Sashe 11
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
In mai karatu bai manta ba, kun san lokacin da A majeed yace ma Mum dinshi ta zaba mishi duk wacce ta mata, a lokacin ta kira abdul yace yana hanyar dawowa daka abuja..... Bayan Abdul ya shigo abuja direct wajan Mum din AM ya nufa bayan tasa an cika mishi gaba da kayan ciye2 yaci ya koshi sannan ta kalleshi ta fara mai bayani yanda sukai da AM sannan ta daura da fadin tana son ya sama mata yarinya mai ladabi wacce ya yarda da ita kuma tana son yarinya daka poor family domin bata ga ranan auren yar masu kudi ba, Abdul shuru yayi yana tunani can yace ma Mum akwai wata yarinya Tana taraba a karaman hukuman karan, nan yaba mum labarin haduwansu amma bai fada mata cewan yana sonta ba, ya kuma cewa zai kara bincika akan halin yarinyar, Mum tai ta mishi godiya, tabbas Abdul bayan ya koma gida abun ya dameshi domin yana son indo, sai dai kuma ance kaso ma dan uwanka abunda kake So ma kanka, sai yasa ya soma AM indo abdul yana tausaya ma abokin nashi wanda yake kaman dan uwa a gareshi domin kwata2 Matarshi bata da hali ko kadan, sannan yana ganin AM zaifi kula da indo sosai ba kaman shi ba, Abdul kwananshi hudu ya koma taraba don son sanin wacece indo, yayi tambaya tare da kwatancen indo inda yazo har gidansu nan ya hadu da mijin jamila wanda ya taba aiki a gidan su abdul din, abdul ya fada mishi komai da komai akan abunda ya kawo shi, mijin jamila ya fada mishi abunda ake shirin yima indo tare da bashi labarinta abdul ya tausaya mata sosai tare da fadama mijin jamila zai taimaka mata insha Allah, nan sukai sallama akan zai dawo, koda abdul ya koma yaba Mum labarin indo bai boye mata komai ba kaman yanda aka fada mishi Mum harda hawaye tare da fadin zata kwatan ma indo hakkinta amma abdul ya bata hakuri akan tabar maganan Allah zai saka mata, Mum tace taji Tana son yarinyar ba zata bari a bata wanda ake shirin bata ba, bayan mijinta ya dawo ta fada mishi hukuncin data yanke da farko yaki yarda saida ta nuna mishi damuwa sosai kafin ya amince, ya tura wakili akan aje wajan mai anguwan garin a nema ma dansa auren, mai gari ganin dan governor ne bai musa ba duk da bashi bane mahaifin indo amma kauye suna mutunta masu Gari tare da daukan duk wani abu da sukace da mahimmanci ba kaman bariki ba da aka raina su ba, mai gari ya amince duk da yasan neman aure kan aure babu kyau,yace jibi ne bikin sai su zo a daura, koda Mum da Dad din AM Suka kirashi Suka fada mishi ansa bikin nashi jibi kuma za'a daura bai ce komai ba akan bikin sai rokan su da yayi akan yana son auren ayi shi kaman na sirri, nan Mum tace bai isaba akan wani dalili za ayi *AUREN SIRRI* littafin Sis bagudo Dad dinshi ne yaita bata baki akan tayi hakuri shima koda dan nashi bai fada ba hakan yake ganin za'ayi tunda basu fada ma kowa ba, gashi jibi za'a daura, amma nan gaba kowa ai zaiji, dakyar Mum ta yarda da hakan AM yaji dadin hakan domin dama baya so Zainab ta sani, yaso yayi tafiya shida Zainab din ma Mum ta hana tace kuma jibin dole yazo jalingo babu yanda ya iya dole yaje, su Mum kuma Suka koma washe gari, koda akazo daurin auren his excellency wakilci ya tura, mai Gari mutane an taru sai ga dan jummai yazo yace ya fasa, nan wakilin yace yana So a bama danshi wanda Abdul ne yasa yace hakan nan mlm musa yace ya amince domin yana tsoran indo taki aure sulaiman yace zai aureta nan gaba tunda akwak aure tsakani, amma ganin an bada dubu dari sadakin indo ya tashi yabar wajan cikin tashin hankali.... Toh kunji abunda ya faru har AM ya auri indo...... MUN DAWO KAN LABARI
indo na zaune a falo Tana kuka, tare da tunanin koya za tayi rayuwa a nan oho, gashi bata san waye mijin nata ba, koma dai waye ba damuwan ta bane tunda ta kubuta daka auren dan jummai, toh amma wani mai kudin ne ya aureta kaman yanda taji ana fada kuma ko da ganin tsaruwan falon tasan mahaukacin mai kudi ne mai wannan gidan, duk da a tsorace take domin har yanzu bata cire cewa dan shan jini ta aura ba, domin ganin girman gidan da falon, saboda kuka kanta ya fara mata wani irin mugun ciwan kai ga yunwa domin tun safe bata ci komai ba, haka dai ta kwanta a falon cikin tsoro har bacci yayi awon gaba da ita.
Yan kai amarya sun isa Gida cikin farin ciki dajin dadi, domin da yawansu koda dubu biyar tasu ta kansu basu taba rikewa ba, yau sai gasu da dubu ishirin nasu na kansu, lallai indo yar arziki ce, sai sa mata albarka sukeyi, ciki kuwa harda dangin Tani, gaba daya matan gidan Tani suka shiga nan suka samesu ita da Abu sunyi jugum babu mai magana, nan jamila ta fara gudu sauran matan suka cabe ana fadin indo mai kashin arziki nan suka fara ba Tani labari irin abun arzikin da aka musu da kudin da aka basu Tani dan tsabar bakin ciki kasa magana tayi sai Abu da tasa kuka wai ayi ma mijin indo asiri shima ya aureta kaman yanda akama Sulaiman ya aure ta nan mata aka fara salati.........
Taku maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
70to75
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*ALL MASOYAN NOVELS DINA INA YINKU IRIN SOSAI DIN NAN😍*
Tani ta fara kokarin toshe ma Abu baki, amma ina ta fadi komai, nan mutane sukai ta Allah wadai da halin Tani,ciki harda yan uwanta, wata yar tani ce taja hannun Abu domin a kaita gidan mijinta Abu tana ta tirje2, haka aka fitar da ita, sanda Suka Isa gidan mai gari maman Sulaiman tace sam ita sai sulaiman ya saki Abu domin yanzu akazo aka fada mata asiri akama danta ya auri Abu, nan rigima ta kuma barkewa, saida mai Gari yazo ya kashe wutan tare da cewa akai Abu dakinta, nan Suka shigar da ita ciki, amma maman Sulaiman da yan uwanta Sun kudirin aniyar koran Abu tako wani hali wannan kenan.
Indo wajan asuba ta farka domin ta saba tashi lokacin abun ya zame mata jiki, Tana So taje tayi sallah ta rasa inane bayi, tashi tayi domin taga wata kofa, kitchen ne, tana shiga ta fito da gudu dan tsoro domin kayan electric din Sun bata tsoro takurewa tayi waje daya tana dan kuka kasa2, dai2 lokacin A majeed ya fito cikin jallabiya zashi masallacin kofar gidan, ganin mutum yayi a takure ta rufe fuska da alama ma kuka takeyi, dan tsaki yaja tare da fadin wai wannan abun Mum ta bani a matsayin mata, wani irin haushin indo yaji yana ji, duk da bai taba ganin fuskanta ba, domin a rufe yake, masallaci ya nufa, harya dawo daka masallacin tana nan yanda take kaman zai wuce ya tsaya tare da waigowa, magana ya fara kaman baya son yi kee, indo da sauri ta dago fuskan nan tata ta jagule da hawaye gashi fuskan ta kumbura idonta yayi jaa, wani irin takaici yake ji, yace ki tashi ki shiga can dakin tare da nuna mata da hannu, indo kaman jira take ta tashi da sauri ta nufi dakin tana tafiya kaman zata fadi, domin ita tsoran shi take ji, dan taga mutum sak bature amma yana mata hausa ga shegen kyau, lallai wannan dan shan jini ne, shikenan tata ya kare, koda ta shiga dakin rufe kofan tayi da sauri saboda tsoro, shiko A Majeed tsaki yayi tare da fadin yanzu wannan abun Mum ta zaba min duk matan dake kasar nan, ta rasa wanda zata bashi sai yar cikin shi, toh wannan mai zata iya min? Dan murmushi yayi tare da fadin never bazan iya hada jikina da wannan abun ba, dakinshi ya shige ya kwanta tare da tunanin hanyar da zaibi ya rabu da wannan karaman yarinyar da Mum ta jajibo mishi wai da sunan matarshi a haka har bacci ya dauke shi.