← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 42

Sashe 15

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*15*
Wani irin abu ne me
acin gaske ya taso ya tokare wa mairo qirji, numfashinta kuwa sai sassarfa yake yi cikin huhunta, hakan ya jawo
aukewar yawun bakinta, kasa tashi tayi kamar yadda mahaifinta ya umurceta, tozarcin da ake shirin aikata wa gareta ne ya fi komai
aga mata hankali, gaba
aya an birkita mata lissafin qwaqwalwa,
"zaki tashi ne ko kuwa kin raina mahaifin naki kamar yadda kika rainani, fitsararriya,? ni wallahi ba dan kar ace na yi cin fuska ba sai in ce da haihuwarki dai mairo gwara
arin cikinki domin ni ban ga amfanin haihuwar taki ba"
Haulece dai mai mummunan fata ta sake fa
in hakan ga mairo baiwar Allah, shiko ibrahim da yake son ya zauna lafiya da matarshi sai cewa yayi
i ki qara haule, wannan batu naki haka yake, ban ga amfanin da mairo ta min a duniyar nan ba ban da baqin ciki, ace wai wannan yarinyar yaushe aka haifeta amma ta san bin
akin maza, qalu innalillahi wa inna ilaihirraji'un"
Kukan qarya haule ta fashe da shi tana cewa
"ni takaicina Allah yasa babu ciki malam, to gwara cikin ma da irin wannan muguwar cuta mai karya garkuwar jiki, ba za ma a rasa cikin a jikin mairo ba domin alamomin da take nuna wa kwanan nan kenan, aikin kenan zubar da yawu da lasar qasa duk ina lura da ita, ayya mairo ayya mairo baki yi wa mahaifinki adalci ba"
Tana gama fa
in hakan ta sake gigicewa da kukan munafurci
Ai kuwa kamar wanda aka masa allurar doki ya
aga hanu ya gaure mairo da mari tare da haurinta cikin fushi yana cewa
"don uwarki zaki tashi mu tafi ko sai na kusan kasheki a nan gurin, mu je gurin
an iskan naki wallahi saidai ya san yadda zai yi da ke amma ba za a raini cikin shege a gidana ba"
Hausawa suka ce kuka samun dama dariya samun dama, neman hawaye mairo tayi ta rasa sai miqewa tayi ta fara gaba cikin zuciyarta kuwa ban da roqon mutuwa babu abin da take yi, so take kawai ta mutu a tunaninta ko za ta huta da quncin da take ciki, ta manta ko in ce bata san cewa manzon Allah s.a.w yace duk tsanani kar
ayanku ya roqi mutuwa
Shi kuwa mahaifinta yana biye da ita sai haki yake yi irin dai na wanda yayi masifa a rashin sabo
Qofar gidan malam tanimu suka je suka tsaya, a daidai lokacin suna cikin
akin da aka sauki fawwaz suna ta hirarsu, hakan yasa tun a sallamar ibrahim na farko ladan ya ji amma sai da yayi ta kwa
awa har sau uku
Hakan yasa ladan saurin fitowa yana sake amsawa domin a tunaninshi ba lafiyane saboda tun da suke da baban mairon bai ta
a jin muryarshi tayi sama irin haka ba, kwata kwata babu nutsuwa a muryar tasa
"lafiya ibrahim, me yake faruwa"?
A harzuqe yace
"ina baqon gidanka malam?, wallahi duk inda yake ya fito muyi wacce za mu yi da shi domin ba zai lalata min yarinya in zuba masa ido ba, azzalumi yana nan kaman mutumin kirki ashe baqin mugune, to ya zo idan ma da ciki ya san yadda zai yi da shi amma ba za a raini shege a gidana ba"
Tun da ya fara bala'in malam yake kallonsa, mamakine ya daskarar da shi, tambayar kansa ya fara yi anya kuwa yau ibrahim yana cikin hankalinsa, sai da ya ji ya dasa aya sannan ya numfasa yace
"ibrahim akan me kake magana ne?, ni ban fahimceka ba, wani irin magana ce wannan marar fasali"?
Janyo mairo yayi wacce take jingine jikin katanga a gefensa ya wurgata gaban malam yace
"gata nan mairo, baqon gurinka shi ya dinga yaudararta har ya lalata min ita, to wallahi tallahi ba zan yarda ba, ba zan ta
a amince wa
an gaba da fatiha a gidana ba"
"subhanallah, wani irin zancen banzane wannan ibrahim?, menene alaqar Abdullahi da mairo da har zaka zo min da zancen ya lalata maka yarinya?, ita maironce ta ce maka ya mata wani abin"?
"ko mairo ta fa
a ko kar ta fa
a malam duk abin da yake faruwa tsakaninsu ya dawo kunnena, ba fa zan yarda ba, na tabbata haule ba za ta mata qarya ba, toh ga maciji malam ai ba a maganar ja, idan bai lalatata ba ta ina shi kuma cikin da yake jikinta ya zo?, ko kuma tsabar ni ka
ai Allah yake so sai ya ha
a min
a da jika a tare, iyeeh?"
Cikin takaici ladan yace
"eh lallai ibrahim, ban ta
a sanin haukace ta kama ka ba sai yau, idan ba mahaukaci ba yaya za a yi mutumin da yake da kwana shida yau a garin nan ace yayi wa yarinya ciki har ya bayyana?, kai mahaukacin inane ibrahim, to na fahimci abin naka haukane da raini, to bari ka ji in fa
a maka ka tattara 'yarka ka bar min qofar gida tun ban sa yara sun maka korar kare ba, ka je can da tsinanniyar matarka ku nemo wanda ya lalata maka yarinya, balle inshaa Allah saidai ta ga lalacewa akan 'yarta ba dai mairo ba, mahaukacin banza mahaukacin wofi"
Abinka da halin lafiya dan bana ce na hauka ba, cikin masifa da qaiqayin gubar da haule ta saba banka masa yace
"ka dai nemi tsinanne can ba haule ba, yarinyace dai gata nan ku san inda zaku yi da ita wallahi tana tako min gida zan doketa da ta
arya, idan yaso ta shiga duniya wannan ba abin da ya shafeni bane, garin banza ai na farau-farau
in wofine"
"to kuwa saidai ka kasheta nima indai mairo jininka ce ba dai gidana ba, keh tashi min daga qofar gida ki bi ubanki"
Sai jin muryarshi kawai sukayi yana cewa
"malam kayi hakuri, na yarda da abin da yake tuhumata akai, ya fa
i yadda yake so a yi yanzu"
A ki
ime mairo ta taso daga tsugunen da take jin za a tabbatar mata da wani babban laifin da take guje masa, shi kanshi malam a
imauce yake kallon fawwaz irin kallon nan na ban gane ma hauka cikin hankali ba, murmushin takaici yayi yana mai jaddada abin da ya fa
a wa malam da kai tare da fa
"kar ka yi shakka malam, amsa laifi ga mai laifi shine ka
ai mafita"
"ka tabbata"?
Cewar malam yana nuna shi da yatsa, murmushin takaicin ya sake yi yace
"na tabbata"
Kuka ta fashe da shi wanda sautinshi ka
ai zai tabbatar da qunci da baqin cikin da me yinshi yake ciki sannan cikin kukan tace
"wallahi malam ni babu abin da ya ha
a ni da shi, ni bani da komai sharri ake min, ni ko hanuna bai ta
a riqewa ba walla...."
Sai kuma ta kasa qarasawa, abin da ya faru tsakaninsu da safe ta tuna ya hana ta cika rantsuwarta, shi kuma jin tayi shiru ta kasa qarasawarne ya bashi damar takowa kusa da ita ya tsaya ya qura mata idanu cikin hasken farin wata, kasancewar an ci sa'a yau sararin samaniyar ta washe babu hadiri sosai, da sauri ta sunkuyar da kanta tana cigaba da kukanta
"me ya hana ki qarasa rantsuwar?, ki qarasa mana, ummm"?
Jin tayi shiru yasa fawwaz kallon mahaifin mairo yace
"kayi hakuri, ka fa
i abin da kake so a yi yanzu"?
Tuno hu
ubar haule yayi don haka da sauri yace
"matuqar zaman lafiya kake so toh dole ka aureta, hakan ne ka
ai zai sa in rufa maka asiri, amma idan ba haka ba gobe warhaka duk qauyen nan an ji abin da kayi wa mairo, ka je can Allah ya saka min zaluncin da ka yi min akan naka, za ka haifa kai ma"
"shikenan ka yanke mata sadaki, zan aureta amma........."
ISLAM IS MY IDENTITY
[7/22, 4:03 PM] Dr. Gital
Chapter 15 · 0% Book details