← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 56 OF 59

Sashe 56

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

*Bayan shekara daya*
Indo ce cikin wani tsaddan leshi anyi mishi dinkin doguwan riga tayi kyau sosai yaranta suka nufota suna dariya su ukun duk wanda ya gansu zai ce sun wuce shekara daya dan sunyi girma sosai da wayau, rungumeta sukayi suna dariya ita dariyan tayi tare da fadin karku fadar dani dai2 lokacin A Majeed ya fito yana fadin muje yaran daddy yau zaku kauye koh? Kai suka daga duk da basu san mai yake nufi ba, fita sukayi indo Tana fadin ni garinmu ba kauye bane murmushi yayi sunyi ma Zainab sallama wacce har yanzu burinta bai wuce ace A Majeed ya Saki indo ba, fita sukayi cikin wata katuwar jeep driver ke tuki suna baya shida yaranshi da matarshi da yake kalan jeep din nanne mai baya biyu, wayanshi ne yayi ringing Yusuf ya gani dauka yayi tare da fadin mun fito yanzu kuna ina,ban san Mai yace mishi ba naji yace ga munan zuwa, Sun hade da Yusuf da matarshi da yaranshi biyu abba da Hauwa, suma a tasu motar tafiya sukeyi kaman zasu tashi Sama har suka karasa garin taraba yaran duka sunyi bacci indo tunda suka zo garin gabanta ke fadi amma ganin Sun wuce yasa ta kalleshi tare da fadin ina zamu yace jalingo gobe zamu dawo taraba yamma yayi yanzu ya kamata mu huta bata kara cewa komai ba har suka karasa gidansu na jalingo gidan da aka fara kawo ta nan suka sauka Yusuf dai yace hotel zasu sauka dan bazai kwana gidan kanwarshi ba duk da A Majeed bai soba haka suka tafi kafin su shiga gidan saida yasai musu abinci bayan ya dauki yaran ya kaisu falo masallaci ya nufa dan anata kiran sallah magrib, ita kam indo abubuwan daya faru a gidan ne yake ta dawo mata sai dariya take tayi da yake Tana fashin sallah a haka ya dawo ya sameta Tana dariya kallonta yayi tare da fadin maman uku lafiya kuwa turo baki tayi tare da fadin baban uku driya yayi sosai tare da fadin kina tuna baya ne koh? Lokacin da kike tsoran tv dariya tayi mai karfi tare da tashi takai mai dukan wasa a kirji wajan ya rike tare da fadin ashhh Baby akwai zafi fah, tace toh bakai bane kake tsokana na, yace toh na daina kar a hanani abun dadi ido ta rufe da hannu Tana dariya, yace wai yaushe zaki gama wannan abunne nifa gskya a matse nake tace yaranka dai na wajan dariya yayi tare da fadin bari ma in tashe su suci abinci sai su kwanta tashin su ya farayi bayan Sun tashi shida kanshi ya basu abinci sannan ya kaisu daki ya musu wanka tare da sa musu kayan bacci suka kwanta fitowa yayi daka ganin alama shima wankan yayi yace ma'am kema muje in miki wankan tace nagode bana bukata yace kinma isa dariya tayi tare da fadin kazo muci abinci yunwa nake ji yace ohkey nan suka Fara ci har suka koshi suka nufi daki Dan su kwanta su huta.

Washe gari bayan Sun tashi sunyi breakfast wajan karfe 9 Yusuf yazo suka nufi taraba, kauyansu suka shiga yana nan yanda yake babu wani canji har yanzu dai basu da wuta sai dai wasu gidan an danyi gyare2 ta wajan gidan mai gari suka wuce nan ta hango SULAIMAN cikin wasu matasa duk ya rame kaman bashi ba wani irin hawaye taji yana son zubar mata amma ta dake dan tasan yanzu gogan nata zai fara tambaya idan kuma yaji akan abunda take kwallan tasan zaiyi fushi dai2 kofar gidansu Yusuf ya tsaya dan haka driver dinsu shima ya tsaya gidansu yana nan yanda yake sai kwanon daya cire akasa kalan abun itacen nan gidan ya tsufa sosai, indo ce ta fito Yusuf yace ta shiga taga gidan, gabanta na fadi ta nufi gidan babu kowa saida tayi sallama sannan wata ta fito cikin wasu kaya kaman tsumma saida ta kalleta dakyau sannan ta gane abu ce ita koh abu kallon indo takeyi baki sake tana mamakin kyanta tare da fadin anya mutum ce kuwa Baba Musa ne ya fito ganin abu bata dawo ba shima bakin ya Saki cikin wata shadda duk ta kode gashi tasha faci duk da hakan akwai wajan daya yage, hannunshi daya yana makale a kirji daka gani wani gefen jikinshi ya shanye ne yace hjy wa kike nema ne? Tace Baba musu indo ce cikin kuka yace karya kike yi indo ba haka take ba tace wlh nice baba shima kukan ya Saki yana fadin na gode Allah da bai dauki rayuwa na ba iya tsawon wannan lokacin yau gashi na ganki zan roki gafararki duk da akwai aiki a gabana ban san inda zan sami Yusuf ba, cikin kuka tace Baba tare muke Dashi da sauri yace kice ya shigo mana nan ya shiga daki ya dauko tabarma duk tayi datti ita kam abu mutuwar tsaye tayi dan ta kasa ko motsi, Yusuf tare da A Majeed suka shigo da yara da zaliha A Majeed babu komai a ranshi sai tausayin matarshi dama a irin nan tayi rayuwa, indo batai zaton mijin nata zai zauna akan tabarman ba amma sai taga ya zauna, Abu ce ta fashe da kuka Tana fadin dan Allah indo ki gafarta min nayi miki laifi babba a rayuwa duk kuma shairin tani ne da xugani da takeyi dan Allah ki yafe min nima gashi tun a duniya na fara ganin abunda na shuka, indo tace karki damu Abu na yafe miki ina inna tani? Abu tace Tana ciki nan abu ta shiga ta dauko tani dake daki Tana jinsu Tana kuka ana kawo ta duka suka toshe hanci ta rame ta Side babu kyan gani ga ciwo wajan nononta daka gani cancer ne dan wajan yayi kaman donut yayi rawun, tani ta Fara fadin yusuf indo sai kuma ta kara sakin kuka tare da fadin dan Allah ku gafarta min kunga yanda Allah yayi dani koh, duk da abunda ya faru baisa na hakura ba haka naita bin malamai dan mijinki ya koroki ya auri abu wata rana naje wani daji na fadi na soke nonona tun daka lokacin ya fara ciwo harya fara ruwa nasha Magani har na gaji tun ina iya tafiya har na kasa gashi ance sai nayi na asibiti wai daji ne gashi babu kudi mun so mu saida gidan nan mai Gari ya hana wai naku ne duk da a lokacin muna ganin munma yusuf shairi yabar gidan ai gidan ya zama namu Ashe ba haka bane gashi duk yanda naso Sulaiman ya Saki abu lokacin yaki dan nayi mishi mugun sihiri kafin ya yarda ya auri Abu ya rabu dake danginshi tunda suka san asiri aka mai ya auri Abu suka tsaneta sosai shiko kullum santa yake yi kaman ranshi ina ta zugata taita hadashi fada da yan uwanshi harta uwarshi baya Raga mata akan Abu ganin abun nata na yawa yasa suka tashi tsaye wajan addu'a har kadarin mu ya karye kuka ta Saki sosai kafin taci gaba da fadin ranan naga tashin hankali domin aljani aka tura mai yasa ya auri Abu rannan ya fita ya fadi aka dawo dashi Gida yana ta sambatu nan aka gane iska ne aka kira liman ya fara karatu nan aljani yayi magana tare da fadin karku konani dan Allah nima aiko ni akayi nan ya fada musu wanda ya aiko shi nan ya fita koda sulaiman ya farfado aka fada mishi abun daya faru wanda yayi kuka ya farayi tare da fadin yaushe na auri wannan mara tarbiyan ni ban ma san nayi auren ba tashi yayi cikin fushi ya nufi dakin Abu.......

Taku maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

245to250

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*LAST PAGE*
Chapter 56 · 0% Book details