← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 59

Sashe 38

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Washe gari tunda indo ta tashi ta nufi kitchen jikinta ya mata sauki bata jin komai, girki ta fara kokarin daurawa dan taran su inna maryam, saida ta fara hada musu breakfast, ta jera a dinning, Mum ta fito cikin shiri tare da hijab a jikinta ita da dady, Dad da Fara'a yace aysha kin warke kenan ya jikin naki? Amsawa tayi da fadin da sauki Dad, tare da gaidasu cikin jin kunya, nan Suka zauna sukai breakfast, indo ta koma kitchen dan tayi girki, Mum ta shigo kitchen din tana fadin sannu aysha ke daka warkewa sai fara aiki, murmushi kawai tayi, Mum tace zamu Zaria amma yau zamu dawo, matar abokin Dad dinku ne ta rasu, indo tace Allah sarki Allah yaji qanta Mum ta amsa da ameen, munyi waya dasu Maryam sunce Sun taso kudi ta dauko taba indo tare da fadin gashi koda wani Abu zai taso, amsa tayi tare da fadin Allah Ya kiyaye hanya, har wajan mota ta rakasu saida suka fita sannan ta dawo ciki, kitchen ta koma ta daura tuwan shinkafa tare da miyan egusi, falo ta koma ta zauna tana danna wayanta, tare da kallo jefi2 saka wayan tayi a kunne tare da fadin haba Bros shine ka wani shareni koh? Yace sorry sister aiki ne yamin yawa kin san yanzu ni nake kula da komai Na abba, tace ya jikin nashi? Yace da sauki tare da fadin jiya munje hspt anyi mai gashin kafa, tace nazo ma ai hspt din jiya, yace eyya amma maganin da kika bashi yana da kyau dan gskya yace baya jin ciwan jikin nashi kaman kwana biyu da suka wuce, tace nasan yama kusa karewa koh? Yace eh bashi dai da yawa wanda Ya rage, nan tai ta kara bashi shawara akan yanda za'a dinga kula Dashi, yaji dadi sosai inda yake tambayanta ina A Majeed? Dan shuru tayi ba tare da tace komai ba, yace sister lafiya kuwa? Tace lafiya Bros yana lafiya ta amsa ne dan kar ya zargi wani abu, sunyi dan fira kadan kafin sukai sallama, kitchen ta koma ta fara tuka tuwan, ji tayi an riketa ta baya da sauri ta saki kara cikin tsoro, dariya Ya fara yana fadin ki nutsu is ur husband, ajiyan zuciya ta sauke tare da hararanshi taja jikinta daka nashi Tana kara sauke ajiyan zuciya dan tamke fuska yayi tare da fadin baby plz yunwa nakeji, bani wani abu mana inci, cikin yar siririyan muryanta tace aiba ajiye ni kayi ba da zaka ce in baka, ido ya kura mata yana kallon yanda take magana, ganin irin kallon da yake mata yasa ta juyar da kanta, janyota yayi tare da fadin kara fadin abunda kika ce, gabanta taji yana fadi amma duk da haka saida ta bude baki tace nace aiba...... Ganin ya kura mata ido yasa tayi shuru domin Ya Mata kwarjini, dan murmushi yayi tare da fadin u r hardhearted, mai yasa bakya yafiya plz my Baby u have to change fada baya miki kyau, daure fuska tayi tare da fadin plz ka sakeni, hannunshi yasa akan fuskanta yana shafawa tare da fadin yaushe zaki zo muje ki zabi kayan akwatin ki, kin san Nafi son ki zaba da kanki, shuru tayi ba tare Da tace komai ba, saketa yayi tare da fadin plz kiban breakfast am hungry, fita yayi yabar kitchen din tsaki ta sake tare da fadin sai yayi ta taba mutane, kwashe tuwan tayi tare da sakawa a kula, fita tazo yi ta hangoshi a dinning alaman yana jiranta komawa tayi tare dayin tsaki daukan sauran abincin dasu Mum sukaci tayi dan dama ita bata ciba, chips nd egg ne da plantain, sai farfesun naman rago, a plate tasa mai ta zuba mai farfesun a cikin wani bowl, sannan ta hada mishi tea ta jera a Tray ta dauka, tunda ta fito ya kura mata ido harta karaso ta ajiye mai, a hankali ya furta thank dear, har zata wuce ya kira sunanta tsayawa tayi cak ba tare data waigoba yace aysha dan Allah kiban 5mnt za muyi magana ne kaman karta tsaya taji ya kara cewa dan Allah, komawa tayi ta zauna a gefen kujera breakfast dinshi ya fara ci harya gama, sannan ya nufi kujeran da take tare da zama a gefe, yace aysha mai yasa kike min haka? Mai yasa har yanzu kika kasa yafe min? Aysha trust me wlh ina sonki sosai,plz tell me miye matsalanki Dani, kanta a gefe tace matsalanka Dani shine bana sonka ji yyi komai nashi ya tsaya cak, tashi tayi tabar wajan, idanshi ne ya kada yana mai zafi ga knshi dake mishi ciwo lokaci daya, dakyar ya tashi yabar gidan dan baya son zama a ciki kai tsaye gidansa ya nufa, dakyar ya karasa Gida, yana zuwa ya fada kan kujera tare Da lumshe ido, yana mai jin zafin maganan nata, har zata iya fadamai bata sonshi a gabanshi, lokaci daya ya shiga cikin wani hali mai ysa ta yarda ta aureni bayan bata sona Why? Wani irin hawaye mai zafi ya fito mai wanda bai san ya fito ba, lallai yana son aysha amma baya tunanin zaiyi posing nata akan taso shi, duk san da yake mata baya tunanin zai iya zama da ita bata sonshi amma zai fita daka hanyar ta harta tare domin su nema ma kansu mafita.

Inna Maryam tazo indo tayi murna sosai, an farama indo gyaran jiki sosai ga Magani ana bata masu kyau, yau sati daya da zuwan su inna maryam wanda rabon A Majeed da gidan shima yau sati daya bai zoba, inna Maryam Tana lura dako waya basayi, yau indo na daki inna Maryam ta shigo indo tayi Bala'in kyau gyaran Da ake mata, inna Maryam tace aysha tunanin mai gidan akeyi? Indo tayi dan murmushi wanda bai kai ciki ba, inna Maryam tace aysha inaso muyi wata magana wai miye tsakaninki da A Majeed, na dauka kun fahimci juna kafin aka maida auren idon indo ne ya ciko da kwalla tace hakane inna, inna maryam tace aysha fadamin gskiya karki boyemin komai, indo cikin kuka tace wlh har yanzu na kasa gane miye a zuciyata inna ina cikin rudani...

Taku Maryam obam😘

[11/12, 15:17] Hassan Atk: *💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

200to205

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

Daukanta yayi kaman yanda ake daukan jariri, sai kaiwa da komowa yakeyi gata a hannunshi yama rude ya rasa maiya kamata ya mata, toilet ya nufa da ita tare da ajiye ta cikin bath ruwa ya zuba a ciki mai dan dumi, a hankali ta sauke ajiyan zuciya lokaci daya kuma ta rungumoshi tana fadin ka barni ka barni, wani irin tausayinta yaji ya kamashi tare da kara sonta ya kara shiganshi a hankali ya furta sorry Baby na barki, bari in taimaka miki, bude idanta tayi ta ganta a toilet, hada ido sukayi tayi saurin rufewa lokaci daya abunda ya faru ya fara dawo mata, wani hawaye mai zafi ya fara zubar mata tare da fadin maina aikata haka, mai yasa na amince na bashi jikina, shikenan yanzu zan fara ganin wulakanci kala2, jin hannunshi tayi akan fuskanta yana goge mata hawayen tare da fadin aysha plz stop it bana son kukan ki plz my baby, wani irin haushin shi taji yana kara shiganta, shiya taimaka ya mata wankan ta Danji dama2 zugin da takeji kuma ya ragu, fita yayi domin tayi wankan tsarki, bayan ya fita ta fashe da kuka mai ban tausayi tare dayin dana sani dan tasan bawai yana sonta bane kawai jikinta yake so kuma ya samu sai yanda ta gani yanzu, shiko bayan ya fita gyara gadon yayi tare da canza wani zanin gadon, dauke wannan yayi yasa a washing machine ya wanke tare da busar dashi, harya dawo dakin bata fito daka toilet ba, kaman ya shiga ya dubata amma saiya zauna tare da fadin bari ta fito, yayi wajan 10mnt zaune bata fito ba, tashi yayi ya nufi toilet din, ganinta yayi ta kife kanta da giwa tana kuka, cikin tausayawa ya nufeta tare da dagota ya daura mata towel, sannan ya fito da ita, akan gadon dakin ya zaunar da ita, wata rigan Bacci ya kuma dauko mata, ganin bata da niyar sawa yasa ya saka mata Da kanshi, sannan ya kwantar da ita tare da rufeta da blanket, har yanzu Tana jin zafi amma ba sosai ba, shima kwanciya yayi akan kujeran dakin yana mai Tuna abunda ya faru, lallai mata suna suka tara irin nutsuwan da yaji tare da aysha bai taba jiba a wajan Zainab, lumshe ido yayi yana mai kara godema Allah daya bashi aysha a matsayin mata bacci ne ya daukesu duka basu farka ba sai wajan asuba, tashi yayi tare da nufan gadon hancinta Ya danja a hankali ta bude ido, murmushi ya sakar mata tare da fadin tashi kiyi sallah, kokarin tashi ta farayi ya kamota tare da mikar da ita, Jan jikinta tayi daka nashi ta nufi toilet tana tafiya a hankali murmushi yayi shima ya fita daka dakin.
Chapter 38 · 0% Book details