← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 9 OF 42

Sashe 9

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*9*
Yanzu halin da ake ciki kuwa hatta yarana da na haifa a cikina na musu umurnin duk mai sonta ya nemo aurenta a rabata da qangin bautan da take ciki amma usman da usaini duk sun je gwada sa'arsu amma qiri-qiri matar nan ta cewa ibrahim ba za a aurar da yarinyar yanzu ba har sai yarinyarta tayi aure wai saboda ita indon itace gaba da ita, da na ji haka da kaina na samu ibrahim
in amma abin al'jabi bu
ar bakinsa sai cewa yayi sai dai in nemi haule in ji abinda zata ce, don shi duk abin da tace haka za a yi, Abdullahi a wancan ranar sai da nayi kuka da idona na tausayin ibrahim da marayun yaranshi guda biyun nan, domin duk rashin fahimtar mutun dole zai gano ibrahim ba ya cikin hayyacinsa, kuma abin takaicin ita yarinyartar ko kare babu wanda yake zuwa gurinta saboda mugun halin uwarta, ka ga kenan yarinyar bata da ranar barin wannan uqubar
Dakatawar da malam yayi hakan yasa ya fahimci labarin ya zo qarshe don haka ya motsa qafarsa tare da sauke numfashi ya sunkuyar da kai qasa, ya
au lokaci a haka sannan ya
ago da kansa yana kallon malam yace
"malam ya maganar karatu kuma?, tana zuwa makaranta kuwa?"
"ina ga rabon yarinyar nan da makaranta tun da mahaifiyarta ta rasu aka yanke mata saidai lokacin da su jamila sa'anninta yaran gurina suka zo zana jarabawar kammala primary na ha
a baki da headmastern su ya zo ya bu
e musu ido akan hukumace ta turoshi ya fa
a musu dole su bar yarinyar ta je tayi jarabawar idan ba haka ba hukuma za ta zo ta kamasu, to akan ba yadda haule za ta yi ta hakura yarinyar ta zana jarabawar"
Nan ma Abdullahin shiru ya sake yi na tsawon lokaci sannan ya ce
"na gode malam da ka bani lokacinka, ita kuma maryam ubangiji ya kawo mata kyakkyawar mafita"
Ameen ameen malam yace sannan ya juya ya nuna wa Abdullahi koko da kosai da aka kawo masa da
umamen tuwo yace
"ga kayan karin kumallo nan, watakil ma yayi sanyi, mun tsaya surutu"
Ya qarasa maganar yana murmushi, shi ko Abdullahi fuskar nan ba raha balle wargi, ciki ciki yace
"Allah ya biyaka malam, ina godiya sosai"
Miqewa malam yayi ya fita daga
akin yana cewa
"ameen Abdullahi'
Ba tare da ya ji qyanqyamin cin abincin ba ya janyo ya fara kaiwa, ka
an yaci tuwon sannan ya sunkuya kan kunu da kosai
*************
A jikin masallacin suke tsaye bayan sun idar da sallar azahar, cikin neman alfarma yace
"malam ina roqon alfarmarka guda
aya, don Allah ka min alfarmar zama da kai na sati
aya mana, garin ya min da
i, bana son barinshi a yau, duk aikin da kake so zan maka shi matuqar zaka amince min"
"to shikenan malam Abdullahi, ubangiji yasa hakan alherine"
"ameen ameen" yace da sauri yana murmushi shima malam murmushun yayi yace
"Abdullahi ina jinka kamar
an uwana"
Murmushin ya sake fa
awa yace
"na gode malam"
Ladan ne ya fara gaba sannan Abdullahi ya bi bayanshi suka kama hanyar gida suna ta hira,
Hira suke yi sosai kamar wa
an da suka da
e da sanin juna, Abdullahine da
an malam tanimu mai suna shafi'u, shi ma a ranar ya dawo daga qauyen babarshi can tafare, duk da
an gayune amma halin ubanshine da shi bai rainawa mutane, hakan yasa bai raina yanayin bakon nasu ba, suke ta hirar duniya abinsu, saidai shi kanshi baqon ya
kan lura da tsananta kallonshi da shafi'u yake yi, saidai da ya ga za su ha
a ido da bakon nasu sai yayi saurin
auke kai, duk da ya sha jinin jikinsa amma bai bari shafi'un ya fahimci ya san yana masa wannan kallon ba
A hankali take tafiya
auke da tiren
anyen kayan miya da bushasshe, kan ta a k'asa yake ta zo wuce gaban su Abdullahi
Bin ta da ido yayi sannan ya dawo da kallonsa kan shafi'u wanda shi kuma shi yake kallon, magana yayi wa shafiun qasa qasa, sai gani nayi shafiun ya mai da kallonsa kan mairo sannan ya
aga murya ya kwa
a mata kira
A hankali ta juyo baya bayan ta amsa kiran, ita dai sai a lokacin ta lura da wa
anda suke gurin, gaban shafiu ta zo ta
an sunkuya tace
"ina wuni yaya"
"lafiya mairo, ya gidan"?
"lafiya qalau yaya, ka dawo qalau"?
"lafiya lau mairo, yaya idris"?
"lafiyanshi qalau"
Tace sannan ta mayar da hankalinta kan Abdullahi tace masa
"ina wuni"?
e rai yayi ya kawar da kansa gefe ya amsa ciki ciki kamar baya so, ba ta ji da
in yadda ya amsa mata gaisuwan ba don haka ta juya tana kallon shafiu jiki a mace cike da rauni tace
"yaya zan tafi"
"toh mairo, amma kin ci abinci"?
Raurau tayi da idanunta kamar za ta yi kuka amma ta kasa cewa komai sai ma sunkuyar da kai da tayi
Kallon Abdullahin yayi ya na nuna masa ita da ido, cikin cin magani yace
"ka ce mata ta mayar da tallen har sai ta ci abinci"
Dariya shafiu yayi yana kallon Abdullahi yace
"kar ka fara, ka san wacece haule kuwa?, yanzu zata surfa maka rashin mutunci"
Wani kallo ya masa wanda ya sanya shakku cikin zuciyarsa sannan ya juyo da kallonsa kan mairo ya k'ura mata ido, take ta ji wani tsoro ya shigeta, cikin dakiya ta ji yace
"ki jirani a nan kin ji ko, idan na fito daga gida ba kya nan....."
Sai yayi shiru yana wani girgiza kai sannan ya tashi ya wuce cikin gida, neman izini yasa aka masa gurin malam sannan ya shiga ya samu malam
in yana ta fifita da mafifici kasancewar yanayin akwai zafi, zama yayi yana fuskantar malam sannan ya fara magana
"malam don Allah ina so ka taimakeni akan yarinyar nan, duk abin da zaka ji nayi akan matar can kar ka ce komai, na yi maka alqawarin ba zan aikata abin da za ka yi danasanin kar
ar baquntata ba, ka zuba min ido kawai har sai na dakatar da zaluncin da ake aikatawa ga wa
annan marayun, yin hakan wani nauyine a kaina"
Gyara zama malam yayi kansa a k'asa yana nazarin maganganun bak'on nasa sannan ya
ago kai yace
"ban fahimci kalmar nauyine a kanka ba, akan me hakan ya zama nauyi a kanka, wa ya
aura maka?"
Murmushi yayi ya lanqwashe k'afafunsa yace
"Allah ne ya
aura min"
"kamar yaya Allah ne ya
aura maka"?
"hadisin annabi yace, duk wanda ya ga abin qi daga cikin ku to ya kawar da hanunsa, ko da harshensa, ko da zuciyarsa, ni kuwa malam ina da ikon aikata duka ukun, kana ganin idan na bari Allah ba zai tambayeni ba"?
Cikin jimamin lamarin malam yace
"kana ganin babu abin da zai faru, ina jiye maka tsoron abin da zai biyo baya, tun da ba ka da alaqa da su"
Murmushin girmamawa yayi wa malam yace
"kar ka damu da wannan malam, ina daidai da duk abin da zai faru, rauni na a zahirinane amma zuciyata cikakkiyar jarumtace cikinta"
Kalamansa sun sanya malam darawa cikin zolaya yace
"ka ce a zuciyarka kai jarumin mazane, qi gudu sa maza gudu"
Take yanayin fuskarsa ta canza, zuwa wani irin yanayi mai wuyan fassara, ba komai ya janyo hakan ba face kalmomin malam da suka tuno masa baya, cikin wannan yanayin ya tashi yayi sallama wa malam ya fice, shi ko malam bin shi yayi da kallo cikin ranshi yana sake jin wannan shakkun akan bak'on nashi yana sake kama mishi zuciya, wani sirri yayi da zuciyarshi ba tare da ya furta ba ya jinjina kai tare da amince wa abin da ya tsara
Gurin da ya barsu ita da shafiu nan ya taraddasu saidai yanzu kuka ya samu take yi shafiun yana ta bata hakuri
A kansu ya tsaya kusan minti uku bai ce komai ba sannan cikin tsumewa yace ta so mu je, shi ko shafiu da tun tsayuwarshi a gurin yake ta qare masa kallo a sace, so yake lallai sai ya tuna gurin da ya so ya san fuskar amma ya kasa
Miqewa tayi jiki a mace ta
au tiren kayan miye, kallon shafiu yayi yace
an uwa minti biyu, ina zuwa, ba damuwa yace sannan ya fara gaba tana binshi a baya
Sallama yayi a k'ofar gidan kamar sau uku sannan ta fito tana yatsina kasancewar baban mairo baya gidan, cikin raini ta kalleshi sama da qasa tace
"malam lafiya"?
"ki ce wa haule ana magana da ita"
yace cikin dakewa
Wani kallon rashin arziqin ta sake masa sannan tace
"kai wani irin haule ba ko ladabi, ina laifin baba haulen"
Tsawa ya buga mata wanda yayi qoqarin lalata mata netwrk sannan yace
"idan uwarkice, ni uwata ce"?
Tun ba a je kiran haule ba wannan tsawar ya gayyatota soron tana cewa
"lafiya indo?, me yake faru...."
bata qarasa ba maganar ta maqale saboda ido biyu da sukayi da dodonta, irin ta nuna taurin kan nan sai ta ha
e rai tace
"kai malam lafiya?, ce maka aka yi muna raba sadaka"?
bai damu da abin da tace ba balle ya bata amsa ya juya bayanshi yace wa mairo ta zo ta shiga gida, cike da tsoro biyu ta fara tafiya a hankali har ta shiga soron gidan idanunsa na kanta, kallon haule yayi cikin tsana yace
"idan kina son yarinyar nan ta je miki talle to dole ki bata abinci kafin ta fita tallen, idan kuma kina buqatar neman sabon jari to ki sake
aura mata talle da yunwa, idan kina neman zaman lafiya kuma kar ganganci yasa ki
ora hanunki akan yarinyar nan, shawarace"
Yana fa
in haka ya juya zai tafi
"toh ban ji ka ce a matsayina na wane ba tsohona"
Haulece ta ke fa
in hakan bayan ta riqe qugu
Juyowa yayi yana murmushinsa na shu'umanci yace
"a matsayina na
an iskan gari, ina fata kin gane"?
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/2, 6:41 PM] Dr. Gital
Chapter 9 · 0% Book details