← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 70

Sashe 2

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Baki dukka suka sake suna dubanta,duk da cewa sun sani ba tun yau ba halin xahra din na daban ne,quruciya da rawar kai kamar bata qara komai cikin shekarunta.

Da sauri saurinta take kutsa kai zuwa sassan 'yar tsohuwar,burinta kawai ta cimmata,don ba qaramar kewarta tayi ba,sabo da shaquwa ne mai yawa tsakaninsu,wanda babu makamancin irin wannan tsakaninta da kowanne jika nata koma bayan zahrar.

'Yar kyakkyawar dattijuwa tsaye gaban freezer tana yunqurin ciro wani abu tana magana da wata matashiyar budurwa dake xaune kan daya daga cikin kujerun falon sanye da hijabi mai hannu kalar blueblack,kallo daya zaka mata kasan shekaru sun fara tura mata,saidai yanayin tsafta da son gayu irin nata ya qawata tsufan nata sosai,don kana iya hangen ragowar jan lalle dake qafarta wanda bai gama fita ba,da tajajjiyar sumarta dake cikin dankwali,wadda ke cike da furfura,saidai kuma awanke take fes cikin tsafta da tsari,sam bata lura da shigowar xahra cikin falon ba sai sautin muryarta daya karade ilahirin falon.

"Hajja!" ta fada cikin nuna zallar farinciki tana nufarta,kafin takai ga juyowa tuni zahran ta isa gareta,ta kuma cukuikuyeta gami da rungumeta tsam ta baya tana dan tsalle
"Yan makaranta....barka,barka" ta fada fuskarta na fadada da fara'a,wanda ke bayyana farincikin dake cikin zuciyarta,yake kuma alamta tarin qaunar dake tsakaninsu
"I miss you my hajja" zahran ya fada tana dariyar farinciki
"A'ah,sauya harshe dai,ni ba gane wannan surkullen naku nake ba,yanzu yayanku ya gama nashi ya fita" dariya zahran ta saki tana sakin tsohuwar,saidai sautin 'yar dariyar da taji daga gefanta yana hankalinta ya kuma hanata furta abinda tayi niyyar fada din,ta waiwaya tana duban sashen.

Kusan a tare suka sakarwa junansu murmushi
"Kicemin keda kishiyarki ne hajja......anty takwara ina yini" ta fada tana qarasawa inda matashiyar ke zaune,wadda fuskarta ke fadade da fara'a tana duban zahran gami da gyara mata wajen xama ta hanyar tattare hijabinta zuwa jikinta ta duban zahran itama
"Lafiya lau takwara.....ya makaranta?"
"Alhamdulillahi....gamu yau mun samu 'yanci"
"Aikuwa dai kam,gida akwai dadi" daga haka ta maida dubanta ga ya hajja wacce ta samu waje ta zauna
"Hajjata....me dame aka tanadarmin?" Tayi maganar a shagwabe kamar yadda ta saba
"Duk abinda takwarata keso" hajjan ta fada tana dariya,qaramin tsalle najin dadi ta doka ta fada saman kujera tana cewa
"Allah yabarmin hajjata"
"Eh qwarai,kafin ki shukamin wata tsiyar taki ba" da sauri zahra tadan bata rai tana wulqita idanu,kana ta maida dubanta ga hajjan
"Haba hajja....Allah yasa ba gaban 'yan adawa kika fada ba,da kin saka sunmin dariya,musamman su o'o" ta fada tana dan satar kallon zahra.

Sarai zahran ta fahimci wa take nufi,saita murmusa tana qunshe dariyarta gami da girgiza kai,kasancewarta mai sauqi da sanyin hali,marason yawan magana da rashin daukar al'amura da zafi
"Inna wuro....inna wuro rigima" ta ambaceta da sunan da yawanci akafi kiranta dashi cikin gidan,saita waiwaya tana duban zahran
"Eh ai nasan kin fahimta.....don nasan bakison laifinsa" ta fada tana sake bata fuska kamar wadda aka zaga,hakan ya sanya zahra yin dariya dole tana kada kai cikin jin nauyin ya hajja dake zaune a wajen.

"Sarkin neman magana,idan ya jiki kuma ya hukuntaki kice wani abu daban,shin kin shiga ma cikin gidan ma kin gaisa da mutane ko kuwa kkka zauna neman magana...." Kafin xahran ta baiwa hajja amsa hayaniyar 'yammatan gidan ta soma dosowa falon
"Tofa,Allahumma salli ala,aikin dawo,yanzu zaku taru ku dinga hanani sakat,sauqin abunma dodonku yana gari shima"
"Ni wallahi hajja ki dinga hanashi zuwa duk sanda zanzo hutu,tsakani da Allah fa hanani sakewa yake,hutun wata daya kacal din da nake samu saina qareshi cikin rashin jin dadi" baki hajjan ta kama tana dubanta,ta rasa wanne irin abune haka irin na zahran,qara kusantowar hayaniyar tasu alamun suna bakin falon yasa ta dauke kai ba tare da tace komai ba har suka qaraso cikin falon riqe da hannuwan jakankunan zahra guda biyu,wanda ta barsu a farfajiyar gidan bata samu daukosu ba saboda tsabar zumudi.

Kyawawan matasan 'yammata su biyar rigis sanye da unifoarm,wanda yafi kama da unifoarm din islamiyya,hudu daga cikinsu farare ne ba kamar kalar fatar zahran ba,yayin da daya ce kawai ta dauki kalar fatar zahra,dukkaninsu shekarunsu ba zasu wuce suma sha shida sha biyar din ba,saidai duk wadda ka kalla a cikinsu a ganin farko xaka tabbatar basu kama qafar zahra wajen kyau da zubi ba,duk da cewa babu mummuna duk cikinsu,kowacce da irin nata kyan,amma saiya zamana zahran ta zama zahara sosai a cikinsu.

Wani ihun murnar ganin juna suka saki kowacce na neman wajen zama
"Kai amma naji dadin dawowarkin nan wallahi,kinxo akan gaba" salma daya daga cikin 'yammatan ta fada,harara yusra ta jefa mata daya daga cikin fararen 'yammatan
"Eheen,kedai kin shiga uku wallahi"
"Ke kuma fa,tara kika shiga?" Salma ta fada itama tana maidawa yusra hararta duk da cewa mai kama da dariya dariya ce
"Kinga manta da ita,bani nasha ya akayi?"
"Bari mu saka labule tukunna saboda 'yan saka eyes....."
"Kunga ku tashi ku bani waje tun ban kira yayanku ba" hajja ta fada saboda sanin hali,ta sani sarai labarin nasu baya wuce na samarinsu shi yasa tayi musu haka,sosai suke wasan jika da kaka da ita,tun tana fada da fushi harta haqura ta qyalesu ta zubawa sarautar Allah idanu,harya zamana ma yanzu bata damuwa ya zame mata jiki,mutum daya ne tak da idan yana nan take samun salama,saboda dukkaninsu shakkarsa suke,kuma tsoron hukuncinsa suke.

"Idan wajen mama zaki don Allah ya zahra kice mata yanzu zan shigo na mata bayanin aiken" yusra ta fada tana duban zahra wadda ta miqe da wayarta a hannu tana murmushi
"Bafa can zata ba" hafsat wadda ta shigo daga qarshe ta fada
"Kema ai tunda kika ga ta miqe tana doka murmushi ai kinsan kwanan zancan" hafsat ta sake fada tana yin fuska,cikin dan jin kunya da nauyi zahra tace
"Kamar a kunnenshi kika fada" saita soma yin gaba cikin sauri sauri yayin da hafsat ta bita da magiyar ta tuba tayi haquri ta fice abinta tana dariya.

"Ni ina mamakin yadda soyayya ke gudana tsakanin yaya da yaa zahra"
"Ahto ai haka Allah ke lamarinsa,ku kuke masa wani kallo da bahagon hukunci,saboda AL茦IBLARKU ta bambanta ta wajen ra'ayi,kowanne bawa komai irin halinsa akwai yadda Allah ya sallada wanda zai iya zama dashi ya kuma rayu dashi".

Tsam zahra ta miqe tana maida hijabin unifoarm din jikinta,wanda har yanzu bata kai ga cirewa ba tana cewa
"Bari na shiga ciki kan ku gama lacture din" don sam bata son irin wannan dogon sharhin na hajja,gani take koda yaushe aikinta shine bashi kariya dason wankeshi a idanunsu,bagan sun riga dasun gama sanin halayyarsa ciki da waje,kuma kowacce cikinsu ta kwana da sanin wannan,so tana ganin babu buqatar dagiya wajen bashi kariya da yima halayyarsa kwaskwarima a tsakaninsu.

Kamar hajjan zatayi magana sai kuma tayi shuru kawai ta bi zahran da kallo sanda take ficewa daga falon abinta ko a jikinta,har takai bakin qofa saita dakata
"Don Allah hajja wayata,tunda na dawo nake jina ba dai dai ba,na tabbata nuruddeen nacan yana nemana wallahi,tunda yasan yau zamu dawo" daquwa wannan karon ta watsa mata
"Qaniyarki,yanzu nake muku nasiha kika tashi kika barni zaune wajen,shine yanzu kikeso naje na dauko miki waya,idan kin damu ai kinsan mazaunarta kije ki dauko da kanki" dariya tayi cike da nishadi,ita da hajjan sun saba hakan,suyi tsiya suyi dadi,duk yadda suka kai ga shaquwa da juna amma indai akan irin wannan batunne sun saba haurawa,ita sam dole saita sanyata sun jitu da juna,ita kuma tana jin wannan shine abu na qarshe a rayuwarta da bazai taba yiwuwa ba,komai nasu yasha banbam,tun kan ta mallaki hankalin kanta yadda ya kamata ta fahimci alqiblarsu tasha banbam,hakan ya haifar da duk wani abu dake gudana a yanzu.

Kanta tsaye ta nufi dakin gadon ya hajjan,harta kusa sai kuma ta sauya akalarta zuwa kitchen dinta,inda take jin qamshin abinci na fitowa.

A nutse ta tura qofar tana wara idanu don ganin wace a kitchen,kamar kullum gaji ce,'yar aikin hajjan qwaya daya tilo data jima da ita,takun shigowarta ya sanyata waiwaya tana duban qofa,cikin fara'a da washe baki ta qarasa waiwayowa gaba daya
"A'ah,ashe kina hanya inna wuro.....marhaba da uwar dakina" murmushi zahra ta saki,saboda gaje ta wajenta ce sosai,yadda ya hajja ke ji da ita haka itama gaje ke ji da ita
"Yauwa inna gaje,na sameku lafiya"
"Lafiya qalau alhmdlh inna wuro,ya makaranta?"
"Mun gode Allah" zahra ta fada tana neman wajen zama saman kanta,kusa da wasu kwanuka data gani a rufe,hannu ta miqe tana shirin budewa gami da cewa
"Me aka tanadar mana haka yaketa zabga qamshi"
"Gasunan bude ki gani,duka naki ne hajja tace a yi miki" a nutse ta dinga budewa tana dubawa,sosai taji dadi har ranta,hakan kuma ya bayyana zuwa saman fuskarta,batun yau ba ta shaida da soyayyar da kakar tata ke mata,bata san me yasa ta fita daban cikin jikokinta ba,ko don sunanta taci?,ko kuma don ita din ita daya ce ta zama marainiya a cikin tarin jikokin hajjan?,saita ture wannan tunanin ta sanya hannu ta soma daukan abinda ke cikin kwanon tana sawa a bakinta.

Duk sai data gama dandanawa sannan ta fara lashe yatsunta tana cewa
"Ashe dai 'yar tsohuwar nan na sona haka,bari naje cikin gida na gaida mutane inna gaje na dawo" ta fada tana ficewa da dan sauri saurinta ba tare data saurari abinda inna gajen ke cewa ba.

Sai data fara biyawa ta dakin ya hajjan ta dauko wayartata hade da charger,ta shiga dakinta dake sassan ya hajjan ta jona chargy sannan ta fito.

*MAMUHGHEE* _UBAIDMALEEK_

*BILLYN ABDUL*
_MAKAUNIYAR QADDARA_

*HAFSAT RANO*_MABUDIN ZUCIYA_

*MISS XOXO*_DALAAL_

*HUGUMA*_AL茦IBLA_

*ZAKU IYA BIYAN NAKU KUDIN TA WANNAN HANYAR*

茒aya___300
Biyu____400
Uku_____450
Hu蓷u____500
Biyar_____700

Zaku biya kudinku acikin wannan asusun namu na banki馃憞馃憞

0225878823 Hafsat Kabir Umar GTB

saiku turawa wannnan numban shedan biyanku(evidence of payment)馃憞馃憞

*_08085405215_*

IDAN KUMA KATIN WAYANE KO VTU/TRANSFER ZAKU TURA TA WANNAN NUMBER TAREDA SHEDARKU馃憞馃憞

聽 0903聽234聽5899
23/10/2021, 08:35 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: *KIJI TSORON ALLAH,KARKI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA MALLAKARKI BANE*

02

Falon yanzu babu kowa duka sun yoye sai ya hajjan kawai,tana zaune tana gyara falle fallen littafin dala'ilu,da alama ta karantasu ne suka kuma hargitse mata take gyarawa,don ita din har tsufanta bai hanata bibiyar litattafan addini ba.
Chapter 2 · 0% Book details