Sashe 20
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
wata doguwar yarinya na gani a tsaye da wani akwati kusa da ita, tasa jallabiya black ta yane fuskanta da gyalen jallabiyan ga glass tasa a fuskanta kallo daya zaka mata kace balarabiya domin irin farinta da kyanta kaman nasu, doguwa ce amma ba sosai ba, ga kirjinta a cike, duk da jallabiyan da tasa bai kamata ba kana kallonta kasan tana da diri mai kyau, gani nayi anyi hugging dinta Mum ce sai yanzu na gane Ashe indo ce😱 cikin jin dadi aysha ta kara rungume Mum, Mum tace aysha barka da dawowa nan driver ya amshi kayan aysha ya tafi Dashi, Mum na rike da aysha kaman wata jaririya suka nufi mota, motoci har biyar akazo daukan aysha indo, direct gidansu Mum suka nufa dake abuja, bayan Sun karasa cikin makeken gidan su, nan sukai ciki Mum takai indo dakinta, indo taji dadi sosai domin ganin wannan ne dakinta an kayata mata shi, komai Pink, harta Cotton din da bed din, dakin yayi kyau sosai Mum fita tayi dan tabar indo ta kimtsa toilet ta fada tayi wanka, tasa wata doguwar riga mai kyan gaske, ta feshe jikinta da turare bata shafa mai ba, ta daura dankwali ta nufi falo inda abinci ke jiranta a dinning, zama tayi Mum tayi saving dinta, indo ta faracin abinci cikin natsuwa da kwarewa, Mum sai kallonta take tana mamakin irin kyan data kara da girma, har indo ta gama nan suka fara fira da Mum, suna cikin haka sai ga Abdul yazo indo ta dan bata fuska, Abdul ya gaida Mum ta amsa cikin Fara'a, sannan ya kalli indo yana murmushi tare da fadin aimin afuwa plz naso inzo in daukeki aka kirani emergency daka office, indo cikin hausanta wanda zaka tadauka tana larabci ne tace aini yaya abdul nayi fushi dakai ka barni a airport inata jira, yace sorry my sister, dan turo baki tayi irin na shagwaba wanda ita bada hakan tayi ba, dariya Suka Saki su duka harda Mum, abdul ido ya kura mata yana ta kallonta yana mamakin irin kyan data kara da girma wanda shi tun asali yana ganin kyanta, ga wani irin wayewa da tayi, gashi magana daya biyu sai tasa turanci da larabci hausan ma kaman bata wani iya sosai ba, haka sukai ta fira har abdul ya tashi yayi musu sallama indo tashi tayi tabi bayanshi domin tana son suyi magana, bayan Sun fita tace yayana wai ya maganan auren naka? Yace hmm ki bari kawai akwai dan matsala ne amma inaga komai ya kusa zuwa karshe, indo tace wani irin matsala kuma? Nan ya fara fada mata yarinyar kaman wacce take rikonta ba yarta bace so kaman bata so yarinyar tayi aure tafi son taita mata bauta, indo shuru tayi tana nazari lallai mata da yawa za suci wuta, dan tuna rayuwanta tayi a baya da yanda yanzu ta sami canji duk saboda Abdul lallai ya kamata itama ta taimaka mishi, nan dai tace bari idan ta dan kwana biyu ta huta za suyi shawara akai, motar A Majeed ne ya shigo cikin gidan, indo kallo daya tamai ta gane shi, dakanshi yake tukin, kawar da kanta tayi taci gaba dayi ma Abdul magana, A Majeed da Tun shigowanshi ya ganta gabanshi yaji ya fadi tare da fadin tsarki ya tabbata ga Allah domin bai gane indo bace dan tayi mugun canzawa, danshi a tunanin shi wata daka cikin yan uwan Mum dinshi ne, bayan yayi parking ya fito ganin yana nufo su yasa indo tayi ma Abdul sallama ta wuce, A Majeed da ido ya bita yana tunanin inda ya santa, Abdul ne ya katse mai tunani da fadin yanzu wajanka nake son zuwa, A Majeed yayi ajiyan zuciya tare da fadin ya akayi Abdul yace maganan zuwa Kaduna, A Majeed yace kai har yanzu kana nan da wannan yarinyar duk da iyayenta sunce sun mata miji, Abdul yace wlh basu mata miji ba kawai dai uwar rikonta ne keda matsala, nan suka tautauna amma gaba daya hankalin A Majeed yana ga yarinyar data shiga yanzu dan haka yace ma Abdul su shirya suje Friday sannan ya shige ciki, koda ya shiga Mum kawai ya gani a falo, bayan sun gaisa ya dan sosa kai tare da fadin Mum kinyi bakuwa ne? Mum tace wace bakuwa kuma? Dan shuru yayi can yace wacce ta Shigo yanzu kaman yar kasar ku ce dai, Mum tayi murmushi tare da fadin au kodai aysha kake nufi, cikin razana ya furta aysha tabbas itace dan yanda yake tunanin a ina ya santa sai yanzu yaga kamannin sak.....
Taku Maryam obam
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
110to115
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
A Majeed gaba daya ya shiga cikin rudani tare dayin daya sani, tunawa yayi da Mum ta taba gaya mishi hala ma tayi aure, hada hannunshi yayi ya buga da karfi, Mum ta kalleshi tace lfya kuwa, idonshi lokaci daya ya kada yayi ja wani irin zafi yake ji kirjinshi nayi, Mum ganin halin daya shiga yasa ta tashi da sauri ta nufo shi tana fadin maike damunka? Dakyar ya furta babu komai Mum kawai kirjina ke ciwo, tashi yayi ya fita Mum ta bishi da kallo yana fita abdul ya kira yace Abdul kana ina ne? Abdul yace ina Gida, kashe wayan yayi ya shiga motarshi ya nufi gidan abdul, bayan Mai gadi ya bude mai gate yayi parking, kai tsaye falon gidan ya shiga abdul na falo yana cin abinci cikin take away, A Majeed zama yayi akan kujera tare da lumshe ido abdul da ido ya bishi bai dai ce mishi komai ba, A Majeed yayi wajan minti biyar kafin yace abdul aysha tayi aure ne? Abdul yace wace aysha kuma? A Majeed yace matata mana, abdul yace toh kai ina ruwanka da ko tayi aure koh batayi ba, A Majeed yace plz ka bani amsan tambaya na kawai, dakyar Abdul ya fada mai cewa batai aure ba, A Majeed wani irin ajiyan zuciya yayi cikin jin dadi domin yasan komai zai zo mishi da sauki tunda batai aure ba, abdul ne ya katseshi da fadin A Majeed mai yasa amma kake son sanin hakan, dan murmushi yayi tare da fadin saboda ina son in dawo da matata mana, abdul yace amma dai wasa kakeyi koh? A Majeed yace wasa fah kace, toh inma wasa kake gani toh ka daina dauka hakan, abdul yace inda zan baka shawara kar kayi gigin furta wannan maganan domin aysha ba ajinka bace ko ka Manta ne, itafa yar aikin matarka ce, ganin abdul na son bata mai rai yasa yabar gidan cikin fushi, Abdul ya girgiza kai tare da fadin Allah ya ganar dakai abokina.