← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 30 OF 70

Sashe 30

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Har hajjan takai bakin qofa ta waiwayo
"Waye haisam?" Tambayar data daurema zahra kai
"Haisam kuma?" Zahran itama ta maimaita sunan ta sigar tambaya wa hajjan
"Eh shi" nazari kadan zahra ta fada,tafi kowa sanin cewa ta jima da yiwa kanta shamaki da duk wani da namiji bare tace ko yana da alaqa ne da rayuwarta,don haka ta girgiza kai
"Bansanshi ba hajja" kai ta jinjina
"Bari yayankun ya dawo" bin hajjan kawai tayi da kallo saboda ta kulle mata kai,waye haisam din?,kuma meya hadinsa da yaa haidar?,data kasa canka saita tattara tunanin duka ta watsar,koma waye kuma koma.meye matsalarsu ce,itakam ta jima sa cire sabga ko sha'anin maza daga tsarin rayuwarta,hakanan ta dade da ciresu daga cikin jerin matsalolinta da zasu dameta.

Tun randa ta dawo a daren hindatu ta nemeta basu ganta ba,washegari tazo gidan,ta gaya mata lafiya lau,kada ta damu karsu nemeta,zata nemeta da kanta.

Tunda hajjan ta fita take kwance tana saqa tana warwara kan yadda lamarin zai warware mata cikin sauqi ba tare da wata matsalar ga sake sawo kai ba,tunda tana fatan wannan ta mutu,a haka har bacci yayi nasarar yin awon gaba da ita.

*_ABINDA KA SHUKA_*

A nutse take tafiya kan hanyarta zuwa gida,tun daga nesa take hango mutum biyu,daya a tsugunne daya a tsaye bisa saman kansa,haka taci gaba da tahowa tana matsar inda suke harta qaraso dab dasu,sai a sannan taga fuskokin mutum biyun sosai.

Na tsugunnen abdulyassar ne,na tsayen kuma auwal ne,sam babu alamu na walwala ko farinciki kan fuskar abdulyassar din,face ma uban gumi da yake hadawa,fuskarshi amurtuke sosai.

Kai ta dauke zata gotasu taji an riqe hijabinta,saita juyo da sauri,auwal ne,ya soma magana cikin zallar damuwa kamar zaiyi kuka
"Haba zahra....yanzu kina ganin abdulyassar haka zaki wuceshi ba zaki kulashi ba?,don Allah ki dawo ki tambayeshi me yake damunsa?,wallahi kinga munyi munyi ni da hajiyarsa ya gaya mana abinda yake damunsa yaqi cewa komai tun daxu,babu yadda bamuyi dashi ba,munyi munyi ma ya tashi daga nan amma yaqi" hijabinta ta fincike daga hannun auwal din tayi gaba abinta,tana jin auwal din na kiranta,tana kuma hangen yadda abdulyasar din yaci gaba da zama awajen.......
(Exactly haka yarinyar tayi mafarkinsa kwana biyar da rasuwarshin,na manta ban kawoshi tun a sannan ba saboda ajizanci na mantuwa).

Firgigit ta farka daga baccin daya dauketa din,ambaton sunan Allah ta shiga yi tana tunawa daya bayan daya dukkan abinda ya faru cikin mafarkin,a yanayin da taga abdulyasar din yana cikin damuwa babu ko shakka,saita miqe ta soma cire kayan jikinta ta shiga bandaki tayi wanka ta fito ta shirya,har a sannan mafarkin na maqale cikin ranta,saboda haka koda ta fito falo ta zuba abinci tana ci hajja ta soma baiwa labari.

"Zai iya yiwuwa haqqinku ke tambayarsa,ki yafe masa idan kinsan a baya baki yafe masa ba" baki zahran ta tabe
"Ni na yafe masa mana hajja,yaji da haqqin sauran da bansan adadinsu ba,da marasa zuciyar tausayi da zasu kasa mancewa bare su yafe masa".

Tana kammalawa tace bari taje wajen umminta,don tunda tazo bata je wajenta din ba,saidai yanayin yaddata amsheta,da yadda ta amsa gaisuwarta ta ya daga mata hankali ya bata mamaki,ta kuma shiga wasu wasin anya kuwa ba wani abu taji kan case din daya dawo da ita gida ba?,tunda haidar din mutuminta ne,to amma ita kanta tun ranar bata sake ganin haidar din ba,asalima kamar taji suna waya da hajja na masa fatan alkhairi kamar ma tafiya yayi wani waje,wannan abun saiya sake sanyata a rudanin data fita,ko sansa ta koma sassan hajjan saita kasa sukuni.

*_BA ZATA!_*
_baya da 茩ura_

Masu karatu muje zuwa
_Da gaske iya qarshen matsalar kenan wa zahra???_ 馃毝馃従鈥嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔忦煔娥煆锯€嶁檧锔

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN 鈥楧AI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234聽803聽081聽1300/+234聽808聽540聽5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:42 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 19
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN 鈥楧AI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234聽803聽081聽1300/+234聽808聽540聽5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
_____________________________

*_BA ZATA!_*
_Baya da qura_

Tana tsaka da sallah sau biyu inna gaje na leqowa dakin da zummae ganin ta idar din?,a zuwa na uku ne ta sameta tana zaman tahiya,saita tsaya tana dakon zahran har zuwa sanda ta kammala ta kuma yi sallama.

"Uwar masu gida anason ganinki a falo" inna gajen ta fada tana duban zahra,saita saki addu'ar da takeyi tadan ja tsaki
"Anty uwani ko?,ni sam banison zuwanta gidan nan wallahi,haka kawai baka taka mata ba baka zubar mata ba ta saka maka idanu" kai inna gaje ta kada
"Ba ita bace,hajja ce....da alhaji babba" haka kawai taji wani faduwar gaba da batasan meye dalilinta ba,haka nan sai jikinta yayi sanyi
"Tom,ina zuwa" ta fada tana qarasa addu'o'inta ta shafa sannan ta miqe.

Tun kafin ta qaraso gabanta ke dukan uku uku saboda fuskokin data hanga cikin falon,abba babba abba yusuf,abban tsakiya haidar da kuma hajja,sai umminta daga gefe
"La haula wala quwwata illa billah" shine abinda take maimaitawa,take dukka qafafunta sukayi wani irin sanyi kamar ba zasu iya daukar gangar jikinta ba,hakan yasanya tafiyarta ta koma slow harta qaraso cikin falon.

Cikin girmamawa kamar kowanne lokaci ta gaidasu,suka amsa mata fuskar kowannne babu komai a samanta,ko kuma ace ba zaka karanto wani sauyin yanayi tattare da ita ba.

Shuru ne ya biyo baya na wasu sakanni,sa'annan abba babba ya soma magana
"Zahra'u..."
"Na'am abba" ta amsa cikin sanyi da raunin murya
"Mahaifiyarki tazomin da wani al'amari wanda yake da girma a wajenmu,bayan na saurari dukka bayananta da kuma hukunci da matakin da take buqatar a dauka.....nayi magana da aliyyu gashinan,na kuma ji duk abinda ya sani daga bakinsa,saina samu hajja na kuma tuntubeta game da lamarin....tayi mana bayanin komai itama,da kuma yadda kika gaya mata,saidai duk da haka mun nemi ta bamu damar yin magana dake,duk da cewa da farko taqi hakan,to a yanzu gamu gaki inna wuro,ina son ki dubi girman Allah ki gaya mana cewa shin da gaske a hotel haidar ya ganki?" Qas tayi da kanta,qwalla na taruwa cikin idanunta,kunyar kalmar takeji kamar qasa ta tsage ta shige,dana sani da nadama na sake cika zuciyarta,ta kasa cewa komai har sai da abba babba ya maimaita tambayarshi,cikin muryar kuka tace
"Eh haka ne abba.....amma wallahi wallahi abba,na rantse da wanda raina yake hannunsa abba ba wani mummunan abu bane ya kaini,munje ne yin karatu nida sauran qawaye na saboda test da muke dasu da yawa a satin....ko sanda ya haidar ya ganni amsar abinci ya fito dani...."
"Ya isa haka,yarinya aita gama magana....idan dukkaninku baku yarda da ita ba,bakuma yarda da abinda tace din ba ni na yarda da hakan,dukkanku na fiku sanin wacece zahra'u....bama ita kadai ba,addu'ar da nake na dare ba rana ina da tabbacin ubangiji bazai wofantar da ita ba,babu wani cikin zuri'ata da xai aikata alfasha da iznin ubangiji"hajja tayi maganar da alamun ranta ya fara baci,ajiyar zuciya abba babba ya sauke,duk da dama zuciyarsu bata taba basu zahra'un zata aikata wata alfasha ba,amma yanayin yadda take magana ya isa ya shaida maka gaskiyar abinda take fada din,hakanan kuma bayanin nata ya sake sanya musu nutsuwa a ransu,saidai dukka ba zasu nuna haka tashin farko ba,dole ne su tauna tsakuwa don aya taji tsoro,don haka abba yusuf ya soma fada sosai kan zuwan da tayi,wanda yace sam bata da wata hujja ta zuwa din,tunda ba tarbiyyar gidan bace,hakanan duk wanda ya ganta akwai kallon da zai mata da kuma yadda zai fassara ta,haka ya dinga fada sosai,saboda kusan duka ya fisu zafi,yayin da kanta ke qasa hawaye wasu nabin wasu.
Chapter 30 · 0% Book details