Sashe 5
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Tunda asuba ta farka, duk da jikinta baya mata dadi haka ta fito ta share gida sannan ta dauki roba domin dibo Ruwa, gidan kusa da gidansu basa nan, dan haka ta nufi rafi, ta dibo ruwan tana kokarin daurawa a kanta, taji an rike mata kugu, da sauri ta waiga taga dan jummai ne saurayin Abu, tayi saurin matsawa da baya tare da sakin ruwan ya zube, dariya yayi yace haba yan mata miye abun jin tsoran nifa taimakonki zanyi, indo ta dauki bokintin da nufin ta wuce ya janyota ta fara ihu, ya fara dariya tare da fadin ihunki banza domin babu mai jinki, dan babu kowa a nan kinga gwara ki yarda kiban hadin kai, nifa taimaka miki zanyi, kuka ta fara tana rokanshi akan yayi hakuri ya barta amma ina bai masan Tana yiba, da yaga tana mai ihu yasa ya toshe mata baki da dayan hannunsa, tare da kokarin cire mata riga, tana ta kokarin tureshi amma ta kasa, riganta ya farka nan kirjinta da suke tsaye kyam Suka bayyana nan dan jummai idonshi ya kada tare da kara rudewa, kokarin kai hannu yayi yaji anyi jifa dashi ta gefe, nan aka fara dukanshi ganin dukan bana wasa bane kuma ya gane yaron mai gari ne yasa ya gudu, indo rufe jikinta tayi da dan kwalin kanta tana kuka, sulaiman ganin yanda tayi yasa ya cire Rigan shi ya bata ya koma daka shi sai singlet, mika mata yayi yace gashi kisa, da sauri ta amsa ya juya baya ta saka, yace ta tashi ya rakata gida, bata tashi ba kuma bata mishi magana ba, sai kuka da takeyi, sulaiman jin kukan yake har ranshi domin tunda ya ganta yaji yana sonta, zama yayi kusa da ita yace esha dan Allah kiyi hakuri kibar wannan kukan kizo muje in raka ki gida, kai ta girgiza alaman a'a, yace saboda me, dakyar ta iya furta za'a bigeni, yace kaman ya? Cikin kuka tace dan Allah kayi hakuri karka kara kulani domin inna tace duk sanda na kara kulaka saita kashe ni, daukan bokitin tayi ta diba ruwan, har tayi gaba ta tsaya tace zan aiko maga da riganka nagode, Sulaiman kasa cewa komai yayi domin gaba daya abun ya daure mishi kai, wai wacece Indo? Koma dai wacece ina sonta kuma bana tunanin zan iya rabuwa da ita, tashi yayi domin ya nufi gida dama ya fito gudu ne,ya biyo ta rafi shine yaga wannan aika aikan, koda indo ta nufi gida bata ga kowa ba, hakan ya mata dadi ta nufi daki ta cire rigan Sulaiman da yake ta kamshi mai dadi ta dauko wata kodaddar rigan atamfanta tasa, sannan ta boye nashi rigan, yanzu gari yayi haske makotansu sun bude kofa dan haka nan taje ta dibo ruwan ta cika ko ina, sannan ta hada murhu tasa ruwan kunu, kaman dai kullum, yau da wuri ta hada wainar rogo, gashi Tani ta hanata abinci haka ta fita tallah, tare da rigan Sulaiman inta ganshi ta bashi, amma har takai tasha bata ganshi ba, tana ta yawo wajan motoci tana fadin asai wainar rogo, babu laifi an dan siya, kadan ya rage, har takai yamma sauran bai Kare ba, dan haka ta nufi hanyar gida ga yunwa tana ji, muryan sulaiman taji yana fadin esha, kaman karta tsaya sai dai dole ta tsaya kodan ta bashi rigan shi, tsayawa tayi ya karaso inda take, mika mishi rigan tayi tare da fadin kayi hakuri ban wanke maka ba dan kar inna ta gani, kallonta yake yi yana murmushi, yace Ai yanzu ba nawa bane naki ne rigan, kai ta girgiza alaman a'a ni bana so, yace toh nima dai bazan amsa ba, ajiye mai tayi a qasa tayi gaba binta yayi yana fadin ta tsaya suyi magana, ganin bata da niyan tsayawa yace shikenan anjima zanzo gidan naku, cak ta tsaya tana hawaye tare da rokanshi akan karya zo, ganin tana hawaye yasa ta bashi tausayi yace toh shikenan indai bakya so inzo to kizo mu zauna a can muyi magana, bata musa mishi ba ta bishi, a dan wani dakali Suka zauna, yace esha ina son ki fadamin ke wacece, nan indo ta fad'a mishi tare da fadin dan Allah tunda kaji koni wacece dan Allah ka rabu Dani, Sulaiman idonshi ne ya kada yayi jaa, tabbas ya tausaya mata, ita indo tana ganin idan yasan ko ita wacece zai rabu da ita, amma sai taji sabanin hakan, yace esha tunda nake ban taba ganin macen da naji inaso ba sai ke, labarinki da kika bani yasa na kara sonki sosai, esha inaso kimin alkawari komai zai faru baza ki gujeni ba, har ranan da za muyi aure, tabbas an zalinceki keda dan uwanki, ni na yarda dake bazaki aikata wani abu mara kyau ba, zan tayaki neman dan uwanki har Allah yasa a dace, nidai so nike kimin alkawarin zaki yarda ki aureni sannan ba zaki taba gudu naba komai zai faru, indo shuru tayi domin tabbas karyane tace bata son sulaiman duk da shi din ba Sa'an auranta bane, kaman yasan abunda take tunani yace shi so babu ruwanshi da kudi ko mikami, dan Allah ki amince dani, rufe fuska tayi tare da fadin nima ina sonka amma bazan taba aurenka ba, cikin tashin hankali yace saboda me? Tace Inna ba zata bari inyi aure ba., sulaiman yace karki damu zan ma mahaifina magana duk yanda mukayi zan fada miki, murmushi tayi tare da fadin to ni zan tafi kar ace na dade, yace toh yanzu sai yaushe kuma ko inzo gida anjima zare ido tayi, ganin haka ya fara dariya tare da fadin wasa nake miki amma lokacin da zan fara zuwa ya kusa kinji My esha, bata ce komai ba sai murmushi kawai yace gobe in kin fito diban ruwa sai mu hadu, rufe fuska tayi ta ruga da gudu dan ta tuno abunda dan jummai ya mata......
Yawan comment yawan posting
Taku Maryam obam😘
💅 TAMBARIN TALAKA 💅
NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA
🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝
Vote me on wattpat @maryam-obam
WWW.maryamobamnovels.com
35to40
DEDICATED DIS PAGE TO...
Maryam Obam novel grp😘
Ina yinku irin sosai din nan One luv❤
Murmushi sulaiman yayi, tare da girgiza kai, yana mamakin son da yake ma yarinyar Lokaci daya, koda indo ta shiga gida, Tani da Abu suna tsakar gida akan tabarma suna cin tuwo, sallama tayi babu wanda ya amsa mata, dan haka ta nufi inda tani take tace inna gash..... Tani tace yanzu sauran da kika dawo dashi ubanki ne zai siye yar iska, indo tace inna wlh ina ta yawo dashi amma yaki karewa naga yamma tayi shine na dawo gida, Tani tace maza ki dauka ki fitar min Dashi wlh kar inga ko daya a roban nan, indo dauka tayi ta fita waje tama rasa ina zata dashi, can tace bari taje gaban layin su domin Akwai inda maza ke taruwa suna fira, nan ta nufa ta zauna a gefe da wainar rogon, harta gama zamanta ta gaji babu wanda ya siya, ganin dare nayi yanzu wajan takwas da wani abu, da sauri ta tashi domin ta tuna tana da canjin da suilaiman yabar mata, gida ta nufa tana dan sand'a Allah yasa babu kowa, dakinta ta shiga ta juye wainar rogon duka na saba'in ne, ta kirga kudin ta fito,dakin Tani ta nufa inda ta gansu ita da mlm musa suna yar fira, kanta a 'Kasa tace inna ga kudin, amsa Tani tayi ta kirga taga sun cika dai2 dauko sauran tuwan da suka rage tace gashi, amsa tayi tare da fadin ngd, sannan ta fita, ruwa ta diba a kofi ta nufi dakinta, wainar rogon ta cinye sannan ta hada da tuwan, ranan saboda koshi cikinta kaman zai fashe, haka ta kwanta cikin jin dadi.