← Book details Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 2 OF 42

Sashe 2

Zakkatah Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*ZAKKATAH*
*MARYAM A.I GITAL*
SADAUKARWA GA
*khadijah ringim*
*Garga
Ban yarda a juya min littafi ba, duk wanda ya canza ko harafi
ayane Allah ya bi min hakkina
*2*
Tsaye yake rataye da hannayensa a baya, idanuwansa na kan wani babban enlargement dake manne a bango ko qyaftawa bayayi tamkar mutum mutumi, matashi za a kirashi don bazai wuce shekara arba'in ba, cikakken na mijine me siffar qarfi da jarumta tare da tsayayyen zati da ubangijinsa ya qaga masa, yana da tsayi amma a tsaye yake car be tanqwara ba, abune me sauqi a ha
a ido da shi a diririce saboda kwarjininsa da tsananin dakewarsa, abin da yafi
aure min kai ga wannan matashi shine zubar hawaye da naga yanayi
aya bayan
aya kan kumatunsa duk da wannan tsumewa tasa, idanunsa kuwa sun riki
e sun burkice saboda damuwa da zubar hawayen da yake ciki, na da
e ina kallon ikon Allah sannan naga ya sake matsawa gab da hoton sannan ya
aga hanu ya
auko shi daga majinginarsa ya rungume a qirjinsa, take kukansa ya qara tsananta cikin wani irin yanayi me ban tausayi, abin da ya sake kashe min jiki shine shessheqar kuka da na ji yana yi, magana naji ya fara yi cikin shessheqar kukan
"na miki alqawari kuma sai na cika shi da izinin Allah, ki yafe min bazan iya barin aikina ba har sai na
au fansa, ki yafe min, ki yafe min, nine silar komai......."
Kasa cigaba yayi da maganar sai ma durqushewar da yayi a gurin yana cigaba da tsiyayar hawaye, bazan iya qiyasce tsawon lokacin da ya
auka a durqushe a gurin ba abin da na sani dai ya
au lokaci me tsawo durqushe a gurin sannan ya miqe tsaye cikin qyaftawar ido abin kamar sarafawar computer, take raunin fuskarsa ya narke zuwa tsananin jarumta da tsoratarwa, hoton ya mayar ma'adaninsa sannan ya wuce zuwa ga wata qofa da nafi tsammanin toilet ne,
******
Tsaye yake a jikin madubi yana gyara ma
allan rigarsa ya ji an turo qofa, ta cikin madubin ya hango su, take fuskar en mazan ta sake riki
ewa zuwa zallar farinciki da annashuwa
Macece da alamomi suka nuna cewar mahaifiyar wannan matashin ne suka shigo
akin da wata kyakkyawar yarinya wacce baza ta fi 4yrs ba, farace qal yarinyar sa
anin matashin da yake baina-baina, shi ba fari qal ba kuma baya cikin baqaqe kamar dai siffar dattijuwar nan, da gudu yarinyar ta cilla tayi gurinshi, shima hanu ya bu
e mata da sauri ya cafeta yayi sama da ita yana juyawa da ita yana cewa
"my cwthrt and lovely amrat"
Dariya take yi cike da murna tana cewa
"my dady..."
Dakatawa yayi ya zauna akan kujera tare da
orata kan cinyarsa ya rungumeta kamar zai maidata ciki, fuskarsa ya mayar kan mahaifiyarsa hajiya hafsat yana murmushi yace
"Allah ya taimaki mahaifiyata, ya qara mata lafiya da imani"
Ameen tace tana murmushin da yake nuna zallar qaunarta ga
anta
"mun tashi lafiya hajiya"?
"lafiya lau fawwaz, ya gajiyar hanya"?
"alhamdulillah hajiyata, yanzu nake shirin zuwa duboku sai ga ku"
Nuna amrat tayi da take saqale da hanu da cikin dadynta tace
"ka ganta nan fitinanniya ita ta dameni da tambayar daddynta tun ba a shiryata ba, tun ina ce mata yanzu zaka zo tana yarda har dai ta fara min kukan rigima wai sai na kawota gurinka"
Murmushin farinciki yayi ya
ago fuskar yarinyar yace
"cwthrt
in daddy na makarane nima ban je duboki da wuri ba, jiya bayan na dawo kuma na je dubaki kina bacci, kiyi hakuri kin ji"
Dariya tayi tace
"toh dady"
Kanta ya shafa yace "yawwa my amrat, me kika kawo wa dadyne"?
Sauka tayi daga jikinsa ta riqo hanunsa tana cewa
"abinci zaka zo ka ci daddy, hajiya tace min ba kyau zama da yunwa, ko hajiya"?
Ta qarashe maganarta tana kallon hajiyar, gya
a kai hajiyar tayi tace
"sosai ma kuwa qawalliyata"
awa tayi kan cinyar hajiyar ta rungumeta tana dariya, farincikinta take nuna wa sosai idan hajiya ta kirata da qawarta, shi ko fawwaz ido ya zuba wa yarinyar cikin wani irin yanayi na tunani da damuwa, idanunsa har sun fara riki
ewa, hajiyace ta kalleshi da nufin masa magana sai ta ga halin da yake ciki, gaba
aya yanayinsa ya canza, juyawa tayi ta kalli amrat tace
"qawata je ki gurin usaina ki ce ta
ora min ferfesun cowtail gani nan zuwa, ki ce ta koya miki yadda ake yi ke ma, idan na sake buqata sai ki min kin ji"
Tsallen murna tayi ta fice daga
akin tana ihun murna,
Kallon tsab hajiya ta masa wanda hakan yasa ya sunkuyar da kai, cikin muryar lallashi hajiya ta fara magana
"haba fawwaz, haba fawwaz ummmm, yanzu ace haka rayuwa zata yi ta juya maka cikin qunci, ashe baza kayi tawakkali ba, shin baka san duk abin da ya faru da bawa muqaddarine daga
bangijinsa ba, a waje ka zama kamar mayunwacin zaki a gida kuma mace ta fika dauriya, ko so kake raina ya
aci in
auke amrat daga gidan nan, wataqila idan ta nisanceka ka samu nutsuwa, kar ka bari na yanke wannan hukuncin fawwaz, kana jina ko?"
ago idanunsa yayi wa
anda suka rine yana kallon mahaifiyarsa ya fara magana cikin rauni
"kiyi hakuri hajiya, ba laifina bane, babu yadda zan yi da zuciyatace, duk lokacin da naga yadda amrat take gudanar da yarintarta sai ta tuno min da safiyyata, hajiya ni na raineta fa ko kin mantane?, na fi kowa tuna yarintar safiyya da quruciyarta ashee....., Allah sarki safiyya....."
"ya isa haka, shikenan, amrat zata koma gidan hajiya bilki, ba sai ka ganta ba sannan hankalinka ya tashi, ai shikenan"
"ki yi hakuri hajiya, ba zan iya barin amrat a wani gidan ba"
Yana gama fa
in hakan ya jingina bayansa jikin kujerar ya rufe idanunsa, hannayensa kuwa har
e suke a kan qirjinsa
Cike da tausayawa hajiya take kallon
an nata, ita kanta ta fa
ane don ta shawo kansa amma baza ta iya
auke amrat daga cikin gidan ba, domin ita ce farincikin gidan gaba
aya, ita kanta hajiyar yarinyar tana tuna mata rayuwar safiyya a tsakaninsu, dauriya kawai ta fi fawwaz, ajiyar zuciya tayi sannan ta tashi ta bar
akin tana me masa fatan samun sauqi a ranta
*******
Cikin shigarsu ta sojoji yake yana tsaye a gaban mahaifiyarsa tana masa adduar Allah ya kiyaye yayin da amrat take riqe da hanunsa sai tsalle tsalle take yi abinta, wayarsa da take hanun sunday ce ta
au ruri, da sauri ya miqa masa cikin ladabi irin nasu na masu
amara, kar
a yayi ya kara a kunnensa yana sauraro, take fuskarsa ta riki
e zuwa
acin rai, bai gama sauraron abin da ake fa
a mishi a yawa ba ya kashe wayar, ya juyo
angaren da sunday yake yace cikin dakakkiyar murya
"sunday"
imauce sunday yace
"sir"
"ka dakatar da kowa, tare da kai kawai zamu fita"
"yes sir"
Cewar sunday tare da sarawa sannan ya juya ya fice
"hajiya zamu wuce"
"Allah ya kaika duk inda zaka je lafiya, ya tsareka, ya kareka, ya baka nasara"
Ameen yace sannan ya sumbaci goshin amrat ya juya ya fice cikin zafin nama amrat tana cewa
"Allah ya tsare dady"
Duk damuwar da yayi da amrat ko juyowa be yi ya kalleta ba balle yace ameen
*******
Duk da a haukace ya shigo falon amma hakan bai sa ya kasa sallama ba, tamkar wani matashin zaki ya tunkari tiqeqen mutumin da yake kwance kan kujera kamar kayan wanki, qafarsa
aya ya
aga ya
ora a kan kujerar da tiqeqen yake babu shakka balle shayi a tattare da shi, da yatsarsa ya fara nunashi yana masa kallon qasqanci sannan ya fara magana
"kar ka sake ka yi wasa da tunaninka, kar ka yi marmarin ganin yadda zaki yake farautar abinci a halin yunwa, ni fawwaz habeeb ba sai ka nemoni ba, ni zan nemoka sai na zame maka tamkar guguwa me tsananin turnuqu da qura mai yaji, zaka jini a lokacin da baka yi tsammani ba tamkar saukar aradu, na rantse maka da ubangijina sai na zame maka tamkar wuta mai tartsatsi da tsananin quna, ka saurara, akwai lokaci zakine ni bana tsoron namun dawa"
Yana gama fa
in haka ya sauke qafarsa qasa sannan ya curo qaramar bindigarsa ya
aga kansa sama ya saita wata kafaffiyar na'urar CCTV ya tarwatsata sannan ya cilla bindigar tana dawowa ya mayar da ita aljihu ya juya cikin takun jarumta tamkar matashin zaki
ISLAM IS MY IDENTITY
[6/21, 7:32 PM] Dr. Gital
Chapter 2 · 0% Book details