← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 70

Sashe 48

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A hankali yake takowa direction dinta,fuskarshi a dinke idanunsa a kanta,ya isa gabanta ya duqa a hankali ya riqo hannunta ya dagata cak ya miqar da ita tsaye,duk sai tajita wani irin a mugun takure,duk da ciwon da takeji,don babu mayafi a jikinta bare dankwali.

Taku biyu yayi ya hade tazarar dake tsakaninsu,kafin ta ankara ya jata zuwa qirjinsa kamar mai shirin rungumeta,ajiyar zuciya ta subuce masa a sirrance,ya dora hannunsa a hankali a bayanta yana lalubar zip din rigarta,saita sandare a tsaye tana raba idanu,jikinta ya dauki rawa gaba daya lokacin da taji ya kama zip din ya soma zugeshi zuwa qasa
"Zzzzzan...." Take fada bakinta yana rawa kamar yadda jikinta yakeyi,ko harafi daya ya kasa fitowa daga bakinta,har sai da taji yakai zip din qasa,rigar ta rabe gida biyu,taji hannunsa saman kafadarta,yana nufin sabule mata rigar xaiyi?,ta tambayi kanta da kanta,ai batasan sanda ta cafe tsintsiyar hannunsa ba cikin hawaye tace
"Zanc.....zan cire da kaina" nannauyar ajiyar zuciya ya saki yana zame hannunsa daga cikin nata,don dama yana tunanin ta yadda zai qarasa aikin da yake pretending din yin,saiya taka da baya da baya,sannan ya juya bayansa,ya tafi zuwa window din dakin ya yaye labulen ya bude glass din ya saka kanshi a ciki yana sake sauke ajiyar zuciya gami da fidda iska daga bakinsa zuwa hancinsa,yana jin wani irin yanayi cikin jikinsa.

Kamar wata sakarya ta riqe wuyan rigar gam,tana tsaye tana rawar sanyi,tana kuma satar kallon yadda ya juya mata baya,yana nufin yana dakin xata canza kaya kenan?,idanunta ne suka sauka kan qofar toilet,sai tayi sauri ta nufi bandakin itama tana sauke ajiyar zuciya.

Bata jimaba ta fito sanye da hijabi,kamar yaji takunta ya waiwayo a hankali,Ya qarasa inda ya aje kayan,sannan ya biya ta gaban mudubi ya dauko wiper da yakan ajjiye saboda goge busashen abu,sosai ya zauna a gabanta har gwiwarsa na gogar tata,ya ciro daya daga cikin wipes din ya kamo fuskarta tsakiyar hannunsa sannan ya fara dauke duka powdern dake fuskarta.

Idanunta ta rufe gam,sanyin wiper din na ratsa fatarta,numfashinsa dake fita anutse na dukan fuskarta,yayin da kuma takejin nauyin idanunsa dake yawo saman fuskarta.

Kowanne waje idan ya saka wiper ya goge saiya kalleshi,sosai yake ganin kamanninta wanda a baya ko za'a tsireshi baisan ya fuskarta take ba,manyan idanu dake qawace da gashin ido dogaye,daga samansu kwantacciyar gira ce mai yalwar suma itama wadda ta kusa hadewa da juna,a hankali harya gangaro kan lips dinta da suka jambaki,saiya sauya sabuwar wiper,ya saka dan yatsansa a cikinta ya dora saman lips dinta ya fara gogewa.

Jikinta ta qanqanme saboda ji take kamar yana mata tafiyar tsutsa,ta gefan aliyyu kuwa haka ya dinga goge jambakin ainihin kalar labbanta na fitowa,baisan cewa ya jima yana gogesu ba sai da zahra da har yanzu idanuna ke rufe tace
"Zafi"saiya janye hannunsa da sauri yana sake daure fuska,sai yaja tsaki qasa qasa sannan ya aje abincin gefanta,ya miqe ya fice yana yarfe hannu,gami da tuhumar kansa,me yasa bai bar mata kwalliyarta ta goge da kanta ba?,daga bisani ya aza hakan a matsayin kyautata zai gwada yi mata kamar yadda mahaifiyarta ta gwadawa tashi rayuwar.

A hankali take cin abincin kamar ta rusa kuka saboda yadda sam baya mata dadi a bakinta,ga numfashinta dake wani irin nauyi,bata ci da yawa ba ta ture kwanon ta koma rub da ciki,a yanzu duk yadda taso ta daure dauriyarta ta qare,ta soma raki a bayyane don ta kasa yin shurun.

Dai dai sanda ya sake dawowa dakin bayan ya gama shirin barcinsa yaga iya abincin data ci din,sauri yadan qara zuwa inda take kwancen,sai yaja da baya,ya zuba ruwan dumin daya tafasa ya barshi yadan sha iska cikin cup din daya dauko,ya sanyata ta sake zama tana sharar qwalla.

Kallo daya yayi mata ya dauke kanshi yana tuna zahra,lokacin da qwalla ke fita daga idanunta kamar haka,tana cewa ya yafe mata mutuwa zatayi,bai taba kawo mata mutuwar ba a sannan sai gashi ta tafin,wannan tunanin yaji ya motsa zuciyarsa,wannan tunanin yasa yaji baiso yabar dakin,hakanan ya di ga jin idan yabar dakin kamar wani mummunan abu zai biyo baya,saboda haka ya koma dakinsa ya dauko duk abinda yasan zaya iya buqata ciki harda sytem dinsa da wayoyinsa ya dawo dakin,a lokacin tayi rub da ciki cikin bargo,bata juye juye kamar daxu,saidai lokaci zuwa lokaci takan motsa,da alamu ta samu relief ne daga ciwon.

Saman kujerar dakin yayi zamanshi bayan ya maida dakin dim light,saiya bude system dinsa ya soma rage aiki,aikin yadda zai gudanar da office dinsa,da kuma bataliyar rundunar sojin dake qarqashin jagorancinsa,ya soma tsara komai bisa hikima,saidai baya daukar wasu mintuna masu tsaho bai daga kai ya dubeta ba.

A hankali ya zare gilashin idanunsa da yake amfani dashi idan zai dade saman screen na waya ko system,ya ajeshi gefe yana miqa,ya sake duban inda take kwance sau babu adadi,har yanzu dai ba alamar bacci ya dauketa,saiya tattare komai waje daya,ya taka a hankali har ya isa saman katifar,ya zauna sosai,saita rintse idanunta tana jin yadda ya zauna gefan nata kamar tayi kusanci da yawa,gabanta ya dinga faduwa,sanda ya dora hannunsa saman goshinta da wuyanta bayan ya yaye bargon data rufa numfashinta ya sake yi mata wahalar shaqa,hakan yasa yadan firgita,saiya dagota daga kwanciyar da tayin,ba tre da tunanin komai ba ya zira dukkanin hannunsa cikin rigarta ta baya,ya kama maballin bra dinta yana qoqarin balle mata wai ko zata samu damar shaqar numfashin sosai,kamar yadda yaga suna yiwa juna sometimes a gida ko a battlefield idan tsautsayi ya ritsa da dayansu numfashi ya fara masa wuyar shaqa,suna cire masa duk damarar dake jikinsa don a rage masa wahala.

Ji tayi kamar zuqa daya ya rage mata na iska a duniya sanda taji dumin hannunsa a bayanta,kawai saita tafi luu gaba daya zuwa jikinsa tana jin wuta na dauke mata,bai damu ba,hakan ma saiya rage masa aiki,ya balleta gaba daya ya saka hannu ya zareta ya wurgata gefe,sai kawai ya gyara mata kwanciya saman cikinsa ta rub da ciki yadda ya fuskanci tafi jin dadin kwanciyar,bata da wani zabi da ya wuce tayi likimo,babu qarfin zame kanta daga gareshi,sannan tsoro da tsananin mamakin jinta kwance tsakiyar qirjin mutumin da bata taba kawowa kanta hakan ba yasa batajin akwai wata kalma guda daya da zata iya fita daga bakinta.

Wani dumi ne ya dinga ratsata,duka sanyin da takeji yayi nasa waje,daddadan turaren aliyyu daya zama tambarinsa ya baibaye dukka kafar hancinta,lallausan gashin qirjinsa ya dinga gogar fatar fuskarta,ta dinga jan numfashinta da nauyi tana saukewa,ba tare da saninta ba sai hakan ya zamana kamar wani communication ne tsakanin jikinta da nashi,sai ya zamana kamar tana pushing jikinta da nashi.

"Subhanallah" ya fada cikin zuciyarsa yana qaryata kansa,take ya dinga jin tsigar jikinsa na zubawa,saiya dunqule kowane hannu nasa ya damqe tafin hannunsa sosai,sai a sannan ya lura ya kuma gane gangancin daya aikata,wanda shi sam bai kawo hakan ba,ya karkata tunaninsa da son ganin ta samu relief na ciwon da takeji.

Ga mamakinta kuma saita dinga jin komai yana daidaita,numfashinta ya fara zama dai dai,hakanan ciwon shima yana raguwa da kadan da kadan,sai kuma idanunta suka fara nauyi kamar an dora mata dutse,da alamu qaqqarfan bacci ne yakeson sureta,wanda ciki qanqanin lokaci ba tare data ankara ba yayi awon gaba da ita.
23/10/2021, 08:47 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 31

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_

_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_

_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_

_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_

_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_

_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._

_MUNA KUMA SAYARWA AKAN 鈥楧AI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_

_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_

_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_

_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_

_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _

_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234聽803聽081聽1300/+234聽808聽540聽5215_

_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._

_RANO NET..!!!!_
___________________________________

Yadda yaji numfashinta na sauka a hankali cikin nutsuwa ya tabbatar masa da tayi bacci,hannunsa yasa zai sauketa saita motsa,hakan yasa ya fasa ya maida hannunsa ya ajiye,tsahon minti biyar ya sake daga hannun nasa zai sauketa,hakanan wannan karon a karan kansa yaji ya kasa,saiya sake maida hannun nasa ya ajiye yana maida numfashi gami da runtse ido,wani irin yanayi yakeji cikin jikinsa,irin wanda tunda yake bai taba jinsa ba,wani nauyin jiki da kasala yakeji,minti daya biyu saiya kalli fuskarta,duk da baya iya ganinta sosai saboda fuskar na kife a saman wuyansa ne,gaba daya jikinta dake manne da nashi ya soma takurashi gami da rikita masa lissafi.

Yayi tsammanin zai jure amma saiya kasa,don haka tilas tasa ya zameta daga jikin nasa cikin dabara,ya koma gefe yan furzar da iska daga bakinsa,ya kuma kulle idanunsa,sannu a hankali jikinsa ya soma nauyi shima,bacci ya qara maaa rauni da kasala,saiga bacci ya fisgeshi ba tare daya sani ba.

Dukkansu babu wanda ya sake farkawa, saishi ne da akayi kiran sallah firgigit ya tashi,sam ya mance a inda yake sai daya nutsuwarsa ta dawo jikinsa,saiya miqe a hankali bayan ya gama addu'ar tashi daga bacci ya miqe a nutse ya nufi bandaki.

Alwala ya daura,ya dauki dadduma a nan dakin,sannan ya dubeta yana qarasa inda take,yasa hannunsa saman pillow din da take kwance ya bubbuga,ta bude idonta dake cike da bacci sai cikin nasa,tayi saurin mayarwa ta rufe,shi kuma ganin haka ya sanyashin yin gaba yana cewa
"Lokacin sallah yayi" yana qarasa ficewa daga dakin.
Chapter 48 · 0% Book details