← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 70

Sashe 37

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yana shirin xama su husna na gaidashi,ya amsa musu,duk sai suka miqe suna barin falon,sai ya zamana daga shi sai hajjan a falo,muryarshi a dake ya soma gaidata
"Barka da dare hajja....an yini lpy"
"Qalau muke" ta amsa masa a kaikaice
"Ka gama guje gujen naka?" Ta tambayeshi tana tsareshi da ido,dubanta yayi kafin ya amsa mata
"Gudun me fa?...ba inda naje,kawai shiryen shiryen bikin qarin matsayin nan ne ya sanyani gaba,yazo kuma ya hade da wannan"
"Kai ka sani,nidai ina sake jadda da maka wallahi ka fita idanuna....ka kuma kiyaye ni,idan ba haka ba...bakai kawai ba,har tsohonka bazai ji da dadi ba" ta furta maganar tana kanne ido gami da nunashi da yatsa,sumeshi ya shafa yana furzar da iska
"Ya salam....to nikam hajja bansan me kikeso ba dani kuma,duk abinda kika tsara anyishi,saura me kuma?,me ya rage?" Zamanta ta gyara sosai tana kallonshi
"Ai kafi kowa sani,tunda dai kasan cewa cikin satin nan matarka zata koma makaranta ko?"
"Matata?" Ya tambaya yana jin kalmar wata banbarakwai,da confidence dinta ta gyada kai
"Eh,matarka zahra'u.....kana nufin mu ko dangin uwarta ne zamu ci gaba da dawainiya da ita?,ko bakasan haqqoqin mata akan mijinta ba na kira malami su karanta maka?" Ta qarashe da tambaya gami da zuba mishi idanu,idanunsa kawai ya dauke daga kanta ba tare da yace komai ba,kamar bazai magana ba sai kuma ya amsata
"Nima cikin satin nan zan koma,saboda 'yan kwanaki ya rage na karba sabon matsayina" kafada hajjan ta daga
"Oho maka....kaika jiyo,ka fara sallamarta tukunna da dukkan abinda ya dace,idan yaso kafi ruwa ma gudu"
"Hajja hajja" ya kira sunan nata har sau biyu,tsohuwar tana son takai masa iya wuya,itama sai tace
"Ali...ina jinka,da magana ne?" Kai ya kada yana miqewa
"A bani abinci idan akwai"
"Zakaci iya na kwanakin dana diba maka ne kawai wlh,don bazanci gaba da aikin baban giwa ba" ta fada kamar me qunquni,yaji me ta fada amma sai yace
"Magana kike hajja?"harara ta dalla masa,saboda ta fuskancin yanzun so yake ya tsiro da wasan jika da kaka tsakaninsu
"ban sani ba,nace ka quce dakinka za'a kawo maka"
"Godiya nake" ya fada yana ciro wani turare daga aljihunsa ya aje gabanta,tabi turaren da kallo kana ta raka aliyyun da ido.

Turarenta ne da take amfani dashi,take kuma matuqar so,aliyyun yasan lagonta lokutta da dama,ba banza ba take sonshi duk cikin jikokinta,koda tayi fushi ta ruwan sanyi yake sauketa,sai tasa hannu ta dauka turaren,tana qwalawa inna gaje kira.

Cikin sakanni ta bayyana
"Gani hajiya"
"Shiryawa Aliyyu abinci maza gaje"
"Toh...toh,yanzu za'a kai masa?" Kai ta girgixa
"A'ah....ki hada kawai,matarsa ce zata kai masa"
"To toh,hakan yayi kyau" ta fada tana juyawa zuwa cikin kitchen din tana murmushi,ko ita abun yayi mata sosai,ta jima a ranta tana qiyasta auren aliyyu da xahra,ta dade tana sha'awar haka,amma bata taba furtawa ba,sai gashi Allah ya haskawa hajja,don haka cikin kuzari ta shirya komai cikin wani foldable basket mai kyau,sannan ta dawo ya shaidawa hajjan ta hada,ta amsa mata sannan ta turata ta shiga daki ta kira mata zahra,sai a sannan ma abunda ya faru dazu ya dawo mata kai,wato bisa dukkan alamu tajiyo maganarsa ne tun kafin ya shigo shi yasa tabar falon?,saita saki murmushi kawai cikin ranta tana addu'ar Allah ya shiryesu,ya kuma hada kansu.

Tare da inna gajen suka fito,tana dan rarraba idanu a falon ga zatonta yana nan saboda qamshinsa daya barwa falon,sai data tabbatar baya nan sannan ta qaraso tana sakin jikinta.

"Dauki abincin nan ki kaiwa yayanku" tace da ita tana murtuke fuska don kada ma ta kawo qabli da ba'adi,ido tadan fiddo
"Waiya musty ko ya abubakar?"
"Zaki" hajjan ta amsa mata a taqaice,ba shiri ta nemi wajen zama gefan kujera saboda yadda maganar taxo mata ba zata,wanne irin masifa hajja keson janyo mata tana zaman zamanta ne?,meye hadinta da kaiwa ya aliyyu abinci?,ita kaf rayuwarta ma zata iya tuna sau nawa ta shiga sashensa,shigarta ta qarshe ma kusa shekara goma,don duk abinda zai kaita dakinsa bata yarda ya hada da ita,iyakarta dakinsu ya musty,ko su dinma ba'a barinsu suje saida dalili,
"Amma hajja da kin baiwa su ilha..."
"Ban isa na aikeki ba kenan?" Ta jefa mata tambayar tana kallonta,xancan umminta ya dawo mata,saita saita fuskarta tana girgixa kai
"A'ah ba haka nake nufi ba,bari na dauko mayafina" ta fada tana miqewa,hajjan tabi bayanta da kallo cikin ranta tana dariya gami da cewa
"Kyayi kya gama".

Ta jima a dakin tana jan innalillahi,gaba daya hajjan ta sakota gaba,meye na aikenta wajensa bayan tasan yadda suke dashi?,sai data gama dibi dibinta sannan ta zari zumbulelen hijabinta da baka ganin komai sai hannayenta da saman qafarta ta zura ta dawo falon ta dauki kwandon ta fice.

A hanya ta hangi aslam dan abban tsakiya,ta miqa masa kwandon
"Yauwa mutumina,don Allah kaiwa ya haidar yana dakinsa kazo na baka lada" baya yadanja yana dubanta
"Wa?,ni?,ba ruwana inna wuro,kinga,mommy ce ma ta aikeni zan karbo mata gugar kayanta zasu fita yanzu da abba".

Yaran gidan kusan hudu ta hadu dasu kafin takai,saidai kowa ta nemi yakai abincin sai taga yaja baya,abun saita lura kamar hadin baki,ko suna tsoron wani abu,tunda dai tasan yaran gidan kaf da tsananin bin na gaba dasu,koda kuwa ba wasu shekaru masu yawa ka basu ba,hakanan basu da qiwa sam koda ga jama'ar waje bare na cikin gidan,da haka da haka tana haduwa dasu kowa na bata uzurinshi har ta isa kofar dakin nashi.
23/10/2021, 08:44 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 23

*Assalamualaikum warahamatullah taala wabarakatuhu*
08121491609
*Aisha s bayero traditional medicine and herbal reaserch center*
08121491609

*_MUN TANADAR MUKU INGANTATTUN MAGUNGUNA WADANDA BABU NA BIYUNSU KAMAR HAKA_*

*Step 1*

1_maganin sanyi
2_maganin niima set
3_maganin nankarwa
4_maganin kiba babba 8kkkarami
5_maganin hips
6_maganin gyaran nono
7_maganin rage kiba
8_maganin saka feeling
9_maganin cida kwai
10_zuma yar asali
11_maganin basir kowanne iri
12_hodar niiama
13_maganin mallaka
14_gumbar nonon rakumi 10k boket馃槰
15_gumbar madara 10k boket馃槰
16_turaren farin jini
17_kaza Mara kwai
18-turaren mallaka 3step
19_hadin matar minister
20_ kaza me kwai

*Step 2*

1.Turaren mallaka me kwalba
2. Me kunama Dan matsi 3k
3.tuaren goshi
4.turaren girji
5.tauwadar Mata
6.memory
7.kahon mallaka 8.yajin maza tea din maza
9. Dambun matsi
10. Man ayu 11.man damo pure daga zuwa sama
12. Kwallin idonka idona
13 garin Sha daka me kyau
14. Kubewar Mata gasunan dai da yawa bazan iya lisaafawaba harda na kyakkayin cinyoyin da matse matsi kina shafawa zakiji wasai

08121491609
dadai sauransu serious buyer yabiyoni private
me shawara ta bari saita gama karki batamun lokaci please

*_ku tuntubeni ta wannan number wayar_*馃憞馃徑馃憞馃徑馃憞馃徑

08121491609

Tana tura qofar dakin wani bala'e'en sanyin Ac da qamshin freshner ya mata sallama tun kafin takai ga shiga,ashe da gaske ne ranannan data ji su hafsat na gulmarsa kan yadda yake babbakawa kansa ac,saita maida hannayenta cikin hijabi saboda sanyi,sannan ta sake tura qofar ta shiga sosai bakinta dauke da sallama qasan maqoshinta.

Tsaf dakin yake,hakanan babu wani tarkacen kaya duk da girmansa,babban gadone lafiyayye guda daya,sai kujera one sitter da two sitter da tv plasma daga gabansu kadan zaune saman wata tv stand ta zamani me tsari da yawan lockers,wanda ta tabbatar anan ya boye tarin takardunsa masu muhimmanci,bayan dan qaramin study room dinsa dake manne da dakin.

Haidar dake zaune saman daya daga cikin kujerun ya daga kanshi ya amsa sallamar,suka hada idanu saiya maida kan nasa qasa yana ci gaba da duba takardun daya barbaje a gabansa.

Yau daya sai taji ya mata wani irin kwarjini daya ratsa har cikin qasusuwanta,duk da cewa ba yaune karon farko data saba ganinsa ya hade girarsa haka ba,a'ah....dama dabi'arsa ce hakan.

A nutse ta qaraso gabansa ta aje kwandon,so tayi ta tafi amma suna hada ido sanda take shirin tashi saita koma ta zauna,kaf gidan sunsan tsarinsa baya sarving abinci da kansa,tuntuni sun saba al'adarsa haka,yana da wata izza da jin sarauta a jininsa.

Tana kammale kwanukan taji ya magantu cikin qasaitar nan tasa,takarda da biro ne ya aje gabanta
"Ki rubuta duk wani da kike buqata na komawa school",daga haka ya dauki bowl din dake daukw da farfesun danyan kifi ya saka spoon ya fara shan romon a nutse bayan ya harde qafarsa cikij ta juna,yayin daya maida kallonsa ga tv dake aiki kan qaramin sauti da bazai damu mutum ba.

Ta gefan idanu ta kalli takardar sannan taja tsaki cikin ranta
"An gaya masa na damu ne da wani kayan hannunsa,koda can shi yakemin" tana kaiwa nan ta miqe abunta ta soma takawa zata bar dakin.

Taku biyu rak tayi ta tsinci dakakkiyar muryarsa yana cewa
"In kika sake kika fita saina biyoki har gaban hajjan na kakkarya wadan nan sili silin qafafun" yadda yayi maganar ya tabbatar mata bada wasa yake ba,duk da taji haushin ba'ar da yayi mata haka ta shanye,ta juyo tana zumbure zumbure,ta dawo ta samu can gefe ta zauna bayan ta dauko takardar.

Abu uku kawai ta rubuta taje gabansa ta ajjiye,da idanu ya kalli rubutun,kamar zaiyi magana sai kuma ya janye idanun nasa ba tare da yace komai ba,hakan ya bata damar ficewa tana gunguni cikin zuciyarta.

Koda ta koma da kallo hajja ta bita,saboda bata tsammaci dawowarta da wurwuri haka ba,amma saita shanye,bata ce da ita komai ba.

Washegari tana kwance hajjan ta shigo
"Tashi kije ki gyara dakin mijinki" batasan sanda ta dawo rigingine daga kwanciyar rub da cikin da take ba fuskarta a hade tana duban hajja
"Waye kuma mijina?" Daquwa ta watsa mata
"Ungo nan....nace ungo nan,zaki tashi ko sai na radeki?" Ta fada tana kai mata dundu,tuni ta hantsilo daga gadon tana sosa bayan kamar ma ta sameta tana kuma duban hajjan
"Abun har yakai haka hajja?" Ta tambayeta kamar zata saki kuka
"Yama fi haka,indai zaki dinga min musu da shegen taurin kai....kuma indai kika ci gaba da yimin haka naga wanda ya isa ya karba miki takardar taki duk duniya" da haka ta juya ta fice daga dakin.

Tsoron furucin da tayi ne ya sanyata zarar mayafin doguwar rigar jikinta ta yafa tana ta mita a haka ta fice.
Chapter 37 · 0% Book details