Sashe 9
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
An yanke bikin indo da Abu nan da sati biyu,abu anata raban cingam, sai shirin biki akeyi Tani Tana ta gyara Abu, biki ya rage kwana uku aka Kawo akwatin abu guda uku, kaya ne makil anata maganan akwatin ai Abu tafi duka matan garin wannan kayan masu uban yawa kaf kauyen babu wanda aka taba kawo ma kaya irin shi, Tani anata guda da yada habaici ai yarta mai kashin arziki ce, ita dai indo tana daki Tana rusar kuka yanzu dai shikenan dan jummai ya kusa zama mijinta, wasu mata ne tsofaffi guda biyu Suka shigo da bako a hannu nan aka gaigaisa Suka Mika ma Tani bako din tare da fadin ga kayan akwatin indo inji dan jummai, Tani ta saki guda tare da budewa atamfa kala biyu sai leshi guda daya, kuma duk babu dinki, Tani ta fara fadin Abu mai kashin arziki ba irin su o o ba masu kashin tsiya sudai tsofaffi basu ce komai ba Suka fice......
*plz ku sani a addu'a mura da ciwon wuya ya sani gaba*
Taku Maryam obam 😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed, Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
55to60
*DDEDICATED THIS PAGE TO......*
*HAUSA NOVELS GROUP*
*INA YINKU RIN SOSAI DINAN*
*MUSAMMAN.....*
*MUMMYN SULTAN*
*MANANA NOOR*
*HASSY AMINU*
*MARYAM BALA*
Tani ta fara nunawa mutane kayan indo nan masu dariya Suka fara masu tausaya ma indo dai shuru sukayi kaman su jamila, sai shirye2 akeyi na biki amma ita indo inda zata mutu da tafi jin dadi, ji take da zata iya data kashe kanta ta huta, ankai kayan Abu gidan mai Gari gefe daya mai Gari ya ware ma Sulaiman, manyan daki ne ciki da falo da bayi safe content, ginin bulo,babu laifi Tani ta mata kaya na gani da fada domin ta kashe kudi, yan uwan tani Sun cika gidan makil sai guda kake ji a gidan da habaice2 da yan uwan tani da ita kanta tanin suke ma indo, indo na daki Tana kuka ga yunwa tana ji sosai, Tani ce ta bude kofar ta kalli indo sama da kasa tace sannu yar iko, kinzo kin kwanta kina rusa kuka sai kace kanin uwarki ne ya mutu, maza ki tashi kije kiyi wanke2 makira, tashi tayi ta dauki hijab tasa, Tani tace sai shegen rufe jiki kaman munafuka, indo ta fara hada kayan wanke2 yan uwan Tani sai hantaranta suke ita dai bata ce komai ba sai faman hada kaya takeyi harta gama ta fara wanke wa, kayan sunyi yawa sosai sai kace duka kwanukan yan unguwan ne dan yawan su, haka ta wanke su tas, ga yunwa bayan ta gama tani tace maza taje ta dibo ruwa duk da yamma tayi haka ta fita dibo ruwan, haka taita zuba ruwan suna amfani Dashi kuma da gayya sukeyi gashi tani tace sai ta cika komai, haka taita dibowa har aka kira magrib Kafin ta gama, jamila ta faki idon mutane ta shige dakin indo tace mata maza ta fita waje zata fito ta sameta, hakan ko akayi bayan indo ta fita jamila ta sameta a waje, nan jamila ta bata abinci tace taci indo amsa tayi Tana ci kaman za'a kwace Allah Sarki *TAMBARIN TALAKA* *cikin sa* bayan ta gama ci jamila tace indo kin san abdul wanda kika bani labari kwanaki koh? Tace eh yaya Abdul, jamila tace eh yazo nan neman mahaifinki ya hadu da mai gida na, ashe ya taba aiki gidan su abdul din, nan ya bukaci yasan ko ke wacece nan ya fada mishi komai, yace yazo da magana mai mahimmanci ban san dai ko miye ba, amma yace insha Allah zai taimaka miki dan haka ki kwantar da hankalinki kinji, indo tace toh inna jamila nagode, jamila tace tashi ki koma ciki kinji, tashi tayi ta shiga gida tare da tunanin yaushe rabonta da yaya Abdul din ma harta manta, tace Allah sarki yaya abdul ko baka taimakeni ba wannan karan kayi min babban taimako a rayuwa bazan taba manta alkhairin ka ba, wani hawaye mai zafi ya zubar mata a ido, tunawa da Sulaiman da tayi da irin son da yake fada mata yana mata, bata taba son wani namiji ba sai shi amma gashi ya yaudareta gashi sonshi ya kamata har gobe bata tunanin zata iya cire sonshi a ranta, amma tana rokon Allah ya cire mata.
Jummai ce zaune da kawarta mai suna habiba, habiba tace jummai ke yanzu bari Za kiyi dan jummai ya auri wannan yarinyar wacce tun tana karama tasan namiji? Hmm kedai bari habiba aini wlh yanda bana kaunar mutuwa ta haka bana son wannan auren amma dan jummai da babanshi Sun kafe, yanda kika san an musu baki, habiba tace zo kiji naso inji maita fada mata amma na kasa jiyowa, dariya naga sunyi tare dayin tafi.
Rana dai bata karya sai dai uwar diya taji kunya, yau za'a daura aure a kofar gidan mai gari kaman yanda mlm musa ya bukata, auren Abu aka fara daurawa kafin aka daura na indo, nan akai ta yamadidi akan auren musamman ma na indo inda aketa surutu akan auren, kowa abun ya bashi mamaki jin kudin sadakin indo har dubu dari,
Tani na zaune ana ta yada habaici,saiga wata makociyar su ta shigo da sauri Tana fadin tani Tani, Tani tace wannan uwar kira haka, tace ke labari na kawo miki kin san an daura aure kuwa? Tani tace eh yanzu yaci ace an daura, Matar tace To indo dai dan jummai yace ya fasa, Tani tace kaman ya matar tace ai yanzu bada shi aka daura ba da wani aka daura kuma naji anc...... Bata karasa ba mlm musa ya shigo cikin tashin hankali yana zufa Tani tace mlm an daura kuwa? Yace eh an daura sai dai dan jummai yace ya fasa auren nan wani yace yana so a bama danshi, ban musa Ba na amince nan ya zaro dubu dari kudin sadaki ya bada Tani tace kutumar uba mai kace........ Hmmmm wa indo ta aura ku biyoni domin jin amsa...
*kuyi hakuri da wannan dakyar na muku wlh bana jin dadi*
*nagode da addu'a ina yinku sosai*
*Taku Maryam obam*😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
60to65
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*MY AMINIYA KAWAR RAI DA RAI HABIBA BUSY😝*