← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 42

Sashe 21

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*21*
Carko carko suke tsaye tsakar gidan yayin da haule take ta sheqa rashin mutuncinta, idan hankalin mairo yayi dubu a wannan lokacin to duk sun tashi, har wani irin jiri ne taji yake
ebanta, haka mahaifinta shima a wannan lokacin yana cikin wani irin ru
ani ne da fargaban abin da yake shirin faruwa, musamman kalaman da haule take ta furtawa tun jiya akan lamarin
"yarinya dai anyi asarar haihuwa, daman nasan wannan matsiyacin ba dawowa zai yi ba tun da ya gama samun rabonsa, wa zai auri karuwar gida? ai sai dai mahaukaci da bai san inda kanshi yake ba, toh ga shi nan dai qarya ta qare, jiya ina cewa ya gudu ne kawai abinsa wannan tsohon najadun yace a jira yau, toh ga yau
in tayi ina yake?, yanzu gashi har ana kiran sallar azahar shiru, yanzu kuma wani qaryar zai mana?, kai ni fa bari ka ji malam, wallahi har yanzu ina kan bakata, dole ayi
aya cikin biyu, ko dai yarinyar nan ta bar gidan nan ko kuma ni in barshi domin ni bazan zauna da yarinyar da zata
ata min tarbiyar yara ba, ka ji na fa
a maka"
"haba haule, don Allah kiyi hakuri, babu wanda ya isa ya min wannan cin kashin, tunda yace
an abokinsa ne dole ya nemo sa duk inda ya shiga, ba zan ta
a lamunta......"
Da gudu ta shigo tana haki kamar wacce zaki ya biyo ta, gaba
ayansu suka firgice da shigowar na ta, hakan yayi matuqar tasiri gurin sanqame maganar da baban mairon yake yi, idanunsu duka suka zuba mata suna sauraron abin da za ta fa
Cikin haki tace
"ba...ba...haule!.. motocin sujojine da yawa suka shigo garin nan, kuma...kuma...kuma"
"ke dan ubanki ki yi mana magana mai kyau, duk kin firgita mu, kuma me?"
Tana qoqarin daidaita numfashinta tace
"tambaya suke yi wai ina ne gidan ladan"
Dafe qirji tayi tare da zaro ido tace
"la me?, wani ladan
in?"
Wani irin bugawa qirjin mairo yayi wanda ya janyo mata
aukewar netwrk, yawun bakinta ma qamewa taji yayi, haka kawai taji ta tsargi kanta da shigowar sojojin cikin qauyen, take ta fashe da kuka wanda sautinsa ya doki kunnen kowa a gurin
Jiyowa sukayi da hankalinsu kanta kowa da irin kallon da yake mata
"munafuka ko dai kin san wani abu akan zuwan nasu ne?, in ba haka ba daga cewa sojoji sun zo gidan ladan sai ki tasa mu a gaba ki fashe mana da kuka"
Indo cikin rashin mutuncin nata da ta saba tace
"yoh wa ya sani ko
an iskan nata
an fashine ko wani mai laifin ya
uya a nan jami'an tsaro suka samu labari suka biyoshi, ke kin manta ta'addancinshi"
Cikin yarda da maganarta haule tace
"zancenki dutse indo, tabbas wannan
an fashine ko dan saboda yadda yake nuna wa mutane dabanci, kin manta da bakinsa yace min shi
an iskan gari ne"?
"ina kuwa zan manta baba haule"
lallai kuwa tsohon
an iska, wata qila ya ji labarin suna nemansa shine ya raina mana wayo ya gudu, lallai baban abula da ka zama sirikin
an fashi hhhhh"
Ta qarasa maganar da dariyar mugunta, ni ko nace
amsil basirati
Rasa bakin magana baban mairo yayi, sai zazzare ido yake yi, duk mai kallonsa sai ya tausaya masa don ba za ka gane haqiqanin halin da zuciyarshi take ciki ba sai ka kalli cikin qwayar idanunsa
"toh kai malam ka tsaya kana zare ido, ai zuwa za ka yi ka jiyo mana labari"
Nan ma haka ta sake tuntsirewa da dariyar mugunta har da tafa hanu
Haka kuwa zungwi zungwi ya yi hanyar fita daga gidan, sai dai tun bai qarasa ficewa ba haniyar mutane daga waje ya sashi qarasawa da gudu, firgicewa yayi sakamakon yawan sojojin da ya hango wasu cikin mota wasu da qafa suna qarasowa gidan malam, ita kanta haule da yaranta haniyar ne ya
auko hankalinsu zuwa waje ko lullu
i babu, ita dai burinta idanunta su gane mata abin da yake faruwa
Shi ko malam da ya fito ganin sojojin bai saka shi firgicewa ba sai ma farinciki da godiyar Allah da yayi, take ya fara fa
in Allahu akbar, Allahu Akbar, Allahu Akbar sannan ya
ora da cewa
"kowa yace yaya zanyi ya manta da Allah"
e qofar mota wani daga cikin sojojin yayi, sai ga wani hamshaqi daga cikin sojojin ya sako qafa domin ni a tunanina gee fawwaz
in ne zai fito sai kuma na ga banbancin fuska amma hatta khakheen jikinsa irin na fawwaz ne.
Rufa masa baya wa
ansu cikin sojin sukayi yayin da yake takawa zuwa gurin malam, abinka da qauye har guri ya fara
inkewa da jama'a, wai don hausa people ma sun ce soja marmari daga nesa
Hhhh yoooh ko a birni ne ai sai an kalla balle irin mu da ba mu saba ba, hhh qauye da
Da gudu yaran malam mazan suka ratso cikin mutane a firgice domin rahotonni ya riske kowanne akan sojoji sun zo tafiya da babansu, saidai fa kowannensu cin burki yayi domin ba halin tambaya wai tsohuwa ta shiga turakar
anta
Shafi'u kuwa ya qaraso gurinne daidai lokacin da malam yake gaisawa da abokin general fawwaz, shidai daman ba a firgice ya zo ba domin ya san komai,
duk da bana jin me suke fa
a amma ganin yadda bakin malam yake washewa na san zancen yaji zuma
Su haule sai Allah2 ake yi aga an cacumi ladan an yi gaba da shi amma sai shiru take ji, shi kanshi baban mairon kansa ya kulle, ya rasa me yake shirin faruwa da maqwabcin nasa
Ana haka sai qarar jiniya ta sake doso qauyen, gaba
aya hankalin sojojin da ma sauran jama'ar gurin komawa gurin yayi, take sojojin suka qame cikin jeri tamkar daman can a jere suke, wasu daga cikinsu kuma sai kore jama'a sukeyi, cikin qanqanin lokaci suka samar da wadatacciyar hanya a tsakiya
Kamar yadda ya saba fita haka ne yau ma, motocin sojin ne guda biyu a gaba, sai motar da yake ciki da hajiya bilki da antyn raudat sai wata dattijuwa, yayin da wasu motocin biyu tam da sojojin suke bayansu, kai tsaye suka nufo qofar gidan ladan, sai da aka sake bu
a wa fa sannan motocin ayarin fawwaz suka samu gurin fakin
Ni kaina tun da aka bu
e qofar motar gaban qirjina yake dukan tara tara saboda kokawa baba haule kyakkyawan gamon da za ta yi a yanzu
Qafafuwansa ya fara fitarwa kafin ya sako kai gaba
aya, cikin takunsa na jarumta yake takawa har zuwa qofar gidan malam, kasancewarsa cikin uniform ya
auke masa wancan kamar tasa ta talauci musamman rashin fara'ar fuskarsa, wannan dalili yasa har lokacin da ya qarasa gaban malam babu wanda ya ganoshi cikin jama'ar qauyen
Antyn amrat da hajiya bilkin suma fitowa suka yi yayi da hajiya bilkin take riqe da hannun dattijuwar
Malam da kanshi ya musu jagora cikin gidan yana ta washe baki kamar gonar auduga
Karramawa ta musamman da tar
a me kyau suka samu gurin malam, ji yake kamar ya ha
iye fawwaz, hajiya bilki da ta fara nuna qyanqyaminta wa qauyen ma saida ta sauko ta
an dara saboda barkwancin ladan da iyalansa
Wai fa don hauka har lokacin haule bata fahimci komai ba, saidai zuwa lokacin ta samu daman komawa cikin gida ita da zugarta sai zuba zance suke wai a ina ladan ya samu sojoji haka, wai meye alaqarsu da shi??, nan dai aka saki labarin mairo aka kama na ladan, saidai daga mairo har babanta babu wanda yace uffan, kowa da abin da ya dameshi, ita dai mairo a lokacin ta bar kuka amma jinta take yi a sanyaye kamar ba ta da lafiya kamar irin ana zuba mata qanqarar nan
Sallama akayi a qofar gidan, kasancewar ba a cikin nutsuwarsa yake ba hakan yasa yayi saurin amsawa tun daga cikin gidan tare da miqewa yayi waje
Har bakinsa na rawa yake gaishe da malam da wannan sojan mai irin kayan fawwaz, a mutunce suka amsa sannan suka fara gabatar da abin da ya kawosu ta bakin malam
Sumewane Allah bai ba wa baban mairo damar yi ba amma ya matuqar gigicewa da kalaman bakin malam, a tsorace yake kallon ladan yace
"malam idan dai na maka wani laifine toh don Allah kayi hakuri, na tuba ba zan sake ba, ka min rai, amma ta yaya wancan mutumin zai zama general fawwaz bayan shi sunanshi Abdullahi"?
"eh wannan ma abin da ya kamata ka jimanta ne amma kai kira yalla
in ya zo don Allah"
maganar ya qarashe da yi wa abokin gee fawwaz umurni
Murmushi yayi ya ciro waya ya kira fawwaz a ranshi yana mamaki da al'ajabin abin, shi ko a mafarki bai ta
a tsammanin fawwaz zai nemi aure yanzu ba balle a qauye ma irin wannan
"muna jiranka"
Abinda yace kenan sannan ya jinkirta sai kuma ya sake cewa ok
Ayya fawwaz me masoya, cikin sauri ya fito daga gidan malam, ai kuwa sojoji suka qame, ba tare da ya sauraresu ba ya qarasa gurin da su malam suke ya musu sallama, tunda baban mairo ya
ora idanunsa akan fawwaz ya kasa motsi kuma bai bar kallonsa ba
A ladabce fawwaz ya gaishe sa, muryar fawwaz
in ce ta dawo da shi daga doguwar sumar zaunen da yayi
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/1, 2:03 PM] Dr. Gital

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
Chapter 21 · 0% Book details