← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 42

Sashe 4

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*4*
Cikin qasaitacciyar takunsa irinta jarumta yake shiga cikin gidan,
angaren mahaifiyarshi yayi kai tsaye domin dubo lafiyarta da ta tilon gudan jininsa,
Zaune ya samu hajiyar kan rug tana duba kur'ani sanye da farin glass a idanunta, yadda bakinta yake motsi da er qaramar sautin da take fitowa daga bakinta zai tabbatar da karatun kur'anin take yi
Tsananin farin cikine ya lullu
eshi sakamakon ganin mahaifiyarshi cikin wannan yanayi, shiyasa yake alfahari da samun iyaye masu tsananin riqo da addini, shiyasa kullum yake cikin kewar mahaifinshi tare da masa fatan samun rahamar ubangiji saboda kyakkyawar tarbiyar da ya
orashi a kai
Gefen hajiya hafsat ya je ya zauna yayi shiru yana sauraronta, saida ta kammala suratul waqi'ah sannan ta dakata tayi adduointa suka shafa tare sannan ta juyo ta kalleshi tana murmushi tace
"fawwaz ka qaraso"?
"eh hajiyata, mun tashi lafiya"?
Yace yana murmushi
"lafiya lau, ka baro gurin aikin naka lafiya"?
"alhamdulillah hajiya, ya qawarki, na jita shiru"?
"bacci take yi, tun da aka mata wanka ta koma baccin wai sai babanta ya dawo a tasheta, sanyi take ji"
Cewar hajiya
Miqewa fawwaz yayi ya nufi hanyar
akin amrat da yake cikin
akin hajiya yana cewa
"hajiya ko dai bata jin da
ine tun da tace sanyi take ji"?
"to me 'ya, jeka ka dubota da kanka, ko ba ta da lafiyar ne, wannan uwar iyayi da manyancen ai zata fa
i abin da ya fi haka ma"
Shidai fawwaz murmushi yake yi ba tare da yace komai ba ya tura qofar
akin ya shiga,
Idanunsa ya sauke a kanta, kwance take tana sheqar baccinta cikin kwanciyar hankali, tayi kyau sosai cikin barcin kamar a sace ta a gudu, domin ba qaramin kula yarinyar take samu daga mai rainonta ba, tsab tsab da ita gwanin sha'awa
Bakin gadon ya zauna yana murmushi ya
ago da kanta ya
ora a kan cinyarsa yana shafa kanta tare da fa
"cwthrt, cwthrt tashi ki ga dadynki"
Bai da
e yana kiranta ba ta wata miqa ta rungumeshi tare da shigewa jikinsa sosai tace cikin muryar barci
"dadyna"
"na'am 'yar dady, bacci ake yine"
e idanunta tayi a hankali ta
ago kanta tace
"eh dady, yau ba school in ji nanie"
"haka ne amma kin ci abinci"
Cike da iyayi ta yi alamun mamaki tace
"dady..., yaushe hajiya za ta barni in yi bacci idan banci komai ba"?
Dariya yayi cike da qaunar yarinyar ya sake rungumeta yana cewa
"to tashi mu je gurin hajiyar, nima yau ina da lokacin wuni da ke my cwthrt"
"yehhh dady" tace sannan ta bashi kiss a goshi tace
"nice father"
Shima cikin qauna ya
agata sama ya sumbaceta a kumatu yana cewa
"nice daughter"
Qyalqyalewa take yi da dariya har suka wuce zuwa gurin hajiya.
Hajiya tana ganinsu ta fara dariyar ita ma tana cewa
"k'awalli an tashi kenan, an ga dady"?
"eh" amrat tace tana sak'ale da wuyan babanta
Da sauri ta sauka daga jikin baban ta nufi
an madaidaicin fridge a
akin hajiyar ta bu
e tana kallon abin da yake ciki, rufewa tayi ta
auko wani qaramin plate ta sake bu
e fridge
in ta
auko apple guda biyar ta
ora a kai ta juyo ta nufi dadynta, duk abin da take yi idanu hajiya da fawwaz suka zuba mata suna kallon manyancen yarinyar
"dady gashi ka ci ka ji"
Murmushi yayi yace
"to my amrat zo mu ci tare"
To tace sannan ta
ale kujera ta zauna kusa da shi ta sanya hanunta ta
auko
aya ta mik'a wa fawwaz sannan ta
auko wata zata kai bakinta ya rik'e hannun, kallonsa tayi da yanayin tambaya tace
"dady"?
"cwthrt kin manta daga bacci kika tashi, jeki ki wanke bakinki sai ki zo ki ci ko?"
Murmushi tayi tace
"toh dady"
Sannan ta sauka ta shige toilet
in hajiya ta wanko bakin sannan ta dawo ta
auki apple
in suka fara ci da baban, shi dai fawwaz duk abin da yarinyar takeyi idanunsa na kanta, ko maganar hajiya zai amsa baya
auke ido daga kan yarinyar, duk abin da yake yin hajiya tana lura da shi, sai da ta barsu suka cinye apples
in sannan tace
"ni ko fawwaz ya maganarmune"?
Sai da zuciyarshi ta harba amma cikin nuna rashin fahimta yace
"wacce maganar kenan hajiya"?
Gyara zama hajiyar tayi tace
"maganar aure mana fawwaz, ya kamata fa kayi auren nan, lokaci da
a qurewa yakeyi ko baka la'akari da hakan ne"?
Take annurin fuskarshi ya
auke, sai ma alamomin damuwar da ta lullu
e fuskar
"ya kamata zuwa yanzu a ce ka cire komai a ranka, kai ko ka
an ne ya kamata ka rage ka auro wacce zata maye maka gurbin safiyya"
Hajiyace ta ci gaba da fa
in hakan cikin lallashi
Sai a lokacin fawwaz ya yi magana cikin tashin hankali da damuwa
"bazan samu madadin safiyyata ba hajiya, ta banbanta da sauran mata hajiya, na da
e ina kallonsu hajiya amma babu wacce take da halin safiyyata, ko da wacce take koyi da ita ban gani ba"
"ba haka bane fawwaz, ba ka yi adalci wa sauran iyaye ba matuqar kace babu wacce ta samu halayen safiyyarka"
"hajiya baza ki gane bane"
Ya fa
a idanunsa cike da hawaye
"ni kuwa na gane fawwaz, idan tarbiyyace da safiyya da raudat duk tarbiyyarsu
ayace domin ni da kaina na tarbiyantar da safiyya da yarka, ita kuma yartaka ita ta tarbiyantar da raudat 'yar mijinta amma haka ka tubure kace baka sonta yanzu gashi raudat har da
Cikin k'osawa da maganar yace
"hajiya safiyya ta babanta da raudat da duk wata 'ya mace, ni dai ban ga kamarta ba"
Cikin
acin rai hajiya tace
"to kace kawai baza ka yi aure ba, amma ka daina fa
a min maganar banza, idan so kake yi ka dinga
aga min hankali da kiran sunan safiyya to ka ci gaba, amma ka sani babu wani da yake rayuwa a duniyar nan da ya fini k'aunar safiyya, tawakkali kawai nayi domin nasan baza ta dawo ba sai a darussalam"
Ta gama fa
in hakan ta fashe da kuka, hankalin fawwaz a tashe ya sauko daga kan kujerar yana tsiyayar hawaye shima ya durk'usa a gaban hajiyar ya fara magana
"hajiya don girman Allah kiyi hakuri ki yafe min, bana son kukan nan hajiya"
Amrat ma da take sauraronsu kukan ta fashe da shi ta rungume fawwaz ta baya
"zan yafe maka fawwaz amma dole sai ka nemo mata ka yi aure, hakan ne kawai zai sa in yafe maka in sanya maka albarka"
"na ji na yarda hajiya, ki taimakeni da addua, zan yi aure amma sai na samu wacce ta dace da 'yata, wacce zata bata kulawa da kyakkyawar tarbiyya, ni dai na riga da na rasa wacce ta dace da ni"
Tausayinsa ne ya kama hajiya sosai, ita kanta da akwai yadda za tayi da bata tilasta masa yin auren nan ba, amma halin rayuwa take jiye masa
"addua kullum ina yi maka ita, inshaaAllahu matar farinciki zaka samu ta zama maka madadi, kar ka
ebe tsammani daga rahamar ubangiji"
Hajiyace ta fa
i hakan bayan ta share hawayenta tare da jan hanci
"ki ban lokaci hajiya, zan nemota kwanan nan inshaa Allah"
Murmushin k'arfin hali tayi tace
"Allah ya maka albarka, ya ha
aka da za
in Allah wacce zata dace da za
in ranka sannan ta dace da amrat, safiyya kuma ubangiji ya k'ara lullu
eta da rahamarsa ya kar
i shahadarta, duk lokacin da ka ji tunaninta ya addabeka to ka dage da nemar mata gafara a gurin Allah, ubangiji ya bamu guzirin taras da su, ka dinga dubawa ka rasa mahaifinka ma fawwaz, ka zama mai k'arfin zuciya don watarana nima rasa ni za ka yi komin da
ewa, Allah ya bamu ikon yin mai kyau domin samun dacewa"
Ameen fawwaz yace kansa na qasa, hawayen sun dakata da kwaranya amma idanunsa kamar garwashin wuta, mik'ewa yayi
ya
aga amrat ya
orata a kafa
arsa zai fita daga
akin
"fawwaz"
Hajiya tace, juyowa yayi still idanunsa a qasa suke ba tare da ya kalli hajiyar ba
"ya maganar sadakar da ake musu, ina fatan ba a mantawa"?
Eh kawai yace ba tare da ya kalleta ba ya fice daga
akin
**********
Zaune suke kamar kullum hajiya da jikarta sai ga shi nan ya shigo cikin kakinsa
Da gudu amrat ta je ta
ale shi tana ihun murna, shima cikin farincikin da baya iya
oyewa idan yaga yarinyar ya
agata sama yana shillata sai dariya kuwa gurin amrat kamar gonar auduga, guri ya nema ya zauna yana gaishe da hajiyar cikin fara'a, sun
an ta
a hira sannan hajiyar tace
"ni ko fawwaz ban ji kana maganar zakkah ba bana, ko hankalinka yayi wani gurin"?
Cire hular kansa yayi ya
ora wa amrat a kanta sannan ya kalli hajiyar yace
"ina sane hajiya, ana kan aiki akan zakkar, idan aka cireta zan bayar amma sai na dawo daga tafiyar da zan yi jibi"
Cikin raha hajiyar tace
"dodon maza kenan, zakkarka ta mai raboce, ubangiji ya amsa maka, har kullum ina roqar maka kariya daga ubangijinka tare da aminci"
Murmushi yayi yace
"na gode hajiya"
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/25, 6:21 PM] Dr. Gital
Chapter 4 · 0% Book details