← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 49 OF 70

Sashe 49

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A nutse ta sauka daga gadon zuwa bandaki tana tuna abinda ya wakana daren jiyan,dukka jikinta babu abinda yake sai fidda qamshin turarensa duk motsin da zatayi,duk sai taji wani irin kunya da nauyinsa sun saukar mata wanda bata taba ji ba sanda ta tsaya gaba madubi ta tuna shi ya cire mata bra,ita kadai a bandakin amma sai ta dinga ji kamar yana kallonta,tasa hannu ta cukuikuye rigarta ta nufi gaban sink ta daura alwala sannan ta fito.

Tana fitowa daga bandakin sanda ta miqa hannunta ta baya tana rufe qofar toilet din shi kuma yana shigowa,kai tsaye idanunsa suka sauka a kanta,rigar jikinta ta kwanta sosai a fatarta,ta yadda duk wanda ya kalleta yasan babu brazier a jikinta,hakan ya baiwa albarkatun qirjinta damar tsayawa sosai kowanne a muhallinsa.

Kamar wanda aka sanyawa shocking haka yaji,ya dauke kansa da wani irin sauri yana qarasa shigowa ciki ya kuma nufi kan gado kai tsaye,yayin da ita kuma ta qame a tsaye cukuikuye da gaban rigarta,gabanta na wani irin faduwa saboda lura da tayi da inda yake kalla din.

Saman katifar ya haura,ya dage filo ya dauki wayarsa,da alama ita ya manta ya dawo dauka,saidai yana miqewa yaci tuntube da breezier dinta,saiya janye qafarsa a hankali ya sauko ya fice.

Da sauri ta qarasa ta sakawa qofar key tana sakin numfashi,wai wannan wane irin abun kunya ne haka,sai data kusan makara sannan ta samu tayi sallar bayan ta tattare katifar.

Har wajen sha daya saura na safe tana dakin bata fita,duk da tayi wanka,amma nauyin haduwa dashi yasa ta kasa fita,uwa uba kuma mararta daketa qulle mata,addu'a take Allah yasa kada period din yazo sai ta koma gida.

A hankali ta bude qofar sanda taji anyi knocking,saita labe daga bayan qofar ta yadda bazai iya hangota sosai ba,haka itama.

Muryarsa kawai taji da mayen qamshin turarensa yana cewa
"U know you r sick....ki fito ki samu wani abu kici"
"Okey" ta amsa masa tana sakin qofar,ta koma cikin dakin tana laluben me zata yafa,ta ciji yatsa tayi Alla wadarai da wadanda suka hada mata kaya,kaf kayan babu hijabi ko daya,sai sannan ta tuna yace mata ta rubuta list na abinda take buqata amma batayi hakan ba,saboda batason abinda zai ja ta dade bata koma gida ba,kodon jarabawarta data tabbatar duk abinda akw ciki ba zasu wuce two weeks basu fara ba,inda kuma ta rubuta din wala'alla ta hada harda shi,amma yanzun idan sun dawo dole ta rubuta abinda ba'a rasa ba,dole qanwar naqi ta dauki mayafi ta yafa.

Saman dining ta sameshi da waya a hannunsa yana dannawa,yana jin takunta ya dago kai,ga mamakinsa ba inda idanunsa ya sauka sai a qirjinta,yayi maza ya dauke kai yana jan tsaki can qasan ransa,mugun haushin kansa ya kamashi,meya kaishi ma daga kai koda fuskarta zai kalla bare wani sashe na jikinta,inda Allah ya taimakeshi bata kula da hakan ba harta qarasa,taja kujera ta zauna,ta gaidashi ya amsa yana ci gaba da danne danne a wayarsa,bata ma sani ba shi ko yayi breakfast din ko beyi ba,ta hada ruwan zafi ta fara kurba a hankali,tana jinta duk a takure saboda zamanshi a wajen.

Tayi rabin ruwan zafin taji 蓳ul daga qasanta
"Innalillahi" ta fada cikin faduwar gaba,da alama period dinta ne yaxo,ita kadai ta dinga wara idanu tana tunanin ya zatayi,bata gama wannan tunanin ba ta tsinci muryarsa yana cewa
"Ki sauri ki gama ki sameni a mota"
"Toh" ta amsa a sanyaye,yayin da shi kuma yayi ficewarsa.

Haka taci gaba da raba idanu da tunanin me zatayi,tana jin kuma yadda jinin ke flowing a jikinta,har zuwa sanda ya aiko mai gadi ya tsaya daga qofar falo yace mata ta fito inji oga,saidai tashin ya gagara,don ta tabbatar ba jikinta kawai ba,har kujerar da take xaune a kai ta baci.

Zabura ta kusa yi sanda ta tsinci muryarsa daga bayanta,ta waiwaya a hankali ta dubeshi,qwayar idanun nashi ne masu nauyi samanta yana dubanta
"Karki batamin lokaci fa...." Abinda kawai ta iya ji kenan daga bakinsa,bata da wata sauran dabara kuma,don haka ta miqe kai tsaye kawai ta tsaya cak ba tare data iya ce masa komai ba.

A hankali idanunsa ya sauka a inda ta tashin,ya fahimta sarai,don ta danyi staining wajen,saiya dauke idon nasa kawai ya juya ya fice.

Ta tabbata ya ga abinda takeson nuna masan,don haka ta nufi dakinta a hankali,ta wuce bandakinta,ta gyara kanta ta sake wanka gaba daya.

Tana tsaye waje daya a tsakar dakin tana tunanin me zata saka ta tare?,ko dankwalinta zatayi amfani taji an turo qofar dakin,duk sai ta duburbuce,ta rasa inda zata boye kanta.

Shi dinma dai kamar dazun,inda idanunsa suka sauka daxu yanzu ma haka
"Ya salam" ya fada yana aje mata ledar gamida juyawa yabar dakin,annan wanne irin jarraba ce yakeson dorawa kanshi?,wani mugun haushin kansa ya kamashi,yaja wani dogon tsaki kamar zai tsinke harshensa,ya shiga motar yana rufe murfin da qarfi kamar ita tayi masa,sumarshi yaje shafawa da hannu daya yana furzar da iska daga bakinsa,can cikin zuciyarsa kuma yana jawa kansa warning,tare da son gayawa kansa da zuciyarsa hakan bazai sake maimaituwa ba.

Sai daya fita taja ledar ta som duba abinda ke ciki,pad ce da pants masu yawa,wanda tasan sundi qarfin buqatarta na dan lokaci,sai ta cira wanda zatayi amfani dashi,ta dora ledar saman akwatinta sannan ta bareta ta saka,tayi mamakin yadda akayi size na pant din yayi mata dai dai.

A gurguje ta shirya sannan ta fito,tun kafin ta qaraso ya hade ranshi sosai,ya kuma dauke kansa daga direction dinta harta qaraso ta bude gidan gaba ta shiga.

Tafiyar kurame dai sukayi kamar kullum,har suka isa ginin da kallo daya tayi masa ya gaya mata asibiti ne,private asibiti,daga yanayin tsarinsa da gininsa kadai ya isa ya gaya maka kudin da ake lasa na marasa lafiya,saidai kulawar da suke baiwa mara lpy ya cancanci kudin da suke karba.

Da alama nan yake zuwa idan yana garin,duk da cewa akwai na sojoji,saidai wala'alla kayan aikinsu da ma'aikatan ne basuyi masa ba.

Tare suka shiga ganin likitan,yana tsaye ta gama bayani ya rubuta mata magani,da kansa ya tsaya a pharmacy na asibitin ya amshi maganin.

Ita kam komai yayi mamaki yake bata,tamkar ba ya haidar din data sani ba,bata taba kawowa ranta akwai ranar da zatazo ta samu koda kallon mutunci sau daya ba bare akai ga kula da lafiyarta.

Bayan sun baro asibitin saiya tsaya a wani babban kanti yayi musu siyayya bisa radin kansa,ya zaba abubuwan da yake tunanin zata iya buqata sannan ya dawo suka tafi.

*_washegari_*

Tun qarfe shida na safe ta kasa komawa bacci saboda yunwa da takeji,wani lokaci ulcer dinta tana yi mata haka,sai ta sanyata jin yunwa kamar hauka,uwa uba kuma zaman banza data gaji dashi,wanda daga kwanciya sai danne danne a waya,gaba daya zaman ya gama gundirarta,babu wani abu na debe kewa.

Parlour din shuru babu kowa,saita wuce kitchen din kai tsaye,wanda wannan shine shigarta ta biyu tunda tazo gidan,sai a sannan ta qare masa kallo,babu abinda babu a ciki,babun ce kawai babu,hakanan komai atsare yake,da alama kuma tun tafiyarsu hajja ba'ayi girki a ciki ba.

Da iya cikinta kawai tayi niyyar dafa abinda zata ci wanda bazai ja mata lokaci ba,amma saita tuna gida,daga umminta har hajja basa gaba yin girki iya cikinsu,dole sai sunyi da al'ummar annabi,da kuma wanda rabonsa ya tsaga zaici,data duba store da fridge din kuma saita tadda akwai duk wani kayan buqata na amfanin girki,zata iya dafa kowanne abinci,don haka ta diba duk abinda tasan zata buqata ta fara sarrafawa.

Gas din waje hudu ne dashi,saita kunna biyu yadda komai zaifi mata sauri ta dora,ganin bata da sauran abinda zatayi saita fara tattare kitchen din,duk da bawai datti yayi ba,amma akwai qura na rashin shiga kwana biyun,data gama taga har yanzu abunda ta dora baikai mata ta sauke ba,saita miqa falon.

Tas ta gyareshi,ta kuma gyara guraren da baiyi mata ba,dama wani aikin sai diya mace,nan da nan sai gashi ya sake tarwai kamar an qara masa kyau,zuwa sannan ta koma kitchen taga abunda ta dora yayin,saita dora da aikinta daga inda ta tsaya.

A gaggauce ya fito daga dakin yana sake kallon agogon da yake daurawa a hannunsa,cike da mamakin yadda lokaci ya kufce masa haka yanata aikin bacci,sam baisan lokaci yaja haka ba,sai daya soma jiyo qamshin girki a hancinsa,wanda da farko ya zaci a mafarki ne,sai daya farka yaji cikin gidan ne,bai kawo zata shiga kitchen ba,don haka ya barwa ransa daga maqota ne,abinda ya sanyashi gaggawar kuwa daya tuna babu abinda zataci cikin gidan,jiyan dama nasreen ce ta kawo musu shi.

Sanda ya fito falon,dai dai lokacin da zahran ke fitowa dauke da warmers guda biyu,tana ta sauri ta gama ta jera ta koma daki abinta,don batason ya ganta,tayi ne kawai don babu kyau mugunta,musamman ta yunwa.

Ido suka hada dashi,saita dauke qwayar idanunta da sauri gabanta na faduwa hakanan,sannan wani kyau taga ya mata a ido yanzun da yake sanye da wasu kaya,saita koma takawa a hankali tana wassafa yadda zata wuce ta gabanshi,saboda yana tsaye qyam ne,kuma dole ta giftashi,uwa uba ma kuma riga da skert din dake jikinta na roba ce mai rawa,ya zauna yabi kowanne lungu da tudu na jikinta,kanta ne kawai keda dankwali,shi kansa dan kwalin rabi ne,dukka sumarta ta baya da goshinta ana gani.

Sannu a hankali idanuwansa suka bar fuskarta data dan yi fayau saboda ciwon kwama biyun da tayi,sai suka zarce suka sauka a muhallin da tun daxun yake gargadarsu a kanshi,hannunsa ya damqe waje guda yana dauke idanun nasa daga kanta,saidai shi kansa baisan yadda akayi ba yaji qarar faduwar flask din hannunta a gabasa,gab da yatsunsa,saura kadan su sauka a qafarsas,sannan ta daki jikinsa ta zame zata kai qasa.

Cikin matuqar zafin nama ya tarota,gaggawar yin sarving dinta ta hanyar tarota yasa ya dora hannunsa saman qirjinta ba tare daya ankara ba,da sauri ya daga hannun nashi daga wajen,kamar yadda itama ta miqe da sauri ta tsaya da qafafunta,duka sai suka duqa kusan lokaci daya suna qoqarin daga flask din.
Chapter 49 · 0% Book details