← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 35 OF 42

Sashe 35

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
FASAHA ONLINE WRITERS
*35*
"wacce matar kenan"?
Kai tsaye yace
"haule mana"
"amma ina fata ba a gaban yarinyar kake fa
in wannan kalamai ba, ka dinga tuna cewa fa ita ma mahaifiyarta ce"
"Allah ya sauwaqe, ta je can ta nemi 'yarta da ta haifa ba dai wannan ba"
"ai kuwa ko a addini ita ma mahaifiyarta ce domin irin seat
in da mahaifiyarta take da shi a gurin mahaifinta haka ita ma wannan take da shi, ka ga kuwa dole ka mutuntata a matsayinta ta mahaifiyar matarka"
e rai yayi kamar antyn raudat
un tana gabanshi yace
"addinin da kika zo da shi kenan, toh bari ki ji, maryam dai matatace, ni ke da iko mai qarfi a kanta kuma ina da damar cewa babu wanda zai ganta, kuma dole, tilas a hakura da abin da nace, kuma ita da nake shirin
aureta ma ne za ta zo yi a gidana"
Sai jin muryar hajiya yayi tana cewa
"toh sannu mai mata, ka ji nace sannu, kul ka kiyayeni na fa
a maka, ka rabani da wannan zafin zuciyar taka, ko da wasa kar na sake jin wa
annan maganganun a bakinka, idan ba a ce mahaifiyarta bace a ce wacece?, to ko ma dai menene idan ka tozartata ka tozarta mahaifin matar taka sirikinka kuma, ita kanta yarinyar sai ta ji ciwon hakan idan baka sani ba, ko da wasa ban yarda ka sake zaginta a gabanta ba, na fa
a maka"
Ran nan a
ace yace "shikenan sai mun zo"
Wayar ya jefa a aljihunsa ya kalli maryam yace
"ki fito mu tafi"
Yana fa
in haka ya juya ya fice daga
akin, kujera ya nema cikin kujerun falon da yake kusa da feenat ya zauna ya
ora
aya kan
aya yana girgiza qafa
Yadda feenat taga fuskarsa a tamke yasa ta tashi cikin tsoro da dabara ta koma kujerar nesa da shi sai satar kallonshi take yi
Ita ko mairo da take tsaye cikin sanyin jiki ji tayi hankalinta ya tashi da irin yanayin da ta ga fuskarshi, musamman kiran sunanta da taji yayi a wayar tana da tabbacin fushinsa yana da alaqa da ita,
Cikin sanyi da mutuwar jikin ta
auko gyale ta yafa ta fito tana ta kici kici da gyalen tana yafashi yana zamewa, ko takalmi babu a qafarta
Yadda feenat taga tana yi yasa cikin tsautsayi da rabon ayi tace
"antynmu ba da wannan gyalen ya kamata ki ha
a wannan kayan ba, ki je ki canza"
Kallonta tayi cike da rauni sannan saci kallon fuskar gee fawwaz tace
"toh da wanne zan ha
ewar da ta karanto a fuskarta yasa tace "mu je na za
a miki wanda zai fi kawo wuta"
Toh tace tana yi tana cigaba da satan kallonsa
Har sun juya za su shige
akin suka ji muryarshi cikin tsawa yana cewa
"keh wa ya baki izinin shiga min
aki"
Dukkansu sun firgice amma dukkan alamu sun nuna mairo ta fi tsorata saboda yadda ta qanqame jikinta, cikin rawar murya feenat tace
"babu"
"to ban son raini, kin ji ko ba ki ji ba"
Da sauri tace "naji"
Daga ita har mairon ya banka wa harara sannan ya tashi ya riqo hannun mairon yayi cikin
akinsu sannan ya saketa, da saurin ta matsa nesa da shi
Yadda ya qureta da idanu yasa ta sunkuyar da kai cikin tsinkewar zuciya
"baki ji abin da na ce ba ko"
Kai ta
ago tana girgizawa idanuwanta taf qwallah
Qarasowa yayi gabanta cikin masifa yace
"toh me yasa kika kika mata izinin shigo min hurumina"?
Yadda yayi maganar yasa ta sunkuyar da kai hawaye har ya fara ambaliya, cikin muryar kuka tace
"ka yi hakuri"
Hawayen da ya gani yana tsiyaya daga cikin idanuwanta ya sanyaya masa jiki da zuciya, ha
arta ya tallafo cikin sanyin jikin
"kuka kike yi?, ki daina saurin kuka irin haka, kina tare da wanda zai amintar da ke ne ba wanda zai cutar dake ba, ni kawai na fa
i abin da bana so ne duk kuma a kanki nayi hakan amma ba za ki gane yanzu ba, ke dai ki kiyaye kin ji"
Kai ta ka
a masa tana matsar qwalla, hankyn da ya ciro daga aljihunsa ya fara share mata fuska da shi yana murmushi yace
"kin ga har kin
ata kwalyarki da hawaye, yanzu dai bari na za
o miki takalmi da gyalen sai mu je feenat ta sake gyara min amaryar tawa ko"?
Da sauri ta rufe fuskarta da tafukan hannayenta, abin mamaki su fawwaz har da dariya sannan ya wuce ya fara binciko mata takalmi da gyalen yana cewa "yau zamo taho da sauran kayayyakinki ma daga can, ni ban ga amfanin zamansu a can ba, ko kuwa"?
Shiru tayi ba tare da ta bashi amsa ba, shima bai sake magana ba ya zuba mata takalman a gabanta ya mata umurni da ta sanya sannan ya yafa mata gyalen, duk yadda ya so gyalen ya zauna ya qi har dai ya gaji yace
"anya maryam ba gurin feenat
in zamu tafi ba kuwa, kin san abinka da tsohon gwauro, har na manta yadda ake yi"
Murmushi tayi cikin jin kunya ba tare da ta ce komai ba, hannunta ya riqo suka fice daga
akin, ba su samu feenat a falon ba dan haka kai tsaye qofarta ya je ya tsaya yana qwanqwasawa, tana bu
e qofar ya wanketa da murmushi yace "qanwata ina neman afuwa kin ji, ga antynki idan kun gama sai ku fito mu tafi"
Yana gama fa
in haka ya juya tare da neman guri a falon ya zauna
Tsab suka fito ta qara gyare maryam tare da
ora mata gyale
amas a kafa
arta kamar gwanar abin
Basu tsaya
ata lokaci ba suka wuce gidan hajiya cikin jerin motocin fawwaz ai kuwa sai baza jiniya suke yi a hanya har suka isa gidan
Hannunta cikin nasa suke takawa zuwa cikin gidan yayin da feenat take binsu a baya
Hajiya da tun jin shigowar motocinsa ta fara farinciki da murnar ganin matar
anta da za ta yi fitowa tayi daga can cikin
akinta ita da antyn raudat suka zo tar
arta a babban falon gidan
Suna shigowa hajiya ta tashi ta rungumota tana cewa
"oyoyo da amaryar autana, oyoyo da maryamuna"
Ita ko maryam cikin jin kunya ta fara zamewa daga jikinta amma duk da haka hajiya bata saketa ba sai da ta zaunar da ita kan kujerar kusa da ita itama ta nemi guri ta zauna, qasa mairo ta zame tana gaisar da hajiya da antyn raudat, cike da farinciki suke amsa mata tare da yaba wa hankalinta domin sunyi sunyi ta hau kujerar ta qi yarda sai ma tukuikuye fuska da tayi da gyale
Gaisawa fawwaz sukayi da hajiya da yarsa sannan feenat ma ta gaishesu bayan ta nemi guri kusa da qafafun hajiya ta zauna tare da
aura kanta a kan cinyarta
"feenat baqin gidan gona, ya aka yi"?
Cewar hajiya tana shafa kan feenat
"lafiya lau hajiya, ina babyna"?
"babynki tana school feenat, tun jiya labarin sabuwar momynta yaqi qarewa"
Ta qarasa maganar tana mai da hankalinta kan mairo tana dariya
Kafin wani lokaci tuni ma'aikatan gidan sun shimfi
e wani ha
en carpet a qasa kore shar a tsakiyar falon sannan aka kewaye gurin da duk wani nau'in kayan marmari masu saurin fisgar hankali, abin burgewar kuma sai wa
ansu qananan abubuwa kamar kofunan zinare da aka jerasu a kusa da carpet
in sai fitar da wani rin dadda
an qamshi mabanbanta sukeyi,
Antyn raudat ce ta kamo hanunta ta je ta zaunar da ita kan wani abu na musamman me laushin gaske kalar jikin
awisu, bismillah ta mata tana mata umurni da ta fara cin kayan alfarmar da aka tanadar dominta
Duk yadda akayi da mairo ta ci taqi ci sai ma sunne kai da take tayi kamar mummunar amarya,
"haba antynmu, ko ka
an ki ci mana, sai kin ci fa hajiya za ta ji da
i, don Allah ki ci"
Feenat kenan me fa
in haka, miqewa fawwaz yayi daga kan kujerar da ya zauna yana cewa "wa yace miki ba za ta ci ba, ko san takurawa mutane kawai"
Zama yayi shima akan carpet
in yana fuskantar mairo, ha
a idanu suka yi da shi yana mata murmushi yace "maryam ki ci duk abin da ya miki kin ji, idan kuma kin qoshi toh zaki iya tashi, ko jikinne"?
Cikin rashin sanin amsar da zata bashi ta gya
a kai tana cewa eh
Cokalin fork ya
auka ya soka jikin wani gutsiren kankana sannan ya kalleta yace "ok ci wannan sai ki je ki huta" ta so yin gardama amma yadda ya tsareta da idanu yasa ta miqa hanu ta
auki wani gutsiren kankanar ta kai bakinta ta fara taunawa cikin nutsuwa bayan ta sunkuyar da kanta, cikin salonshi ya sa ta dinga cin abubuwa amma dai a kunyace take saidai tana tsoron masa musu kar ya ji haushi irin na
azu, shi kuwa goga na mairo sai murmushi yake mata abinshi
Hajiya kuwa suka
auke hankalinsu daga kansu suka yi ta hirarsu, ana haka suka ji wayar fawwaz tana zuba qara
ISLAM IS MY IDENTITY
[8/28, 9:21 AM] Dr. Gital
Chapter 35 · 0% Book details