← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 59 OF 70

Sashe 59

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Da yammacine liqis,tana zaune a falon hajjanta,gidan yau kusan shuru yake saboda dukka yaran gidan suna islamiyya,saura kuma kowa yana wajen sabgarsa ta yau da kullum,kamar sassan nasu yau su biyu ne daga ita sai hajjan.

Da yake anguwar tasu babu laifi basa rasa nepa,tv ce a kunne take aiki,saidai dukka hankalin zahra yana kan wayar hannunta,charting take,kuma tana jin dadin xaman sosai.

Wayar hajja dake gefanta taji ta dauki burari,ta waiwaya ta kalli wayar da yake tana dab da ita kan hannun kujerar da take kai,number ce babu suna,yanzun hajja ta tashi bata jima ba ta shiga toilet,saita miqa hannunta daya ta jawo wayar ta daga ta kara a kunnenta,yayin da daya hannun take ci gaba da danne dannenta dashi a tata wayar
"Hajjan bata kusa,amma idan ta iso xa'a gaya mata" shuru taji anyi,duk da cewa da alamu bawai rashin network bane,tunda ga hayaniya irin daga dan nesa da inda me wayar yakeyin wayar nan tana shigo mata tana ji,saita dan maida hankalinta kan kiran,ta daga wayar ta duba taga ana kan layi,ta sake maidawa kunnenta tana fadin
"Hello....ance hajjan bata kusa,idan ta fito za'a gaya mata" jin still dai an sake yin shuru sai ta daga wayar daga kunneta hadi da jan tsaki,ta kashe kiran,ta maida wayar gefanta ta aje taci gaba da chart dinta.

Tana shirin shiga wani grp nasu na 'yan makarantar kachako unity girls,group ne na 'yan set dinsu da suka gama makaranta a shekarar,saiga saqo daga saman watsapp dinta ya shigo da baquwar number,bata fasa shiga grp din ba,sai data shiga ta gama uzurinta ta fito sannan ta duba saqon,saqone da bai wuce layi daya ba,amma saiya tsaya mata a rai,ta dinga nanatashi ita kadai
*_KINYI NESA DA IDANUNA DA RAYUWATA,AMMA KINA KUSA DA RUHI DA ZUCIYATA_*

sake shiga profile din tayi ko zata ga suna,babu suna babu dp,ta bincike contact dinta tsaf babu me irin number,zargin da yazo kanta yasa tayi saurin daukar wayar hajja ta bude,ta loda numbers din ta danna dial ko zataga suna ya fito a number amma babu,tabbacin zarginta ba haka yake ba kenan,ba haidar bane,to waye?.

Jin takun tahowar hajjan yasa ta maida mata wayar ta ajjiye,don ta lura yanzu wani gani gani take mata akan wayarta,saidai ta ganta hajjan
"Me akemin da waya ne?,bana son fa satar lamba ahto....idan mutum naso yayimin magana da kaina na dauka na bashi" shuru zahra ta mata,sai da taga ba zatayi shuru ba sannan tace
"Ni ai duka wayarki hajja babu lambar da xan sata fa,babu,ni kawai ko bandakin zaki shiga ki dinga shiga da abarki ma huta" baki ta tabe
"Oho dai,banda rashin gaskiya daga jin tahowata sai a maida waya da sauri a aje,kinga kuwa ai babu gaskiya ne" ta qarasa maganar tana zama,sai kawai zahran tayi kwanciyarta ba tare data sake amsa mata ba,tana ci gaba da maimaita saqon,jikinta yana bata daga inda saqon ya fito,amma zuciyarta ta gaza gasgata hakan,har sai data gaji da kallon saqon,kamar shi xai bata amsar tambayarta,ta sauka daga watsapp dinma gaba daya,saita dora wayar saman qirjinta ta lumshe idanunta tana tuna wasu abubuwa da suka zame mata farilla kullum sai tayi bitarsu a kwanyarta,haka nan tunasu suke sanyata nishadi suke kuma debe mata kewa.

****** ****** *******

*_BAYAN WASU KWANAKI_*

Yamma ce lis,wanda tun safiyar ranar ake fama da hadowar hadari da kuma washewarsa,saidai zuwa yammacin hadarin ya hadu sosai a sama,yana bada iska mai sanyi hadi da qamshin qasa,wanda hakan ke alamta cewa ruwan sama na tafe kowanne lokaci daga sannan

Ita da umaima da ilham ne a falon hajjan,ilham na mata manyan kitso a kanta saboda wankeshi da tayi,ya kuma isheta hakanan babu kitso,tana mata kitson suna hira jefi jefi,suna kuma kallon tashar arewa 24,gidan yauma babu mutane sosai,duk sun tafi sunan faccalar hafsat data haihu,da yake macace me kirki,kusan kowa ya santa a gidan,sauran yaran kuwa kowa yana makaranta.

Suna daga zaune suka jiyo qarar shigowar mota harabar gidan,ilham ta kalli umaima
"Kai....yau wani cikinsu abba ya dawo gida da wuri,mun shigesu yau munyi fashin makaranta....wallahi mu nema wajen buya" harara zahra ta aike musu tana cewa
"Ko kun buya saina gaya musu,ba yadda banyi daku ba ai kuka qi ji,haka ma hajja,gwara ma ku xauna suxo su ganku yafi muku sauqi" tana rufe baki hancinta ya soma shaqar mata qamshinsa,saita saki ajiyar zuciya,tana mamakin yadda ta damu da lamarinsa haka da yawa,tasan cewa ba shi din bane,kawai kamar ta saka lamarin a ranta ne da yawa shi yasa take jin hakan,don haka tayi shuru tana duban bakin qofar dakin hajja tana kallon yadda iska ke daga labulen falon.

Kamar a mafarki taga tsaiwar mutum bakin qofar falon,gabanta yayi wani faduwa data jima bataji irinta ba,ta daga kanta a hankali daga kan takalman da idanunta ke iya gani zuwa sama fuskar mutumin dake tsaye.

Haidar ne,cikin unifoarm na sojoji da suka bayyana zallar kwarjini da kamalarshi,cikakken unifoarm ne a jikinsa,saidai babu hula a a kanshi,kamar yadda ta lura ba kasafai ya fiya son sanya hular ba.

Idanunsu ne suka sarqe cikin na juna,kowannensu ya shiga kallon dan uwanshi,zuciyoyinsu na wani irin rawa tamkar an kusanta mayen qarfe da qarfe,a hankali ya soma takowa cikin falon,idanunsa cikin nata,wani irin abu mai qarfi yana jansa,hannayensa zube cikin aljihun wandonsa,tamkar me sanda haka yaci gaba da takowar har ya iso dab da su
"Ya haidar sannu da xuwa" muryoyin ilham da umaima suka karade kunnuwansu,saiya cira idanuwansa a hankali zuwa kan yaran,sam baigansu ba,bai kula dasu cikin falon ba sai yanzu,saiya gyada kai,muryarsa da wani irin laushi ya amsa da
"Yauwa,sannunku" ya qarashe zancan idanunsa na sauka kan lallausan gashin zahran da ilham takai kitso na qarshe ta kalmashe mata jelar,a hankali cikin wani irin sanyi da laushi zahran ta miqa hannu ta jawo dan kwalinta daya zame tunda aka fara kitson ta lullube kan nata,idanunta har yanzu suna qasa,ta gaza sake hado ido dashi,sai zuciyarta dake wani irin bugu,duk sai suka miqe,ilham ta dauke man kitson da comb suka nufi qofa ita da umaiman.

Kansu gama ficewa hajja ta fito,tayi turus cikin mamaki tana dubansa
"Kai kuma yaushe ka shigo?" Fuskarta na washewa da fara'a
"Yanzun nan,ko minti daya banyi ba" sakin labulen data riqe tayi,ta soma takowa ciki
"Lale marhabin,wannan irin tafiya haka babu sanarwa babu labari?,tun muna ta zuba idanun ganinka har mun haqura mun janye" dan qaramin murmushi ya saki na gefan baki yana gyara tsaiwarsa,har yanzu idanunsa yana kanta,ita ke daukar hankalinsa tunda ya sanya qafafunsa cikin falon,wani irin kyau da haske yaga ta qara masa,sai yake ganin kamar an canza masa ita,bai sani ba,tsabar kewar data addabi ruhinsa zuciyarsa dama gangar jikinsa ce,ko kuma dai hakane da gasken ta sauya,yaci gaba da dubanta ta gefan ido sanda take miqewa daga qasa zuwa kujera,saboda wani irin weak da jikinta yayi cikin qanqanin lokaci
"Barka da dawowa" ta fada kanta na kallon yatsunta data sawa lalle jiya da daddare,saboda ta gaji da yadda sukayi fari,har faratan hannunta.

Ko kadan ba tare da wani jin nauyi ba,kamar ma ya manta da hajja dake wajen ya zuba mata mayun idanunsa
"Barkanki......mun sameku lafiya?" Yadda ya amsa din ya tilastata daga idanuwanta ta kalleshi,taci sa'a kuwa sun hada ido,saiya jefa mata wani kallo data ji ya girma kanta,tayi saurin dauke qwayar idanunta,sai kuma tayi rashin sa'a suka fada kan hajja,ashe su take kallo,hajjan kuwa data gwanance wajen iya fuskewa dauke idanunta tayi kamar ba'ayi hakan ba,saita miqe ma data jiyo ringing din wayarta tana cewa
"Yauwa....ina zuwa,Allah yasa nusaiba ce".

Fitarta sai falon ya zamana daga ita sai shi,gyaran murya yayi kamar wanda ya qware,ta fuskanci so yake ta sake kallon qwayar idanunsa,wanda ta karanci al'amura masu dama a ciki,bata jin xata iya bari cikin lokaci kadan ta fadi qasa warwas,kota bari ya gane lagonta,ita din ba yau ta fara soyayya ba,tuntuni ta gama karantar kanta tsaf,ta kuma karanci inda zuciyarta tasa gaba,saidai karatun ya bata tsoro qwarai,saboda banbance babancen soyayyarshi data mata wani irin kamu ta ruwan sanyi da sauran soyayyar data yiyyi a baya,wanda yawancinsu sun mata kamu ne ta farat daya,bata taba zata ko kawowa cewa soyayyar da zata dinga shiga jikinka tana dafa ka a hankali tafi illa fiye da wadda zata kamaka farat daya ba.

Batasan ya akayi ba,tana tsaka da wannan tunanin ta shaqi qamshinsa sosai,wanda hakan yake gaya mata mamallakin wannan qamshin yana dab da ita fa,saita daga kanta da hanzari,yana tsaye a kanta ya kafeta da ido dai kamar maye,ya ciro hannunsa guda daya amma sai yayi saurin dunquleshi ya kuma janyeshi baya saboda jin motsin fitowa hajja,sannu a hankali shima ya janye jikinsa
"Zan shiga na sanarwa mama dawowata" ya fadi yana juyawa a hankali,saidai fiye da rabin hankalinsa yana kanta,so yake yaji kalaman bakinta,hakanan bai gaji da ganinta ba,yana son yajita cikin jikinsa,yaji dumin lallausan jikinta da yayi kewarsa kamar yayi hauka,baisan haka aikin yake ba,baisan harda kanshi zai nanawa hauka ba,inda ya sani,da bai fara aikin ba bare ya tafi da tabonsa,ya hanashi sukuni,rashin sukunin da saura qiris ya janyo masa damuwa kan aikin da yaje yi din.

Wata ajiyar zuciya me nauyi ta sauke,ta manta da wanzuwar hajja sam a wajen,sai suka hada idanu da ita,sake fuskewa tayi kamar bata fahimta komai ba,saidai can qarqashin ranta tana jin wani farinciki yana mamayarta,lallai ba shakka Allah shine abun godiya,ta gama karantar komai,tafiyar haidar din aiki ya zame musu kamar wani haske,kuma mataimaki wajen cikar aikinta,ba shakka lokaci yayi,lokaci yayi da za'a kawo qarshen komai kowa ya huta,zatayi qoqari tayi dukkan abinda ya dace,amma zata bashi sati daya kacal taga shin xaiyi wani motsi daya dace shima?.
"Tashi kije ki sama masa wani abun da zaici kafin ya kintsa,tunda yau tazarce kukayi mana saboda tsabar ganda da qyuya,kinsan kuwa shi din ba ci xaiyi ba" karon farko.....lokaci na farko da taji ranta babu damuwa babu takura saboda hajja tace ta sama masa abinci....lokaci na farko da taji tana marmarin shiga kitchen,tun daga qasan ruhinta zuwa zuciyarta,taji a ranta cewa she's ready a dai dai wannan lokacin tayi dukkan girkin daya dace,don haka ba bata lokaci ta yiwa kitchen din tsinke.
Chapter 59 · 0% Book details