← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 16 OF 42

Sashe 16

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*16*
"ina so ka min wata alfarma"
Da sauri ya tareshi da cewa
"wacce alfarma?, ni babu wata alfarma da zan maka bayan wacce na maka"
Kallonsa kawai fawwaz yake yi ransa a
ace, irin kallon nan ne na ba dan wani abu ba da na yi wani abu
Malam tanimu ne cikin fushi da tsananin haushin da yake ji na baban mairo yace
"Ibrahim ka saurareshi mana ka ji irin alfarmar da za ka masa, me yasa ka zama haka ne kai?, idan yace ba zai aureta ba kana da yadda za ka yi da shi ne?, ko ka kama shi ne lokacin da yake lalata maka yarinyar?, haba wannan wani irin shashancine?"
"toh ya fa
i alfarmarsa ina jinsa amma wallahi matukar alfalmar zai shafi auren ba zan yarda ba, ko ban kama shi ba ai Allah ya kama shi tunda da bakinsa ya amsa laifinsa"
Har malam ya bu
e baki zai cigaba da fa
a fawwaz yayi saurin katsewa da cewa
"alfarmar da nake nema ba za ta hana aurenmu da maryam ba, ina so ka ba ni dama in je in sanar da iyayena domin su samu daman halartar
aurin auren sannan ina so ka san cewa mijin dakake shirin aurar da 'yarka gareshi ba kowa bane, ba shi da komai, bai ajiye ba kuma bai ba wa wani ajiya ba, ina so idan za ka yanke min sadakin ka rangwanta min domin in samu ikon biya"
"ahaff, ni wannan ai bata shafeni ba, ko a jikina, tsuntsun da ya ja ruwa shi ruwa yakan doka, idan
eran masallacine kai tsabar babu ita ta sani, ba ta da miji sai kai, ni ko kyauta zan iya aurar maka da ita ba dan iyakan addini ba, ita ta jawo wa kanta, da ta riqe mutuncinta me za ta yi da aurenka ha
uwar tasha rabuwar bakin gate"
Murmushin takaici fawwaz yayi sannan ya kalli malam da yake bin baban mairo da kallon takaici yace
"malam ka kar
a min ranar auren da ku
in sadakin ni kuma na yi alqawarin duk inda ku
in yake zan nemosu mu zo tare da iyayena kafin ranar da za a
aura auren"
Tun malam bai ce komai ba Ibrahim yayi sauri cewa
"ai ba
ata lokaci za a yi ba, iya qoqarin da zan maka shine sati
aya, sadaki kuwa ko nawane ka kawo domin ba zan
ata baki gurin fa
in abin da ba za a samesshi ba"
Numfasawa ladan yayi yace
"toh ubangiji ya kyauta, ya kaimu nan da satin, sadakin ni zan biya da kaina zai je dai ya taho da iyayensa in Allah ya yarda"
Girgiza kai fawwaz yake yi amma bai ce komai ba
da kyau, hakan ma ya fi tabbas"
Cewar baban mairo,
Ladan bai bi ta kan maganarsa ba ya mai da hankalinsa kan fawwaz yace
"mu shiga ciki Abdullahi ka kwanta ka huta dare yayi"
"zan shigo malam amma ina son yin magana da maryam kafin in shigo"
"toh ba laifi, a shigo lafiya"
Wucewa yayi cikin gidan ya barsu a tsaye a gurin har da baban mairo, shi ma baban mairon shigewarsa yayi gida yana ta masifa abun da ba halinsa ba, wayyo duniya ina za ki da mu
Kusan sama da minti goma suna tsaye a gurin ba tare da sun yi magana da junansu ba, ita mairo kanta a sunkuye yake zuciyarta na ta dukan miliyan miliyan, dukan ya mata yawa, ga tsoronshi da take ji ga kuma sharrin da aka mata, aka mata baqin fenti sannan kuma wai aure ake shirin mata a wulaqance a tozarce, ita kanta ba za ta iya qiyasce quncin da yake cikin ranta ba, kuka ne ya kufce mata ba tare da ya nemi izininta ba, ban da sautin kukan baka jin motsin komai sai haushin karnuka daga nesa
Shi dai fawwaz tun bayan tafiyar su malam ya ke kallon jikin wata bishiyar gwaiba da take saitin gurin da suke tsaye, wanda yake kallonsa zai gane wani irin yanayi da yake ciki maras da
i a qwayar idanunsa, zuciyarsa kuwa ban da zafi babu abin da take masa, baqin cikin abin da ya faru yake ji, yana so ya taimaki yarinyar amma ba shi da niyyar aure kwata kwata, amma babu yadda ya iya da ransa auren mairo a gareshi shine kawai taimako mafi muhimmacin da zai ba ta a daidai wannan lokacin saboda gudun lalacewar rayuwarta.
Sautin kukanta ne ya addabi kunnuwanshi hakan yasa ya juyo gaba
aya ya fuskanceta, kusan minti uku yayi yana kallonta duk da yana da tabbas cewa yarinya ba ta bin maza kamar yadda aka ce balle maganar ciki amma sai yace
"ki fa
a min gaskiya, bana son qarya, me ya jawo wa
annan maganganun?, da gaske ne kina da ciki"?
Kamar abin tsoro haka take kallonsa, ta rasa me za ta ce
Cikin muryar tasa mai dagula lissafi yace
"kin ji abin da nace ko ba ki ji ba"?
Murya na rawa tace
"ni ban san komai akan wannan maganar ba"
"wa yace wa mahaifinki ina nemanki"?
Cikin muryar kuka tace
"ni fa wallahi ban san komai ba, baba haule ce ta fa
a masa, amma Allah ne shaidata bani da alaqa da wani cikin qauyen nan"
"har
an maigari"?
Ba ta san lokacin da ta watsa idanunta cikin nasa ba, abinka da rashin sabo, da sauri ta sunkuyar da kai ta cigaba da shessheqar kuka
"ban ce ki min kuka ba, tambayarki na yi har da
an maigari"?
Girgiza kai tayi ba tare da ta ce komai ba alamar eh amma ba ta bar shessheqan kukan ba
"toh menene na kuka idan har kin tabbatar da gaskiyar abin da kika fa
a?, ko kina kukan auran maqasqancin mutum irina ne wanda ba shi da komai?"
Nan ma da sauri ta girgiza kai domin ita ko wanda bai kaishi bane a ganinta gwara tayi auren da wannan uquba ta gidansu
"ban fahimci abin da kike nufi da girgiza kai ba,? ki bu
e baki ki min magana"
"ko da ka fi kowa talauci ba zan yi kuka saboda zan aureka ba"
"sabo da me?
Yayi saurin taran numfashinta
Shiru tayi sannan ta
ago ta kalleshi tace
"saboda za ka kare min mutuncina kamar yadda kake yi a yanzu"
"Ba kya tunanin zaki sake shiga wani quncin saboda zaki auri miji me qaramin qarfi, kin ga ba lallai ki wadatu cikin gidan aurenki ba kamar yadda maiyuwuwa kike fata"
"um um, bani da sauran buri a rayuwata bayan samin aminci daga tsananin da nake ciki"
"aminci"?
Kai ta ka
a masa tare da sake cewa
"um"
Duk maganganun nan da take yi muryarta a raunace take yi
Wani irin kallon ya mata da ya sanyata sunkuyar da kai
"kin tabbatar da abin da kika fa
a kanta tayi ba tare da ta ce komai ba
Hannayensa ya rungume a qirjinsa yace
"maryam"
ago da kanta tayi a hankali ta kalleshi tace
"na'am"
"inshaa Allahu zan aureki nan da sati guda, na miki alqawari kuma za ki sameni kamar yadda kika yi tsammani, canji zai shigo rayuwarki da izinin Allah, ki je gida zan nemeki gobe inshaa Allah kafin in wuce"
"toh na gode, Allah ya tashe mu lafiya"
Ameen yace sannan ta juya zata tafi gida
"maryam"
Ya sake cewa, juyowa tayi tare da amsawa tana kallonshi ta sanya hannayenta tana share hawayen fuskarta,
"ki kula da kanki kiyi hakuri da duk abinda zaki ji kuma ki gani zai wuce nan gaba ka
an kin ji"
Toh tace masa sannan ta juya ta cigaba da tafiya a
aure
Sai da ya ga ta shige gida sannan ya juya shima ya shiga gida
*******
Dariyar mugunta suke ta qyalqyalawa ita da indo suna maimata abin da ya faru a daren jiya kasancewar baban mairon baya nan ya tafi lambu,
Mairo kuwa a lokacin take shirye shiryen fita da kokon haule, abin da suke ta fa
i a kanta duk da yana qona mata rai amma bata jinsa a ranta kamar kullum, yadda ta nuna ma tamkar ba da ita suke yi ba
"gaskiya baba haule duk da wannan mutumin talauci ta addabeshi amma fa ba laifi yana da kyau"
Cewar indo
"keh ina amfanin wannan kyau nashi, ai shi namiji kyanshi aljihunshi, idan ya kai ruwa kyau mummunane wallahi tunda bashi da qwadala, ni ai na fi kowa murnar auren nan duk da gaskiyar magana zan rasa 'yar nemo ku
i, saidai har na fara hango shegiyar yarinyar nan tana surfe da daka tana ciyar da qaton banza hanu duk kanta"
kwashewa suka yi da dariya don asara irin na uwar banza har da tafawa
"da sauqi ma baba ko ba komai zata dinga kallon fuskarshi tana jin da
i saboda kyawunsa, ba za ta ga wahalar da zata sha
in ba"
"ke dai akwai qaramin qwaqwalwa Abula, har baba haule ta fiki ganewa"
"ni dai ba mai qaramin qwaqwalwa bace saidai indo mai baqin jini"
Cewar Abula cikin jin haushin abin da indo tace mata
"ke dan ubanki ni ce me baqin jinin"?
"ni dai ba ubana ba, na fa
a mai baqin jini, qarya aka miki? ko kare yana zuwa gurinki ne?, ba gwara mairo ba akanki"
Ai kuwa nan suka tashi kamar zakaru sai zagin juna suke yi suna tsine wa iyayensu, duk da haule tana ta musu magana amma babu wanda ya saurareta sai ma
aukan ita ce da indo tayi ta jefa wa Abula, ita ma Abular dutse ta
auka ta jefa wa indon, ai kuwa sai goshinta fas, take jini ya fara wanke mata goshi, ganin jininne yasa tayi kukan kura ta cafki Abula suka fara zuba kokawa, kafin haule ta taso cikin tsautsayi indo ta wawuri qafar Abula ta zuba ta kan robar koko, tuni koko ya watse amma duk da haka da yake abin ya samu masu
acin hali haka sukayi dama dama cikin kunun, hannu baba haule ta saka a ka ta kurma kururuwa
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/23, 6:51 PM] Dr. Gital
Chapter 16 · 0% Book details