← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 51 OF 59

Sashe 51

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Washe gari wajan karfe biyu jirginsu ya daga zuwa London, bayan sun sauka a airport suka hau taxi duk da Dad dinshi yana da Gida a London yace a hotel zasu sauka, direct hotel aka kaisu,indo taji dadin yanayin kasar tare da ganin tsaruwan kasar, bayan sun sauka a dakin da suka kama mai kyau ga girma dakin kaman ciki da falo ne akwai wajan kujeru idan ka kara shiga wata kofa bedroom ne da toilet a ciki, indo akan kujeran dakin ta kwanta dan ta gaji kallonta yayi tare da fadin Baby lafiya kuwa? Tace na gaji da yawa dan murmushi yayi tare da cire mata takalmin kafanta ya ajiye a gefe yace come on muje kiyi wanka sai kici abinci sai mu huta gaba daya dariya tayi tare da fadin anjima zanyi bacci nakeji yanzu ni bana jin yunwa, kallonta yayi, ganin dagaske bata da niyan tashi yasa ya dauketa yayi toilet da ita dariya takeyi tare da fadin plz ka saukeni anjima zanyi bayan sun shiga toilet dinne tace ya fita tayi wankan yace shi zai mata tunda ta gaji babu yanda batayi ba amma haka nan ya cire mata komai tare da kokarin yi mata wankan amma zancen saiya canza salo dan ganin kirjinta wanda yake rudashi dan yana son orange sosai gashi aysha Tana dasu, shafawa ya farayi yana wasa dasu tare da murzasa ido ta Fara lumshewa cikin wani yanayi mai wuyan misaltuwa sucking din boob din ya farayi da karfi ta rikeshi tare da shafa mishi bayanshi da kanshi Tana sauke ajiyan zuciya tare da nishi....... Saida suka dawo hayyacinsu sannan sukai wanka tare da alwala suka fito sallah sukayi ta tashi ta duba jakanka,kallonshi tayi tare da fadin babu cream din dazan shafa, yace yanzu kizo muje mu siya sai muci abinci in mun fita, tace bacci nakeji fah kallonta yayi tare da fadin bazan bari ki kwanta ba har sai kinci abinci baki ta turo sannan ta tashi ta canza kayan jikinta tasa wata doguwar riga tare da boyfriend jacket ta yane fuskanta da Gyale, fita sukayi a kafa suna dan tafiya Tana makale a jikinshi har suka karasa wani super market gefe kuma akwai wajan cin abinci wajan cin abincin suka nufa bayan sun zauna yace mai zaki ci?tace burger nakeso yace ba snack ba abinci wannan sai a siya idan kinci abinci, tace ni shi zanci, babu yanda ya iya shi yasa aka kawo mata shidai yaci nashi abincin, bayan sun gama yasai mata su snack da yawa suka fita super market din suka shiga yana tura keken kayan Tana daukan abunda take bukata har suka gama ya biya suka dawo, suna shiga ciki ta kwanta sai bacci dariya yayi tare da girgiza kai falo ya koma yana kallo tunawa yayi bai kira Zainab ba dan haka ya dauko wayanshi yasa sim dinshi na London doka ma Zainab kira yayi bugu uku ta dauka tare da fadin dear I miss you so much, cikin jin dadi yace nima haka dear ya kike? Tace lfya qlau ya sister dina? Yace Tana lafiya nan sukai fira cikin kulawa daka karshe sukai sallama yana mai kara alfahari dajin dadi domin burinshi kullum yaga Zainab ta canza yanzu gashi ta canza din, Mum ya kira suka gaisa tace ina aysha din yace Mum Tana bacci tace OK inta tashi a gaida min da ita sannan sukai sallama.

Tunda suka zo London kullum indo bacci basu samu sunyi yawo ba kaman yanda taso gashi bata son cin wani abinci sosai sai dai abu daya bataso A Majeed yayi nisa da ita dan tace Tana son kamshin jikinshi duk da ta fahimci abunda ke damunta amma tayi shuru dan bataso ya sani yanzu, shiko abun na damunshi yawan baccin da takeyi ga zaban abinci yau tace wannan gobe wannan, yana zaune a falo ta fito cikin shiri tasa riga da wando tare da daura suwaita a kai mai tsawo, hannunta tasa a gashin kanshi Tana yamutsawa tare da fdin my one tashi muje yawo kasan bamu je ko ina ba, kallonta yayi tare da fadin yau babu baccin? Dan murmushi tayi tare da fadin yau banaji, tashi yayi suka fita ranan sunyi yawo sosai tare da siyayya da yawa sai dare suka dawo suna shiga tayi toilet tayi wanka tare da alwala doguwar riga tasa tayi sallah Tana idarwa ta kwanta a wajan ta fara bacci shigowa yayi ya gnta a kasa Tana bacci dariya yayi tare da fdin bby gskiya gobe dole in kaiki hspt wannan baccin yana cutana, daukanta yayi ya kwantar da ita akan gado tare da rufeta da blanket shima kwanciya yayi kusa da ita tare da janyota jikinshi ya rungumeta a haka bacci ya daukeshi shima.....washe Gari duk yanda yaso suje hspt taki yarda haka ya barta domin ta dage lafiyanta qalau haka taita daurewa suna fita yawo tare da siyayya satinsu biyu cif suka fara kokarin komawa Gida, ana gobe zasu koma suka kuma fita siyayya sosai.

Karfe biyar Suka sauka a Nigeria inda driver gidan Mum yazo daukansu direct gidan Mum suka nufa an shirya musu abinci kala2 Mum tayi mamakin ganin yanda indo ta koma ta kara haske kyau har dan jiki tayi gwanin Sha'awa jikin yayi bul2 Mum yanzu ta tabbatar da abunda take zargi sai dadi takeji tama rasa mai zata bata Mum tace aysha muje kuci abinci bayan sun nufi dinning indo tace ita ta koshi A Majeed ya kalleta tare da fadin wai mai yake damunki ne aysha kwana biyu kallon Mum yayi tare da fadin Mum ki mata magana muje hspt haka tun a can bata cin wani Abu sai snack ga bacci yanzu sosai, Mum tace aysha ya kamata kije a dubaki indo dai shuru tayi dan ita tasan maike damunta, jin Mum tayi Tana fadin bari in kira family Dr dinmu daukan wayanta tayi ta kira family Dr dinsu ita kadai take duba Mum haka Dad Shima yana da nashi, bata dade ba sukazo nan suka gaisa tare da fadin Dr aysha Ya aiki Tana kallon indo wanda kallo daya ta mata ta gane Tana da ciki, nan Mum ta mata bayani akan canjin da indo tayi Dr tayi dariya tare da fadin bari in duba ta Dr aysha muje ciki, tashi indo tayi suka shiga ciki, ta bukaci ta bata fitsari indo tace Dr basai kin gwada ba dan nasan ciki dinne Dr tayi dariya tare da fadin shine kika ki gaya ma mum, tace wlh kunya nakeji yanzu saiki fada mata, fita Dr tayi jim kadan sai ga A Majeed cikin farin ciki da murna a zaune ya ganta a dakinta na da rungumeta yana fadin aysha u r pregnant Alhmdlh Allah na godema ashe nima zanga dana ina sonki Baby ban taba jin labarin da yasa ni farin ciki irin haka ba tun bayan da kika furtamin kalman I love you surutai na soyayya ya dinga mata ji yake kaman ya goyata dan murna haka Mum ta shigo ta samesu ganin Mum yasa ta fara kokarin jan jikinta shima sakinta yayi indo ko kunya taji Mum ta fahimci hakan amma saita basar tare da fadin yanzu dai Dr tace zaki hspt kiyi scan kiga lafiyan jikinki dana Baby Mum tana maganan ne cikin farin ciki duk wanda yaganta yasan Tana murna A Majeed yace Mum bari mu wuce Gida saiki bamu masu aiki ko mutum biyu ne, Mum tace ok amma daka barta in an gyara gidan sai ta koma ko zuwa gobe, babu yanda ya iya dole ya yarda duk da ba hakan yaso ba wucewa yayi masu aiki kuma driver yakai su, A Majeed gidan Zainab ya nufa tayi murnan ganinshi duk da ranta na mata daci tare da kishin mijin nata a hankali ya furta dear baki da lafiya ne? Tace maika gani yace kin rame dariya tayi tare da fadin lafiya na qalau kawai nayi missing dinka ne, peck ya sakar mata a goshi tare da fadin nima nayi missing dinki my dear, ranan dai a gidanta ya kwana amma bini2 ya fita ya kira yaji lafiyan aysha, yace ma Zainab itama gobe zata tare a gidanta ta nuna jin dadinta sosai, washe Gari kaman yanda yace haka kam akayi Zainab bata dauki komai ba sai kayanta na sawa shima saida aka kira mai mota dan kayan suna da yawa, bayan Sun karasa ya nufi gefen Zainab din komai an gyara yayi kyau sosai komai ansa sabo kal, hugging dinshi tayi tare da fadin gidan yayi kyau sosai, nan aka fada duniyar love dama an dade ba'a hadu ba, a kullum yana mamakin yanda Zainab ta yarda take bashi jikinta, fita yayi tare da fadin zaije ya dawo gidan Mum ya nufa dan dauko Indo amma Mum tace ya barta ta kara kwana biyu dan sunje hspt dazu ance cikin wata daya ne da kwanaki Tana bukatan hutu dan cikin baiyi kwari ba abu kadan zai iya sawa ya zube, A Majeed babu yanda ya iya kodan lafiyan matarshi da Baby dinshi dole ya hakura yace Mum kwana nawa za tayi? Tace ban sani ba sosa kai yayi tare da fadin inaso ne dama in dauko mata kaya Mum tace Tana da kaya a nan, shuru yayi tare da fadin yauwa na siya kayan akwatin ta zuwa gobe koh jibi zasu iso kayan sai a kawo mata nan mum tace hakan yayi, kaman yanda yace an Kawo akwatin tare da kayan tsaraban da sukayi akwati guda 18 ya mata ko wanne cike yake makil da kaya gana tsaraban da sukayi mum tace bari a cire mata wanda zata bukata sai akai mata sauran Gida hakan akayi kuwa.
Chapter 51 · 0% Book details