← Book details Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 55 OF 70

Sashe 55

Alkibla Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna sauka a aminu kano airport driver ya daukesu sai gida,ji take kamar tayi tsuntsuwa ta ganta a gida,tafiyar kusan minti arba'in ita ta kawosu gida,wanda tun daga harabar gidan tasan tabbas taro ake,saboda jama'a da kuma rumfunan da aka kafa,indai lissafinta yayi dai dai yaune sunan yasira kenan,harga Alla ta fidda rai data ji bai sake tada zancan ba,shi yasa ta daina lissafin ma.

Zumudi fal ranta ta saka hannu xata bude murfin motar,sai taji an dafe hannun nata,ta waiwayo da sauri idanunshi na akanta,hakanan tana iya jiyo hucin numfashinsa sosai saman fuskarta saboda yadda yake dab da ita,da wata irin kwantacciyar murya taji yace
"Ki nutsu da kyau,kada ki manta ke din wacece,banason yawo jiki a bude da sunan kina cikin gida....ki kiyayemin mutuncin igiyata" gaba daya ita zancan nauyi ma yayi mata,saita maida kanta daya side din,daga nesa tana hango su salma suna kai kawo,da alama hidima ta dauki zafi
"Soja baya son kawo qorafi ko kawo uzuri,just be obedient to my commands" cikin ranta take mitar ance masa a bariki ake dazai soma lissafa mata wasu qa'idoji,bata gama wannan ba taji ya zame wayarta daga hannunta,yayi wasu danne danne ciki sannan ya miqa mata
"This is my number,just call me idan kina da wata matsala ko buqata,bance ki tambaya kowa komai ba,ummi ko hajja,nayi cancel duka,zaki iya tafiya" da sauri ta buda murfin motar ta fito,wanda fitowar tata yaja idanun mutane da yawa,donma aliyyun zamanshi yayi cikin mota,ya kuma nada umarnin a sake fita dashi daga gidan,batasan inda xaije badai,tadai san koda can baison hayaniya kwata kwata,indai ana wani taro a gidan bai zama,sanda bai kuma wani zama saurayi ba wuni yake cikin dakinsu ya kebe kanshi shi kadai,mama tayita faman fadan me yasa baya son shiga dangi ko ya fito su gaisa,tun tana mita da qorafi harta gaji ta qyale,tunda ta fuskanci halinsa ne hakan,

Nan da nan labarin dawowar tata ya zagaye gidan,aka fara cecekuce da zancan dawowarta,ta fara gaisawa da 'yan uwa data samu harabar gidan,suna amsawa gami da tayata murnar qarin girman da aliyyun ya samu,ta sake fuska sosai tana amsa musu cikin walwala da nuna jin dadi,da yawa suka dinga binta da kallo wanda batasan na meye ba,da haka harta isa sassan abba babba,inda canne yafi cikowar yan suna da yawa,tunda anan mahaifiyar yasiran take wato mommy.

Ihun murna 'yan uwan nata suka saka sanda sukayi arba,kowa yayo kanta,suka cika kunnuwanta da magana,kowa da abinda zaice,salma ce daga can tace
"Allah matar ya haidar ba haka muka taho muka barki ba,anya ya haidar bai cika aiki ba kuwa?" Ta qarashe fada qasa qasa,wani wawan dundu zahra takai mata,akayi sa'a kuwa ta sameta,fa gantsare saboda zafi,sauran suka sheqe da dariya,dai dai sanda mommy ta shigo
"Waiku kam bakusan kun girma ba don Allah,yanzu kalli yadda sahal yake kallonku,kin dirke masa uwa.....daga dawowarki kin biye musu,tashi ki qarasa gaisawa da jama'a ki qyale wadan nan shirmammun,kuna nan a waje ana nemanku kunata baqi"tana kaiwa nan ta fice ta barsu.

Tare suka fito da ita,ta soma lalubar mama don su gaisa,a kitchen na tsintota sunata rabon abinci da taimakon masu aikin gidan,wai yau sai ta tsinci kanta tana kunyar maman,tana kunyar hada idanu da ita,tana shirin tsugunnawa har qasa ta gaidata tace
"A'ah,tashi inna wuro kada ki bata kayanki,bakiga yadda kitchen din yake a kacame ba" saita lalubi kujera ta zauna akai saboda ji take kamar zata fadi ta gaida maman tayi mata barka
"Ki shiga wajen hajja,can ne naga da sauqin mutane" da to ta amsa mata,suka fito tare da hafsa.

Hafsan ce ta dubeta sanda suka fito ta qyalqyale da dariya
"Anya zahraty wannan kunyar nidai ban taba gani kina yiwa mama irinta ba kamar yanzu,lallai yayana ya cika aiki....to ku shirya wallahi kuda hajja,tana nan satin nan gaba daya kullum saita muku dan biki" harara ta watsawa hafsan,bata iya bata amsa ba suka qarasa sassan umminta.

Kusan a tsaitsaye suka gaisa saboda jama'a itama dake cike a sassan nata,sai kawai ta wuce sashen mutuniyar tata hajja.

A dakinta ta sameta ita kadai tana tsaye inna gaje na wanke mata bandaki,da alama wani ya shigar mata ne,haka take,duk sanda wani ya shigar mata bandaki indai baqo ne to sai an wanke mata,har mamakin tsafta irin na tsohuwar zahra keyi,wani lokaci kuma ta tsokaneta
"Waike da kika kusa gangarawa tsaftar nan duk ta meye?" Wanda idan wani ne ya gayawa hajjan haka sai inda qarfin zahran yake,takance
"Kaga tafiya lahira a kanka,hajjanmu ba yanzu ba".

Wani kallo hajjan tabi zahran dashi kafin ta yamutsa fuska sanda take gaidata
"Munafukai....sai yau kuka ga damar tahowa?,aida kun sani kun dawwama a can" ta fada da biyu,sabida ta bigi cikin zahran taji me zata ce,hade rai zahra tayi tadan ja baya
"Zaki fara daga dawowata,ni inacan kamar nayi me saboda kewarki,amma irin marabar da zakimin kenan?"
"Na miki da arziqi ma 'yar nan,ina daya ja'irin?" Baki ta turo ta haye gadon hajjan,wanda tayi kewarsa sosai
"Ki kirashi ki tambayeshi mana" ta fada tana kwanciyarta
"Toooo...da saura kenan" hajjan ta fada a ranta,don tayi tsammanin zata kareshi ne
"Muje zuwa mahaukaci yahau kura" ta kuma fada a ranta
"Duk na isheku riga da wando" ta fada tana shigewa bandaki.

Wunin ranar cikin walwala tayi abinta gaba daya cikin dangi,har zuwa dare sanda aka qare sunan,baqi suka tattafi saura 'yan gidan da yaran gidan aurarru wadanda sukayi aure,suma a cikinsu wasu sun tafi,tawagar su zahra kuwa suna tattare a sassan hajjan sunata kwasar hira,kamar ba za'a rabu ba,don yasiran a nan sassan hajjan take zaune tunda tazo haihuwa.

Tana idar da sallar isha'i zahran ta koma wajen ummin nata,suka sake gaisawa sosai sannan suka taba hira,wanda ta lura kusan fiye da rabin hirar tata kan aurenta da aliyyu ne a fakaice,tana mata jirwaye mai kamar wanka a kansa,ta rasa wanne irin qauna ce a tsakaninsu
"Nasan zakiyi mamaki me yasa na damu da zancan aliyyu a kanki ko inna wuro?....nafi kowa sanin aliyyu mijine na kerewa sa'a,irin mijin da ake cewa mijin marainiya,mijin dana jima ina miki addu'ar samu,kici gaba da gyara mu'amalarku inna wuro,zaki fuskanci abinda nake gaya miki,mazan aure irin haidar a wannan zamanin wahala sukeyi,cikin dari guda daya ne tak,Allah ne ya amshi addu'ar dana jima ina muku ya kawo sanadi da kika zama matarsa" wannan shine magana kusan ta qarshe da sukayi da maman nata,wanda da ita ta dawo zuwa sassan hajja,wanda zuwa yanzu an sake yoyewa,inna gaje ta gyara falon fes,sai fidda qamshi yakeyi.

Dakinta ta shige,saita tadda yasira ta baje abinta ita da jaririnta,sai suwaiba da itama zata kwana,sai wata 'yar uwarsu badi'a,itama ba aure ne da ita ba.

Tunda can dama ba wani shiri suke sosai da suwaiba ba,don haka da badi'a suka gaisa kawai,ta diba kayan wankanta ta shige bandakin tayi wanka,sannan ta fito ta dauki kayan da zata saka ta wuce dakin hajja donta shirya,saboda ta fuskanci kamar suwaiba ta sanyawa duk wani motsinta ido,batason ta fusata harta buda baki ta gaya mata magana,shi yasa tabar musu dakin da niyyar kwana dakin hajja.

Saman abun sallah ta tadda hajjan,da alama idarwarta kenan,ta dubi xahran,saidai batace komai ba,har zuwa sanda ta gama addu'o'inta,ita kuma zahran ta gama shirinta,tayi tsalle ta haye gadon hajjan,sai a sannan ta magantu
"Ke zahra'u....tashi kije ki amshi abinci wajen gaje ki kaiwa yayanku"
"Habba hajja,don Allah ki qyaleni mana na huta,ni wallahi bacci nakeji" ta fada tana tura baki,dakewa hajjan tayi
"Tashi ki fita ki bani waje....billahillazi idan na fito na ganki a sassan nan....ke bama sassana ba ko ina nema sai ranki ya baci,ki amshi abinci ki kai masa ya kirani yace a kawo masa,kuma babu uban da zaije kaiwa mijinki abinci...." Tana tura baki tana komai haka ta sauko ta daga saman gadon,har takai bakin qofa ta sake kiranta
"Ba abinci kawai nace ki kai masa ba,karki dawomin sai gobe,idan kinqi ji kuma ba kyaqi gani ba" ko waiwayawa ta dubi hajjan batayi ba tsabar takaici ta qara gaba,itakam gaskiya hajja tana son wuce mata gona da iri,idan batayi wasa ba ta tattara ta koma makaranta zasu jima kafin su ganta,kowa ma a gidan ta shafeshi.
23/10/2021, 08:48 - 馃憤馃徎馃憤馃徎: 36
*KIJI TSORON ALLAH鈽濔煆锯槤馃従鈽濔煆綤ADA KI TABA KAYAN DABA NAKI BANE,BA KUMA MALLAKINKI BANE*

Tana tafe a hanya riqe da kwandon kayan abincin kamar ta sakesu ta sanya kuka saboda takaici,ji take gaba daya hajja ta gama takura rayuwarta tako ina,tana wannan qunci har takai qofar dakin nashi.

Turawa tayi hadi dayin sallama qasa qasa,alamun ranta na a bace ne,a lokacin yana zaune saman kujera,ya miqe qafafunsa lan center table dan qarami dake gabansa,system ce saman cinyarsa yana typing da mugun sauri,da alama wani muhimmin magana yakeyi,dakin a dan hargitse yake da kaya.

Sau daya ya daga kai ya kalleta ya amsa sallamar ya maida kansa ga system dinsa,saita qaraso a hankali ta aje kwandon gefanshi,tsaye tayi ta rasa meye abunda zatayi,tana tunanin ta koma idan yaso hajjan tayi kwadonta ta cinye,idan kuma ta zauna din kamar ta zubda kanta ne,zaiga ita ta kawo kanta ma kenan,kamar tadda yayi mata sharri a abuja.

Sake daga kai yayi ya dubeta,idanunta nacan wani sashen daban,don ta jima bata iya hada idanu dashi,tun lokacin da wancan abun ya faru,duk yadda yakai ga qwaqwqwafi da qwaqwar su hada idanun bata yarda
"Have a sit please.....bana son tsaiwa" ta jishin,saita samu waje tana zama din,cikin ranta tana mitar har a gayawa soja tsaiwa zaice wani baison tsaiwa,takaicinsa ya sake cikata,ta rasa me zata masa ta fanshe haushin da hajjan ke cusa mata a kanshi,don haka ta tsiri zuba mishi abinci,kowanne plate saita cikashi ta tura gabanshi,shi sam baisan ma me ake ba,harta gama zubawar,saita miqe ta nufi dan qaramin fridge dinsa dake dakin ta bude.

Jere yake da hadaddun zobo,wanda da alama jin zuwansa yasa umminta tayi masa,tunda dama itake masa,saboda din mutum ne da idan ba dole ba bai fiya son lemon kwali roba kona kwalba ba,yafi gabe gagajiya,zobo ginger ko kunun aya,su yafi sha indai yana gida.
Chapter 55 · 0% Book details