← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 70

Sashe 35

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yakai hannu zai dauka idanunsa suka sauka kan dan qaramin hoton marigayiya zahra dake cikin wani qawataccen frame ruwan gold,saiya fasa daukan envalope din,ya soma kai hannunsa ya shafi fuskar hoton dake dauke da fuskar zahran,sannan qasa qasa ya furta
"Rest in peace" ya miqa hannu ya dauki takardar ya koma saman kujera guda daya dake dakin ya zauna ya farketa ya zaro takardar dake ciki.

Girman saqon da takardar ke dauke dashi ne ya sanyashi miqewa tsaye qyam cikin mamaki,gefe daya kuma wani farinciki na son kunnuwa tsakiyar bacin ran da yake ciki ya kuma shafeshi cikin mintuna qalilan.

Takarda ce ta qarin girma,wanda sam bai taba kawo hakan ba a ranshi,saboda shekarunshi da shekarun daya dauka yana aikin basu isa bashi wannan matsayin ba,a qalla saiya shekara ashirin da hudu sannan zai taka wannan matakin,amma sai gashi lokaci daya!,dare daya ya samu wannan matsayin.

Har ya nufi qofa da niyyara isa ga hajja da wannan albishir din sai yaja ya tsaya saboda tuna abinda ke wakana,rasa wanda zai raba labarin dashi yayi,don haka ya zauna ya lalubo wayarsa yana neman su abu sufyan,yana da yaqinin labarin bai fasu ba tsakanin manya da qananun sojoji da tuni sun kirashi.

Ya dan jima suna waya dasu,kafin wani lokaci kuma sai wayoyin mutane suka soma turereniyar shigo masa,da alama labari ya fasu,dole ya katse duk wani kira,ya shiga cikin gida ya shaidawa mama da abba babba,amma saiya share 'yar tsohuwar bai shiga ya gaya mata ba.

Kafin ya kwanta sai daya kira general yayi masa godiya sosai bayan ya hadashi dasu abba sun masa tasu godiyar,jin bai tada masa batun su haisam ba yasa ya share shima baici komai ba,saidai ya gaya masa ana buqatarsa a office saboda wasu akwai shirye shirye na amsar office da kuma bikin qarin girman,shi a gobe zai koma wajen aiki,ya amsa masa da yana tafe da yardar Allah.

*********washegari***********

Gaba daya fuskarta ta kode ta jeme kai kace zaman takaba takeyi,saidai abinda ta fuskanta shine babu wanda ma ya damu da damuwarta,tun bayan da zancan ya soma zaga gidan duk wanda ta kalla sai taga fuskarshi a sake take da walwala,bugu da qari kuma saiga kira daga hafsat yusra yasira da salma,duk wadda ta kira tana kiranta ne da ihun murna gami da tambayarta ya akayi haka ta faru?,baqinciki bai iya barinta cewa komai,saidai ta datse kiran,kuma ba zata sake daga kiran su ba,saidai suyita kira su gaji,daga qarshe saidai ta jisu suna waya da hajja daga falo,daga nan babu me sake kiranta,da alama ta gaya musu yadda aka qulla abunne ba bisa son ran kowannensu ba.

A kullum idan gari ya waye dama bata da wani aiki zaman daki tun daga wancan lokacin,saidai wanka sallah da kwanciya,abinci kuwa sai taji kamar cikinta zai hade da bayanta sannan zata dan tsakura ta koma ta kwanta.

Yauma kamar kullum,tana nan zaune gefan katifarta bayan ta gama wanka ta saka riga da zani na atamfa hajja ta turo qofar dakin ta shigo dauke da kwanukan abinci,wanda kullum ita da kanta ke kawo mata koda ba zata kulata ba,zata kawo mata ta ajjiye ta juya ta fita abinta ta barta.

Yau din data dora abincin saman inda take ajjiye mata saita qaraso inda zahran ke zaune ta zauna gefanta
"Ki zauna dai kiyita sanyawa ranki damuwa....ki hadu da wani ciwon tunda qananun shekarunki" karon farko tun bayan zancan da hajjan tabi ta kanta harma ta tanka ta,sai qwalla ta cika mata idanu,ta zumbura baki murya a dasashe tace
"Idan ma ciwon ya kamani aiba damuwa kikayi dani ba,kinga saina mutu kowa ma ya huta" murmushi ne ya kunbcewa hajjan
"Au Allah....saboda na miki gata na baki dandasheshen jikana....shine zaki ce haka?,au ashe?,sakayyar ma da zakimin kenan,maimakon ki bani danqwalelen goron albishir?"
"Ni so nake.....haka kawai ina zamana....saboda Allah bai kawomin miji ba shine za'ayi sadakata" ta fada tana fashewa da kuka,jikin hajjan sai yayi sanyi,saita koma cikin seriouse dinta bayan ta dafa bayan zahran
"Zahra'u,ki tsaya ki nutsu kiji abinda zan gaya miki,na tabbatar dama da farko zakiji babu dadi,zakiji na takuraki,zakiji ban miki adalci ba,saboda kaf cikin 'ya'yana ko jikokina babu wanda na taba yiwa irin hukuncin dana miki....amma abinda nakeso ki sani shine,soyayya da qauna ce tasa nayi miki hakan,na tabbatar ko ba dade ko bajima zakimin godiya,zakiji kuma dadin wannan abun dana miki,alfarma daya nake nema a wajenki idan har na isa,idan har ina da kima da mutunci a idanunki" shuru hajja tayi tana kallon zahra da kukanta ya tsagaita,saita dora
"Na sani cewa a yanzu baki da wani daya shiga zuciyarki bare kice na miki karan tsaye....da wannan nake neman alfarma daga wajenki daki sassauta zuciyarki,ki cire wannan quncin takura da takunkumin da kika sanyawa ranki,ki yi juriyar maida komai ba komai ba....ki bawa aliyyu dama....na miki alqawarin cikin shekara daya indai ya kasa shiga zuciyarki da kaina zan amsar miki takardarki kije ki auri dukkan wanda yayi miki,kuma babu wanda zai tada hukuncina....abinda nakeso shine kawai ki kwantar da hankalinki" shuru tayi tana nazarin maganar hajjan tare da kokwanto,saidai cikin hikima da dabara irin tata ta tsofaffi ta samu tadan sauketa kadan,aka samu canji duk da ba wani me yawa bane.

_hello assalamu alaikum zafafa fans,kuyi haquri da jina shuru jiya,bana jin dadine,yauma da qyar na hada wannan,so idan kun jini shuru gobe kuyimin uzuri,amma in sha Allah ma zan qoqarta,kuci gaba dai dayi mana uzuri kamar yadda kuka saba,mu din 'yan adam ne kamar kowa,mun gode da yadda kuke fahimtar damuwoyinmu_馃檹馃徑馃檹馃徑馃檹馃徑馃グ馃グ馃グ
23/10/2021, 08:43 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 22

_*LAVENDER RESTAURANT..*_
_(Palace of mouthwatering food/delicacies)_

_IDAN KUKAJI GANGAMI DA LABARI, INA MASU SON INDA ZASU SAMU INGATACCEN ABINCI MAI DADI DA LAGWADA? KAI BA ANAN MUKA TSAYA BA, INA SABBIN AMARE? MAMAs, YAYYU? DA KANNEN MU MASU SON KOYAN GIRKUNAN YAN GAYU NA KASAR NIJERIYA DA KETARE?_

_*TO KU MATSO...! AT LAVENDER RESTAURANT GOTS YOU COVERED. ABINCIN KASASHE DA DAMA MUKE KOYARWA,,COME LETS UPGRADE YOUR FOOD TIME TABLE, MATSO KUSA YAR UWA GA DAMA DA ZAKI CANZA YANAYIN ABINCIN GIDAN KI, KOWA YASAN IYA SARRAFA ABINCI NA TAKA RAWAR GANI A GIDAJEN AURE. KAI KO BUDURWA CE INDE KIN IYA GIRKI ZAKIGA KOWA YANA HABA HABE DAKE.._*

_*UNCLES, DADDIES, BROTHERS., NEWLYWED HUBBYS..! KU ZO KU YIWA 鈥榊AYAN KU, MATAN KU DA KANNEN KU RAJISTAR WANNAN HARKA TA KOYAN GIRKI.._*

_*Lavender catering school zamuyi practical class. zamuyi 30 dishes continental,snack & desserts, traditional dishes, drink. Fee din 40k NE. phone number WhatsApp and call 09080299283 akwai discount na 5% ga mutum uku farko wadanda sukai register aranakun independence 1/10/2021 to 3/10/2021 Nigeria @ 61_*

_*ZA鈥橝 FARA CLASSES RANAR 14/10/2021. WATO SHA HUDU GA WATAN OKTOBAR DA MUKA SHIGA YAU._*

_*GIRKE GIRKE GUDA 30馃槴馃槰AKAN DUBU 40 KAWAI, HARDA BONUS NA SNACKS, DESSERTS, TRADITIONAL AND MODERN DRINK, GARGALIYA DA ZAMANI馃WATA DAYA CHAS ZA鈥橝YI ANA KOYAN GIRKE GIRKEN. _*

_*KU SAKE KARANTA WANNAN BONUS DIN馃憞馃従RIGIJI GABJI_*

_*Nigeria @ 61 _*
_*COOKING COMPETITION!!!_*

_*from lavender Catering ina masu son koyon girki ga dama zaku shiga gasarmu ta girki bayan kunyi register damu akan 10k,wanda yazo na 1zai shiga ajin mu free hade da wasu prize din na 2 da na 3 kuma zasu bayar da rabin kudine da wasu prize suma saura kuwa zasu ayi musu ragin 5% da wasu prize wannan gasa zamu yita ranar lahadi ne 3/10/21 zamu rufe registration na gasar ranar asabar_*

_*LAVENDER RESTAURANT: NA GARIN KANO, CLASSES DIN AKWAI PRACTICAL AND ONLINE CLASS GA WANDA KE NESA_*
________________________________

Cikin kwanakin ikon Allah kawai zahra take kallo,yadda aka tada shirye shiryen daurin aure gadan gadan,saiga dinkuna hajjan tayi mata na shaddodi da atamfofi,ko kallon inda suke ita dai batayi ba,saboda ta fuskanci kamar ma kowa goyon bayan abun yakeyi.

Ta fannin aliyyu kuwa shiryen shiryen qarin girma da za'a masa ya janye hankalinsa sosai,don har wani lokacima yakan sha'afa da batun idan ba wani bane daga gida ya tada masa zancan,baya ma samun zama sosai,wani lokacima ba'a gidan ko a garin yake kwana ba.

Ana ya gobe daurin aure saiga baqi sun fara cika gidan,tun zahra na daukar abun me sauqi harta fahimci babba ne,saiga su yusra ma duka sun hallara,salma ta soma mata zancan itako ko qunshi da gyaran kai mana ayi mata a ranar dai.

Yadda ta rufe ido tayi ma salman tas da duk wanda ya goyi bayan zancan salman ya tabbatar musu da cewa lallai a wuya zahran take,ta dinga balbala masifa da bala'i har sai da kowa ya dare ya barta,ta buga tsaki ta sakawa dakinta key tayi kwanciyarta,bata sake bude dakin ba har zuwa washegari da safe,data tashi tana jin yunwa,sassan hajjan kuma akwai baqi,sa'annan haushin kowa takeji,batason yiwa kowa magana bare ta buqaci abinci a wajensa,don haka ta zurma hijabinta babu wanka ko kwalliya tattare da ita,kamar ba ita ake shirin daurawa aure ba tayi sassan umminta.

Abinda ya sake daure mata kai haushi ya cikata shine samun ummin nata da tayi tayi wanka abinta ta shirya cikin dinkin shadda sabuwa gal,daga ita har ilham da yusuf da sulaiman dukka iri daya.

Can dinma akwai baqi,duk da baikai cikar sassan hajja ba,saita gaisa dasu suna kiran amarya amarya,ba wanda ta tankawa,abincinma ji tayi ya fice mata a ka,don haka ta koma da baya zuwa sassan hajjan.

Mutane ta tarar yanxun a dakin nata ciki harda suwaiba,koma bayan dazu data fita babu kowa a ciki,hasina dake zaune gefan katifarta ce tace
"Ah,hala sabani mukayi,ummi tacemin kina nan,na shigo kuma ban tadda ki ba"
"Eh" ta amsa a taqaice tana isa bakin madubi ta dauki brush da maclien tayi bandaki,da hanzari hasina ta miqe tabi bayanta cikin bandakin.
Chapter 35 · 0% Book details