Sashe 54
Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Idanu ta dinga rabawa tana cike da fargabar fita,don batasan ta inda zasu hadu ba idan ta fitan,gaba daya ita wani irin tsoronsa takeji,sanda taji an turo qofar dakin sai taji kamar ta zura da gudu,sai kawai ta sulale ta durqushe a wajen.
_____________________________
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!_
_WHO NO LIKE BETA AWUUF THINGS?_
_IDAN KAJI GANGAMI DA LABARI....! INA MASU ZUBIN ADASHEN DA BA RANAR DAUKA NA DATA?_
_TO KU MARMATSO KUJI, KU KUMA SHARE HAWAYEN KU, MUNZO MUKU DA SABBIN TSARE TSARE NA DATA, WADDA KOWA ZAI IYA SAYA DAI DAI KARFIN SA. A FARASHI MAI RAHUSA_
_RANO NET! RANO NET! RANO NET!__
_(Afford data at chikini price)_
_MALLAKI DATA A KUDI KALILAN DA RANO NET_
_TSAYA KUJI, A RANO NET ZAKA IYA ZAMA RESELLER KO WHOLESALER KAI MA, EH ZAKA/KI IYA ZAMA MA SAYAR DA DATA A FARASHIN SARI MUKE BAYARWA, KAI/KI KAFA KASUWANCIN KU KUMA. DA KUDI KALILAN._
_MUNA KUMA SAYARWA AKAN 鈥楧AI DAYA, KOWANE NETWORK MUNA SAYARDA DATA PLAN DINSA AKAN KUDI KALILAN, MASU FARASHIN SARA KUWA MA KU KUDIN BAI KAI HAKA BAMA_
_AIRTEL_
_9MOBILE/ETISALAT_
_MTN_
_GLO_
_DUK MUNA SAYARDA TSARIN DATA DINSU. KAMAR MISALI MTN MUNA SAYARDA 1GB.24MB AKAN FARASHIN NERA 300 KUMA YANA KAIWA WATA DAYA, GWARGWADON YADDA KAKE AMFANI DA DATA, 2GB 600, 3GB 900!!_
_DUKA WADANNAN TSARIN DATA DAMA NA SAURAN LAYIKA MUNA SAYRWA AKAN FARASHI MAI RAHUSA, WANDA KOWA ZAI IYA YIN TSARIN DAI DAI ALJIHUN SA_
_Ranonet.com.ng_
_GA SITE DINMU NAN DAKE YANAR GIZO, KAI TSAYE ZAKI/KA IYA SIYAN NAKA TA NAN. _
_KO A TUNTUBE MU TA NAMBAR TARHON MU: +234聽803聽081聽1300/+234聽808聽540聽5215_
_KYAU, INGANCI, RAHUSA, ADADE ANA YAWO A YANAR GIZO SAI RANO NET._
_RANO NET..!!!!_
23/10/2021, 08:48 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 35
Cikin wata nutsuwa daya samu ta sanadin sakarma kanshi ruwan da yayi yake takowa zuwa cikin dakin,hannunsa dauke da babban mayafinta da kuma abun sallah,sai daya fara shimfida abun sallar sannan ya qarasa gareta
"Kinyi alwala?" Ya tambayeta,tana daga duqen tana hawaye ta gyada masa kai
"Ohk....getup,tashi muyi sallah" ya fada yana miqa mata hannusa,a hankali ta daga kai,maimakon ta bashi hannun yadda ya buqata saita fuske masa,ta miqe tsaye a hankali tana jin yadda cinyoyinta suke so su fara tsami,riqe dantsen hannunta yayi,ya tsaidata sosai,sannan ya ware hijabin hannunsa ya sanya mata,saita isa da kanta saman abun sallar ta tsaya,don ta fuskanci jam'i yakeso suyi,saboda guda biyu ya shimfida.
Jallabiya ya ciro ya sanya,sai qaramar hula wadda ke tsayawa iya kewayen tsakiyar ka,ya feshe jikinsa da turarensa na da'iman,sannan ya shiga gaba ya tayar musu da sallar.
Koda suka idar saita miqe da niyyar tafiya dakinta,cikin sassauqar murya ya bata umarnin ta hau gado ta kwanta ta huta,sai tayi kamar bata jishi ba,miqewa yayi yana tattare abun sallarshi,sannan ya cimmata tana dab da fita a dakin.
Cak ya dagata ya rabata da qasa,ya isa da ita saman gadon ya kwantar da ita yana dan nishi
"Ashe dan banzan nauyi ne dake?,ke kika jawo na kusa miki aika aika,sannan zaki fice ki qunshe kanki a daki,salon ciwo ya rufeki ki ja mani magana wajen waccar tsohuwar,tace naci amanarta ban kula da ita ba" rau rau idanunta sukayi suna tara qwalla,lallai ma ya haidar din nan,ya cita wasa da yawa,amma babu komai,saita rama,saiya saka dan yatsantsa saman labbansa yana duban qwayar idanun nata yace
"Shshshsh....keep silence please"lumshe idanunta kawai ta dinga yi a hankali har ta rufesu,don tasan bata da wani sauran abun fada,tana gama rufe idanun nata yaja mata bargo ya lullubeta,sannan ya miqe a hankali ya fice daga dakin.
Da kansa ya dauki mota ya fita nema musu abinci,haka ya dinga tuqi a titin a kasalance,ya sauke dukka glass din side dinsa iskar waje tana shigo masa,wadda ke cakude da sanyin tasowar hadari,don ko rana babu a garin sosai,sai daya gama shawaginsa sannan ya zaba wani gidan abinci ya musu takeaway,ya kuma biya na dare da zasu kawo mishi har gida,don bai saka ran zata iya girki ba,daga dan tabata kadan duk ta wani langabe,saiya saki murmushi shi kadai yana shafa sumarsa zuwa habarsa sanda abinda ya faru ya dawo masa,idanun hajja kawai yake hangowa a lokacin ace taga abinda yaso aikatawar,tabbas da kashinsa ya bushe,tijara kuwa yasan sai wadda bata tuna ba.
Sanda ya koma ma bata tashi ba,saiya zauna yaci nasa abincin shi kadai,ya zauna yana duba labarai daga ingantattun jaridun dake kawo labarai online,saboda ya sake samun information da haske kan aikin dake gabansu.
Ranar gaba daya wasan buya dashi takeyi,gudunsa take hakanan wani tsoronsa take ji,tunda ta samu ta fice daga dakin nashi bata sake bari sun hadu ba,iyaka idan yayi knocking xai gaya mata ga abinci nan ta fito taci,sai ta dai daici ya gama ci sannan zata fito ta diba ta koma daki.
Ta gefe guda gaba daya hankalinta ya karkata zuwa gida,saidai bata ga alamu ba,bata kuma sake jin ya tada maganar ba,gashi a yanzun bata jin zata iya tunkararsa bare tayi masa zancan.
Kwana na uku da faruwan abun,da wani yammaci yana zaune a falo shi kadai,yana dai xaune ne kawai,amma sam bayajin dadin zaman,wanda shi kansa bazaice ga dalili ba,lokaci lokaci yakan dubi sashen qofar dakinta,tun ranar gaba daya hankalinsa da tunaninsa yayi kanta,baisan me yasa ba,amma baya yin wani qwaqwqwaran awanni bai tunata ba,duk data yanke daga hulda dashi,shi kuma bai tsawwala ba,saboda baison ya fiya shiga rayuwarta da yawa ya zamana akwai takura.
Wayarsa ce ta dauki tsuwwa,saiya miqe ya cirota daga chargy yana dubawa,hajja ce dai,murmushi ya saka,yasan darun nata ta kira tayi masa,don haka tun kafin yakai wajen zamanshi ya daga wayar,ya soma gaidata ta dakatar dashi
"Ba gaisawa na kiraka muyi ba,nace maka ka dawomin da yarinya amma kayi kunnen uwar shegu dani ko?,wai shinma ni din sa'arka ce koko yaya aka soma?"murmushi yayi wanda ya tabbatar ta jiyoshi
"Haba tsohuwa....na gaya miki fa matata ce....ya za'ayi ace ni za'a baiwa aro,ai saidai ni na baku....idanma naga dama kenan"
"Qaniyarka,nace qaniyarka.....auren bani na hadashi ba kuna tsalle tsallen banza?...." Saiya datsi numfashinta
"To kuma yanzu tsalle tsallen qauna muke.....basai a barmu ba muyi rawar gaban hantsi ba,koda mun dawo ma dan wankan da nake samu tana min Allah idanu xaki saka mana ki hana ruwa gudu...." Dogon salatin data dauko shiya tsaida zancan da yake,dariya irin wadda ya jima baiyi ba ta taso masa,ya danneta sosai
"Hajja....dama kinyi shuru,kin kuma qyaleni,don kin ganta a kusa dani abinci ma zata bani....ki gaya mata ta rage bani abinci da yawa kada mu dawo ki kasa ganeni"
"Ke zahra'u....kinci qaniyarki....qaniyarki nace" katse wayar yayi yayi dariyarsa son ransa,sai yaji ransa fes,ya samu waje ya zauna yana murmushin tsiyar da ya yiwa hajja,ya tabbatar bashi yaci,ya kuma janyowa zahra jagwal.
Kamar ance ya daga kanshi saiya hangeta bakin qofar dakinta,da alama taji duk yadda sukayi da hajja,kanta ta dauke yayin dashi kuma ya sassauta murmushin fuskarsa,tun daxu take dakon jin fitarsa ta fito taci abincin rana daya ce mata taci amma taji shuru,ganin babu alamun zai tashi,ga yunwa zata hallakata shine kawai tayi shahada ta fito.
Baice mata uffan ba harta diba abincin zata wuce yace
"Zo nan" dan hade rai tayi kafin ta juyo ta maida fuskarta dai dai,saita qaraso,ya dubeta
"Zauna nan kici....daga yau duk sanda kika sake rufe kanki a daki....zan balle qofar na shiga,kuma abinda xai biyo baya bazai miki dadi ba,don banga abinda xaisa ki ringa kulle kanki ba anan" narke fuska tayi,yunwa takeji sosai,kuma bata jin xata iya cin abinci a gabansa,kamar ya karanceta sama taka taji yace
"Eheeennn....idan xaki ci abinci kici,kaman bake muke bawa abincin ba a baki muna share miki majina a hanci" da sauri ta daga kai ta dubeshi,sai suka hada idanu,ta sake kautarwa da sauri saboda yadda ta kafeta da idanunsa dake mata kaifi da yawa,kai ya gyada mata alamun tabbatarwa
"Yesss.....ba zaki iya tunawa ba,saboda a sannan kinyi qanqanta da yawa.....kukan kitso...kukan wanka duk kin iya,da kika girma kuma sai kika zama mai tsiwa da taurin kai....right?" Ya qarashe da tambayarta,sosai maganar ta mata nauyi ta kuma bata kunya,zata iya tuna wani abun,amma wani abun ba zata iya tunawa ba,hakanan taji tana son sake jin wani abu daga bakinsa,mutum ce dakeson labarin quruciyarta,tana son a dinga gaya mata abubuwan da tayi zamanin quruciya wanda ita batasan ta yisu ba,ya karanci hakan akan fuskarta,amma bai sake cewa komai ba,saidai ta sanya cokali ta soma diban abincin a hankali tana taunawa,yayin daya lafe jikin kujera kamar mai kallo a tv,saidai ita yake satar kallo time to time.
Da magariba yayi waya aka sama masa ticket na jirgin da zai tashi daga abuja zuwa kano qarfe biyu na rana,bai shaidawa zahran ba ita kanta sai washegari daya dawo daga sallar asuba,haka nan wannan karon sai taji bata wani daukin tafiyar sosai,haka ta sake abinda yake da buqatar a shirya din,zuwa sanda ya gaya mata xasu fita ta kammala komai,ta yafa mayafinta,ta janyo akwatinta tayo falon.
A tsaye ta sameshi tsakiyar falon yana amsa waya,ya baiwa qofar da zata fito din baya,tun kafin ta qaraso ta gama qare masa kallo,sanye yake da wani trouser da shirt,sai high top takalminsa daya dace da kayan jikinsa,tun bata ga fuskarsa ba amma ta tabbatar da cewa shigar ta amsheshi,ta qara masa kwarjini.
Ta gefansa ta raba zata wuceshi,sai taji an kama hannunta dake riqe da majanyin akwatin matafiyar da take ja,waiwayowa tayi sai suka hada idanu,ya mata alama data saki,don haka ta zame hannunta daga cikin nashi a hankali,ya taka ya biyo bayanta yana ci gaba da yin wayarsa.
Dukkansu a baya suka xauna,driver ne ya jasu,wanda idan ya kaisu airport zai dawo da motar ne gida.
Ko a cikin jirgi ma babu magana tsakaninsu,saidai lokaci zuwa lokaci kowa ya kama dan uwanshi yana satar kallonsa,daga bisani ne haidar ya tanka
"Idan na sake kamaki kina satar kallona saina tsole idanun nan naki" gefe tayi da kanta,ciki ciki tace
"Da wanne idon mutum yasan ina kallonshi" baice komai ba amma taji kamar sautin fitar murmushinsa.