← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 29 OF 42

Sashe 29

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*29*
Wayar ba ta da
e tana ka
awa ba hajiyar fawwaz ta
"assalamu alaikum"
Cewar hajiya cikin salihar muryarta
A can
angaren alhaji nasir ya amsa
"wa alaikissalam hajiya, mun wuni lafiya"?
"lafiya lau alhaji, yaya iyalan"?
"iyalai alhamdulillahi"
"toh mashaa Allah, mashaa Allah"
Jim yayi na two minutes kafin ya numfasa yace
"hajiya nace ya maganarmu ne, ina ta kwana?"
Ita ma a can sai da ta
an yi gyaran murya tace
"eh maganarmu tana nan, babu abin da ya canza ta alhaji, ni na
auka ma kun yi waya da fawwaz
"alhamdulillah, na ji da
in jin haka daga gareki, kin san na ce miki nayi ta kiranshi ban sameshi ba, to tun daga lokacin ban sake kiranshi ba, domin na san ke ma idan ya dawo zaki masa maganar"
"ok toh yanzu ka sa mana ranar da zamu zo da shi gidan sai mu tsai da magana kafin iyayensa maza su shigo ciki"
Cikin washe baki alhaji nasir yace
"ni duk lokacin da zaki zo ki sanar da ni kawai hajjaju, zan yi zaman jiranku"
"toh shike nan, bari ya zo sai in ji ranar da yake da rarar lokaci, duk yadda muka yi zan nemeka in sanar maka"
"yawwa hajjaju, ina godiya da wannan karamci sosai sosai, sai na jiki"
"um um ba komai alhaji, an zama
aya ai"
"toh na gode, a gaishe min da amaryata me jan kunne"
Dariya hajiyar tayi tace
"lallai fa kana fama da amarya, gata nan sai surutu"
Dariyar shima yayi yace
"ai haka ake so, lafiyace"
"lallai fa, toh sai anjima"
"mu jima da yawa hajiya"
Kashe wayoyin sukayi duka a tare yayin da hajiya take shan tambayoyin amrat, wai hajiya ta fa
a mata da wa tayi waya, wanene me surutu??
Toh kina yi sai a qi fa
a amrat?
, surutu kamar beauty na
Kallon zeey yayi bayan ya ajiye wayar yana murmushi
"uwata duk kin bi kin
aga min hankali akan shirmen banza, toh dai kin ji a gabanki muka yi waya da hajiyarsa, ta ce za su zo da shi ayi maganar auren, yanzu shikenan ko?, sai a share hawaye a tashi a ban guri"
Sai a lokacin kunyar abin da tayi ya rufeta, sunkuyar da kai tayi tana murmushi kuma ta kasa tashi, abokin karawarta hisham ne ya juyo ya kallo gurin da suke ya sama mata hanyar fecewa
"ban da rashin kunya ma irinta wannan yarinyar akan saurayi ki zo ki hana mu zaman lafiya, kiyi ta kuka a gaban iyayenki, hutu nake buqata tun da na dawo daga school amma kin hanani hutawa da sautin kukanki maras da
in sauraro"
Ai kuwa nan ta
ago fuskarta da sauri tayi kansa tana nuna shi
"kai wallahi hisham ka kiyayeni, ni ba sa'arka bace, banza kawai wawa"
Dariyar shaqiyanci ya mata yana cewa
"hey malama, a tashi min a kai domin na san ba dakuwa zan yi ba"
Dama neman hanyar barin gurin take yi, saboda haka sai tayi qwafa tare da jan wani shai
anin tsaki ta wuce
akinta, shiko hisham sai wuuu taji kunya yake cewa
"kai kai kai, ka shiga hankalinka, ka san dai yayarka ce ko?, ka ji min yaro da rashin kunya, bar ganin ka fara ajiye qasumba har yanzu dai ba a canza wa tuwo suna"
Cewar alhaji kenan yana zare idanu wa hisham
Tashi hajiya tayi tana tafiya tana cewa
"kai kake biyewa wa
annan yaran, anjima ka
an zaka ga suna qusqus, wa ya sani ma ko gulmarmu sukeyi"
Daga alhajin har hisham binta da kallo sukayi suna dariyar maganarta
*********
"shegiya safna, kin so ki kasheni lokacina bai yi ba, da yanzu fa na dawo marigayiya"?
"me kuma nayi zeey baby"?
"ai zan shigo gidanku gobe, dole sai kin biya tsoratarwar da kika min, ai ke banzace wallahi"
Katseta safna tayi da cewa
"qawar banza ba, shirme kawai, ki fito ki fa
i matsalarki kin tsaya nuna min ke 'yar fari ce"
"toh hasidin iza hasada, keh na fahimci baqin cikin kasancewata 'yar farin nan kike yi, kin san dai
an fari shi ne
an so ko?, ba irinku ba, ku ba auta ba kuma ba 'yan fari ba"
"in miki baqin cikin kalar haukan?, da
an fari da auta wannene me kan gado da wayo"?
Dariya suka kwashe da shi duka sannan zee tace
"to 'yar rainin hankali na ji, yanzu dai abin da nake so ki sani shine har yanzu komata tana riqe da wannan babban kifin"
"wanne kifi kenan"?
"gee fawwaz mana yarinya, keh dai ki shirya shan shagalin da ba ki ta
a sha ba, wallahi har yanzu gee fawwaz na zee babyne ita ka
inta"
Dariya safna tayi sosai sannan tace
"toh ban qi miki cewar zaki auri gee fawwaz ba, amma wlh sai dai ki je a ta biyu, domin ina da tabbacin yayi aure jiya, kin san yadda muke da raudat kuwa?, toh tun yarintarmu tare mukayi har yanzu bamu rabu ba, jiya na kirata a waya saboda ina son kai mata wasu kayan da muke so mu yi anko sai take ce min ta je biki gidansu antynta, auren gee fawwaz suke yi"
"keh bar min mugun fata zama da kishiya ba dai a gidan fawwaz ba, sam sam, sai anjima"
Tana gama fa
in hakan ta kashe wayar tayi jifa da ita tare da fa
uwa a kan gadon tana jan tsaki
*********
Saboda yanayin jikin yasa tayi nauyin barci bata farka da wuri ba har gee fawwaz yayi sallah yayi karatun kur'ani tana na
e cikin bargo abinta, sai sheqa barcinta take yi cikin ni'imar da take jinta ciki, musamman sassanyar qamshin da yake ratsata ta ko ina, ga jikinta da yaji lafiyayyen sabulun wanka sau uku a rayuwarta, hakan ya taimaka sosai wajen nitsawarta duniyar barci
Tsaye yake a kanta yana nazarin yadda take shaqar numfashinta, tun bai ta
a jikinta ba ya gano sauqi sosai da ta samu ta yadda numfashintan yake fita, hankalinsa ya mayar kan agogo yaga idan bai tasheta ba za ta iya rasa sallar asuba domin rana tana gab da fara fitowa
Sunanta ya kira tare da bubbuga fulon da ta
ora kanta a kai, a karon farko ba ta ji ba sai da ya sake bubbugawa tare da kiran sunanta
e idanunta tayi a hankali bayan tayi miqa ta saukesu a kansa, kunya ko qauyanci oho sai kawai ta
auke idanunta tare da jan bargo ya rufe mata fuska
Girgiza kai yayi yana murmushi yace
"ki tashi kiyi sallah, ko za a sake wani daren ne maryam"?
Toh tace a ranta tana cewa
"shi kuma wannan ba a ganin zuwanshi saidai mutum ya ganshi a kansa"
Ganin bata tashi ba yasa shi ficewa daga
akin yana cewa
"ki tabbatar kin tashi kin yi sallah kafin in dawo"
Tana gani ya fice ta sauko daman ta qi tashine saboda yanayin kayan jikinta
Tana zaune kan abin sallah ya shigo, kan kujera ya je ya zauna ya mai da hankalinsa a kanta, kanta ta
ago ta kalleshi cikin jin nauyi tace
"ina kwana"?
"lafiya lau maryam, kin tashi lafiya"?
"lafiya qalau"
"da kyau, toh ya baqunta"?
"lafiya"
Shiru yayi na wasu mintoti sannan yace
"kin san me za kiyi yanzu"?
Kai ta ka
a masa tana kallonsa
"ki tashi ki yi wanka, ki canza kaya kafin lokacin break"
Toh tace daga nan ta ja bakinta tayi shiru tana jan yatsunta
"idan kin shirya feenat tana so ta gaisheki, zaki iya fita falon ku gaisa amma ita bana so ta shigo nan"
Nan ma dai to
in tace
Wucewa yayi saitin labulen ya yaye, bin bayansa tayi da kallo tana tunanin me zai yi a gurin, ba ta qarqare tunanin ba taga ya dannan wani abu bangon gurin yayi qasa, waro idanunta tayi kamar za su zazzago tare da rufe bakinta da hannu, ji tayi kamar za ta saki fitsari ganin ya shige ciki tare da
aga bangon sama
Salati ta fara yi har da fifita saboda baqon abin da ta gani, mamaki da al'ajabi da tsoronta a wannan lokacin fa
insu qauyencine, tana so tayi tambaya saidai babu wanda za ta tambaya a gurin, a taqaice ko akwai wanda zai ba ta amsar toh ita ba ta shirya tambayar da za ta yi cikin tsari ba,
******
Ita ka
ai take zaune tana amfani da wayarta, sai tiqar dariya takeyi, daga gani chatting take yi saboda yadda take sarrafa yatsunta
A cikin nutsuwarta ta fito daga
akin tana tafiya cikin sanyi ta nufo gurin feenat, jin motsi yasa feenat ta juyo, ganin mairo yasa ta saki fuska da fara'a tace
"oyoyo antyna kin fito"
arare ta zauna a kan kujerar tana murmushi tace
"ina kwana"?
"waiwai antyna ai nine da miqa gaisuwa gurin amaryarmu, gashi har qamshin amarci ya fara bulbule min hanci antyna"
Cikin jin kunya tace
"qamshin amarci kuma"?
"sosai antyna, ai ku
in manyane, kin san amare gimbiyoyine sai ana muku biyayya don kar mutum ya kasa ganewa"
Murmushi kawai mairo tayi don taga surutun yarinyar ya fi qarfinta, ita ko feenat sai janta da hira take yi saboda ta sake da ita, suna haka suka ji ana ka
a doorbell
Kallon juna sukayi sannan mairo tace
"kamar kun yi baqi ko"?
"kin yi baqi dai, ke ceh matar gidan ai amaryarmu, bari in je in dubo"
Qofar ta je ta bu
"oyoyo cwt amrat, oyoyo nanie"
Abin da feenat tace kenan tare da rungumo kyakkyawar yarinyar da take ta washe baki
hankalinta ta mayar kan yarinyar da feenat ta rungumo, yarinyar ta mata kyau sosai gashi ta sha ado na mamaki, ba ta ta
a ganin yarinya kyakkyawa kamar wannan ba tsawon rayuwarta,
Riqe da kwandon abinci nanie ta shigo ta nemi guri ta ajiye sannan ta zauna ta mai da hankalinta kan feenat tana cewa
"mun tashi lafiya feenat"
Feenat da hankalinta yake kan amrat tana ta tayata rawar kai da surutun da take yi tace
"lafiya lau nanie, ya su hajiya"?
"lafiya qalau, ya amaryar baban amrat"?
Waigawa tayi gefen da mairo take zaune take kallonsu tace
"ga amaryar nan, lafiyarta lau"
Nanie dai ta kusan kwafsawa domin har ta bu
e baki tace
"wann..."
Sai amarat ta katseta da cewa
"oyoyo my father"
Da gudu ta qarasa gurinsa yayin da yake tsaye cikin khakheensa a jikin qofa, hannu ya bu
e mata cikin farincikin da ba zai iya qiyascewa ba yace
"oyoyo cwthrt"
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/14, 7:04 PM] Dr. Gital
Chapter 29 · 0% Book details