar mata hannun yadan ja da baya sannan ya dauke idanunshi,order din abinci yayi musu sannan ya wuce bandaki.

Cikin kwanaki biyu suka gama ibadar umara,sai sauran ziyarce ziyarce da suka biyo baya,sun ziyarci gurare masu yawan gaske wadanda suke da alaqa da tarihin musulunci,manyan gurare da suke da tarihi da kuma alfarma.

Sosai imani qaunar Allah da manzansa suka sake shigarsu,a kwanakin ibada sukayi ba kadan ba,hakanan tsakanin haidar da zahra kowa ya tsinci kansa da yin addu'a cikin zuciyarsa kan katari da kyakkyawa kan tarayyarsa da dan uwansa,dukkaninsu babu wanda yasan dayansa yana addu'a dominsa.

A kwanakin da suke cikin ibadarsu duk da suna daki guda kowa yana kwancinsa,da sun dawo daga masallaci ko xiyara kowa zaiyi wanka ya samu wajen kwanciya,kusan duk kwanciyarsa a qasa yakeyi,yabar mata gadon,yayin data dinga jin nauyin hakan,duk sanda ta daga idanu ta ganshi kwance saman carfet sai taji kamar bata kyauta ba,a hankali ta tsinci kanta yana burgeta matuqa,baya ga soyayyarsa data shigeta ba tare data ankara ba,ta yi mata shigar burtu.

A wannan tafiyar ta sake gasgata zancan mahaifiyarta,duk abinda ta fada dangane da haidar din haka yake,yana lura da damuwar kowa cikinsu,baga mamanshi ba,baga hajja ba,baga abba babba ba,baga ita ba,kullum kwanan duniya saiya tabbatar babu me buqata ko matsala a cikinsu,bugu da qari ta fahimci yadda yasan addininsa yadda ya kamata,duk da ta sani cewa sam gidansu basa wasa da karatun addini,amma kuma bata tsammaci samun sani da fahimtar addini har haka daga wajen soja ba,ta manta cewa suna suka tara,iya zamansu bataga yayi fada ko fushi ko sau daya ba,kamar ma walwalarsa aka qara yawanta,ya qarfafesu dukkansu sun ribanci abunda suka je aiwatarwa,basu sake ba sai da suka gama ziyararsu kaf inda zasu iya zuwa,sannan suka soma kuma yawon ganin gari.
Chapter 62 · 0% Book details