← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 59

Sashe 25

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mamaki maganan ya bata dan haka bata kulashi ba sai fara danna abun takeyi tana dubawa, jin tayi shuru yasa ya bude idonshi daya canza kala daka fari zuwa ja, ido suka hada gabanta taji ya fadi domin ganin Yana yinshi, tayi saurin kawar da idonta tana dan kallan abun, dai2 lokacin Mum ta shigo dakin hakan yama indo dadi, Mum tace aysha ya jikin nashi? Ni inaga muje hspt kawai, indo tace Mum VP dinshi ne yahau sosai, zaro ido Mum tayi tare da matsowa kusa da tilon dan nata tace Abdul Majeed, maike damunka haka da har jininka zai hau, idonshi a lumshe suke amma ji yake kaman yace ma mum aysha ce matsalata amma bazai iya ba dan inda zai iya da tun tuni ya fadama Mum din domin yasan shida kanshi bazai tunkareta da zancen ba dan abunda ya aikata... Mum ce ta katse shi da fadin son ka tashi muje hspt, kai ya girgiza tare da fadin a'a Mum aysha zata kula Dani, indo wacce sai yanzu ta kuma magana tace Mum za'a amso mishi magani bari inje driver ya kaini, da sauri yace No kiba driver din yaje, Mum wacce tasan kanin zancen tace rubuta maganin aysha sai driver ya amso mishi, tace To Mum, fita indo tayi daka dakin jim kadan sai gata ta dawo Mum tace ina takardan? Indo tace na bashi ya siyo dan murmushi Mum tayi tare da fadin maimakon kizo in baki kudi sai kika bayar, aysha shuru tayi ba tare da tace komai ba, A Majeed idonshi lumshe amma kirjinshi kaman ya fashe dan takaici, kishin aysha yake ji bai san dawa take mu'amala ba a hspt, jin kirjinshi na zafi sosai yasa hannunshi yana dan dannawa amma kaman karawa yakeyi, duk abunda yakeyi idon indo na kanshi ta dan tausaya mai ko Ba komai dan Mum ne dole ta tausaya mai, dan haka ta tashi ta fita jim kadan sai gata da Ruwa da Cup da kankara a cikin wani bowl ruwan ta zuba a Cup din tare da kankaran, wajanshi ta nufa jin kamshin turaren Nata kaman kusa Dashi yasa ya dan bude ido, fuskanta babu yabo babu fallasa tace ga Ruwa kasha zai rage maka zafin, kin amsa yayi sai ido daya kura mata wanda hakan Yasa take jin wani iri, Mum tace A Majeed ka tashi kasha mana, kai ya girgiza alaman a'a, indo cikin muryanta karama tace ka daure kasha zaisa kirjin ya rage maka zafin kafin a kawo maganin, ganin yanda take maganan kaman za tayi kuka yasa ya tashi yana cije baki ya amsa tare da shanyewa duka, kallonta yayi yana dan murmushi a hankali ya furta thank for care, bata bashi amsa ba sai barin dakin da tayi, jim kadan sai gata da ledan maganin lokacin Mum bata dakin idonshi a lumshe jin kamshin turaren da yake sashi cikin wani hali yasa ya bude ido dan yasan tana wajan, idanshi akan nata murmushi ya sakar mata fuskanta a daure tace ga maganin, kallonta yake yi yanda ta wani tamke fuska, sai yaga ta kara mishi kyau, mika mai maganin takeyi bai amsa ba sai fadi yayi plz bani ruwan da zansha, ajiye maganin tayi a gefe tare da bude goran faro ta zuba mai a cup, bashi tayi ya amsa jiki babu kwari kallonta yayi tare da fadin plz ki taimaka kiban maganin insha bazan iya budewa ba, dan tsaki tayi kadan wanda bata san zai fito ba har yaji, sai jinshi tayi yana fadin kiyi hakuri nasan na takura miki, but dan Allah za kiyi min, wani iri taji dan haka tayi saurin bude ledan maganin ta fara bashi yana sha, harya gama ya kalleta yace ngd da kulawa, tace no need ina maka hakan ne a matsayina na Dr wanda zan iya yima kowa ma hakan tana fadin haka tabar dakin, ido ya lumshe cikin jin zafin kalaman nata, zan iya yima kowa ma hakan, wani irin kishi yake ji tare dajin zafin maganan nata sosai, duk yanda yaso ya cire abun a ranshi ya samu yayi bacci ya kasa, sai juyi yake tayi ga kirjinshi na mishi zafi sosai dan ma maganin da yasha yasa ya dan ragu amma still yana mishi zafi.

Itako dakinta ta fada ta shiga toilet tayi wanka tare dayin alwala dan yin sallah magrib da aketa kira,bayan ta idar da sallah dinne ta zauna akan kujeran dakin tana tunanin kauyensu wani hawaye taji yana zuban mata Allah sarki inna jamila ko kina nan har yanzu a gidan mu? Abubuwan da suka faru a baya suka dunga dawo mata, gaba daya hankalinta taji yayi Gida ko Ba komai ya kamata ace yanzu taje duk da bata son zuwa garin amma kodan taga inna jamila dako sata sami labarin Dan uwanta dole taje,cikin wannan hakin Mum ta shigo ta sameta, kiran sunanta tayi tare da fadin wai ni kam aysha miye matsalanki ne kwana biyu nan, dan shuru tayi tana tunani tana son zuwa Kaduna da garinsu amma bazata iya fadama Mum yanzu ba saboda ciwan dan nata dan taga hankalin Mum ba'a kwance yake ba, kaman Mum tasan abunda take tunani tace aysha nasan kina Tuna baya ne bayan dazu mun gama magana, amma inaga ki shirya jibi sai kije garinku ki duba su inaga hankalinki zai dan kwanta, indo kai ta girgiza tare da fadin Ba yanzu ba mum sai nan gaba, Mum tace akan wani dalili kin fiso kiyi ta damuwa kullum koh? Tace Mum inaso inje amma zan bari sai A.... Shuru tayi wanda kuka yaci karfinta Mum tace kiyi hakuri aysha kibar wannan kukan, shuru indo tayi tana sauke ajiyan zuciya haka Mum taita bata baki akan ta shirya taje jibi din,tace Mum shikenan amma sai naga yanayin jikin nashi tunda ni nake duba shi, Mum tayi dan murmushi tare da fadin karki damu amma Idan kin bukaci hakan sai ki daga tafiyan, tace toh mum kiran sallah isha'i ne yasa Mum barin dakin indo tashi tayi dan yin sallah, bayan ta idar ta zauna amma saita tsinta kanta da zuwa duba A Majeed din dan haka ta tashi ta nufi dakin a zaune ta ganshi akan dadduma alaman ya gama sallah ne, kallo daya tamai ta kawar da idonta gefe tace kirjin ya daina maka zafi? Ido ya kura mata komai nata yana burgeshi a natse, yace ya daina sai dai ina cikin damuwa, kallonshi tayi caraf suka hada ido tayi saurin kawar dakai gefe dan murmushi yayi tare da tashi dakyar ya koma kan gadon dakin, cikin taushin murya tace gobe zan gwada maka VP din inga koh ya sauka sannan ka cire ma kanka damuwa indai Kana son lafiyanka,ido ya kura mata yanda take mai bayani abun har mamaki yake bashi, dan shuru tayi alaman ko zai ce wani abu jin shima din yayi shuru yasa ta juya zata fita, sunanta ya kira da aysha cikin wani irin murya tsayawa tayi ba tare da ta waiga ba, yace plz ki dan dawo ki zauna ko zan iya bacci, waigawa tayi tana mai wani irin kallo shiko murmushi yake mata, kaman bazata koma ba komai ta tuna kuma ta dawo tare da zama akan kujeran dakin tace zan zauna a matsayina na doctor mai burin inga wanda nake dubawa ya samu Lafiya, ido ya lumshe da alama maganan nata ya mishi zafi, amma saiya daure yace babu komai a hakan ma nagode, bata kulashi ba illa wayanta da take latsawa shiko idanshi na kanta ji yake kaman yaje yayi hugging dinta ko zaiji sanyi a ranshi, wayanshi ne yayi kara wacce yake gefen gadon, hannu yasa ya dauka bakuwar number ne, kuma na waje ko ba'a fada ba yasan cewa zainab ce tunda ta tafi bai kirata ba itama haka sai yau, dan haka ya dauka tare da sawa a Kunne, ban san mai take fada mai ba naji dai yana fadin kin san baki isa ki rabani da mahaifiya taba koh, dan haka ki dinga sanin kalaman da zaki fada a kanta yana fadin haka ya kashe wayan gaba daya cikin bacin rai, indo dake zaune tana saurara duk sai taji ya bata tausayi a karo na farko, dan tasan matarshi tafi karfinshi yana mata son daya wuce kima, dan lumshe ido tayi tana tuna abubuwan da suka faru lokacin datai zama a gidan nashi, haushin shi shida matarshi taji yana kara kamata, dan tsaki tayi kadan wanda sai kana gab da ita zaka iya ji, A Majeed da idonshi ke kanta yana lura da duk abunda takeyi jin muryanshi tayi yana fadin aysha dan Allah ki daina tuna baya ki bani second chance, ina mai baki hakuri akan...... Ya isa haka ta katse shi cikin bacin rai, shuru yayi yana kallonta taci gaba da fadin kar kaga dan daman dana baka yasa kaji koh akwai abunda nake nufi a kanka, karka yaudari kanka ya kamata ka bude idonka daka baccin da kake shirin yi, duk wannan abun ina makane a matsayina na doctor sannan kuma ka kasance kai dan Mum ne sai yasa har nake dubaka kar hakan ya baka daman wuce gonarka...... Wani irin hawaye taji yana zubar mata wanda yasa ta kasa karasa maganan dan haka tabar dakin da sauri......

Taku maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

140to145

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Chapter 25 · 0% Book details