Sashe 23
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Zuciyanta taji yana tafarfasa tare da fadin wai mai yake nufi da ita ne haka, cikin fushi ta waiga amma ganin irin kallon da yake mata yasa ta kasa yi mishi masifan da taso tamai, tsaki ta danja tare da wucewa ta gefenshi ba tare da taji abunda zai fada mata ba, wani irin iska ya furzar cikin wani yanayi mai wuyan misaltuwa,shima cikin ya shiga, koda indo ta nufi falo a nan taga Mum harda Dad suna dan fira, da sallama ta shiga duka Suka amsa, Mum tace a'a likita bokan turai, dan rusuna wa tayi ta gaida Dad da Mum, cikin Fara'a suka amsa Dad yace ya office din dai2 lokacin A Majeed ya shigo yana sallama yana magana kaman baya son yi, amsawa sukayi, zama yayi kusa da Dad din nashi wanda shima Dad din kallonshi yake tare da fadin yauwa kai dama nake nema, wai ya maganan contract dinne? Kayi signing kuwa? Yace eh nayi Dad tare da tashi yana fadin bari in dauko maka, indo tashi tayi ta shige daki, toilet ta fada tayi wanka,tare da alwala bayan ta idar da sallah isha'i tasa wata doguwar rigan bacci ta kwanta tare da lumshe ido, koda A Majeed ya dawo baiga ayshan shi ba gaba daya yaji zaman ya gundureshi amma ya kasa tashi ya tafi dan yana tunanin zata fito ganin har karfe tara da wani abu yasa ya tashi yayi ma iyayen nashi sallama, koda A Majeed yaje Gida baiga Zainab ba hakan bai wani dameshi ba dan inda sabo ya saba duk da abun yana bata mishi rai sosai, bedroom dinshi ya shiga kai tsaye toilet ya shiga wanka yayi ya fito da wani karamin towel yana goge kanshi kaman kullum zama yayi yana gyara gashin kanshi sai kamshi daya kara gauraye dakin Zainab ce ta shigo cikin night gown wanda komai na jikinta ana gani, abun ya bashi mamaki na ganinta a wannan lokacin dan baiyi zaton tana gidan ba kuma abun mamaki yau itace a dakinshi cikin wannan yanayi bai gama tsinkewa ba sai da yaji hannunta cikin jikinshi tana shafa shi tako ina, nan A Majeed ya fara mayar mata da martani dan dama kwana biyun nan dauriya kawai yake ranan yayi mamakin yanda zainab ta saki jiki dashi sosai, cikin jin dadi bacci ya daukeshi, koda ya farka bai ganta a dakin ba, dan murmushi yayi tare dajin dadi harga Allah yana son Zainab sai dai halayanta da baya so har take shirin fice Mai a rai gaba daya, ta gefen Zainab kuwa koda ta koma daki tsaki tayi tare da fadin shegiyan mata maita bani ne yau har nake nemanshi dakai na, gidan wata kawarta taje wata mai maganin mata wacce take Kawo ma kawar tata tazo inda ta basu tace suyi testing Zainab kaman ba zata shaba dakyar ta dan lasa kadan jin dadin maganin mai kama da zuma yasa ta amsa taita sha tun a gidan ta shiga wani hali ba shiri ta dawo Gida, dan tsaki tayi tare da fadin dan ba kara kar aje a maidani tsohuwar karfi da yaji ina cin ganiyan kuruciya Na, koda Gari ya waye A Majeed dakin zainab din ya nufa amma bata ciki ranshi yaji ya baci tare da fadin ina taje da safen nan, wayanshi yaji yayi kara kaman shigowan sako, kaman bazai duba ba ya dauko wayan ya duba sakon daka Zainab dinne *na tafi China jirgin mu 8 zai daga naga kana bacci na wuce saina dawo* wani irin iska ya furzar mai cike da takaici zama yayi tare da fadin wai mai Zainab take nufi Dashi ne haka? Sai kace ba matar aure ba in za tayi tafiya bata gaya min,Dan ajiyan zuciya yayi tare da fadin zanyi maganin abun daukan daya daka key din motarshi yayi ya bar gidan direct gidan mum ya nufa jin motsin mutum a kitchen yasa ya nufi kitchen din dan yasan indai Dad na Gida Mum ke mishi abinci, ganin wacce ke kitchen din yasa shi sakan wani murmushi tare da tsayawa a kofar kitchen din yana kallon yanda take aiki cikin natsuwa, Kare mata kallo yake tayi wacce take dauke da doguwan riga ya dan kama ta saman, kasan kuma a bude yake, ta daura dan kwalin kayan gaba daya ji yake kaman yaje yayi hugging dinta amma babu dama, jin kaman ana kallonta gashi kuma tana jin kamshin turaren shi tun dazu, yasa ta waigo sukai ido biyu wani murmushi ya sakar mata, saurin kawar da kanta tayi tare da waigawa taci gaba dayin aikinta, jin kamshin turaren shi kaman a kusa da ita yasa ta dan waiga ganinshi tayi kusa da ita, har suna iya jin numfashin juna, kokarin kaucewa takeyi dan tabar kitchen din gaba daya amma ya tare hanya domin a gabanta yake, cikin muryanshi Wanda kaman baya son yin magana ya kira sunanta tare da fadin plz ki saurare ni, mai yasa kike irin wannan fushin akai na, kina nunawa kaman baki sanni ba, inaso kiyi hakuri akan duk abunda na miki a bay...... Jin kukanta yasa hankalinshi ya tashi ba tare daya karasa abunda yake son fadi ba, cikin damuwa yasa hannunshi da niyan ya share mata tayi saurin kawar da kanta gefe ganin kaman kukan nata karuwa yakeyi gashi har cikin ranshi yake jin kukan na bai san lokacin daya janyota jikinshi ba tare da lumshe idonshi, da karfi tasa ta tureshi amma ko gezau baiyi ba domin ya riketa dakyu, cin zafin da yayi a hannunshi yasa ya saketa da sauri ta fita da gudu cizonshi tayi a hannun bude wajan yayi ya gani ya tashi yayi ja ga shaidan hakorinta nan a wajan, idonshi daya kada yayi ja ya furzar da wani irin iska mai zafi, fita yayi daka gidan gaba daya kai tsaye gidanshi ya koma gaba daya ranshi a jagule.
Itako indo tana shiga daki ta fada gado tana ci gaba da kuka, wai mai hakan ke nufi mai yake shirin faruwa ne, lallai na yarda namiji bashi da Kunya ko kadan yau itace A Majeed har yake kokarin taba jikinta bayan wasu Lokaci da suka wuce yake nuna kyamanshi akanta a fili ba tare da tuna yanda za taji ba a ranta, wani irin tsananshi taji yana karuwan mata a rai fiye da, dah, ganin zata office yasa ta fada toilet tayi wanka idon nan nata ya dan tashi, powder kawai ta shafa tare da feshe jikinta da turare, ta fito falo cikin riga da zani na Atamfa sai rigan likita akai da wani karamin gyale ta yafe kanta dashi tayi kyau sosai, Mum bata falo dan haka ta wuce office ba tare da tayi breakfast ba, driver ya kaita ya ajiyeta, kai tsaye Office dinta ta shiga ta fara duba mutane takai wajan shabiyu tana ganin mutane sannan ta fito dan ta nemi abinci kusa da asibitin akwai wani wajan snack da coffee, ta ajiye farar rigan Dr din a office ta nufa wajan inda taga yawanci mutanen wajan laraba da turawa sunfi yawa kuma duk yawanci coffee din suke sha, zama tayi akan kujera da babu kowa, nan ta fara duba abunda takeso shawarma tasa a Kawo Mata da chapman, fara ci tayi a hankali kaman bata son ci, yazeed wanda tun shigowanta wajan ya kafeta da ido tashi yayi ya zauna wajan da take tare dayi mata sallama amsawa tayi, sannan yace kiyi hakuri na zauna ba tare da neman izininki ba,dan murmushi tayi tare da tashiwa tace babu damuwa na gama, yace ya zaki tafi daka zama na, plz ki zauna duk maganan da yake mata da turanci yake yinshi, tace sorry ina sauri dai2 lokacin mai amsan kudin yazo tazo zata bayar ya riga ya biya kallonshi tayi a karo na biyu tace nagode tana fadin haka tabar wajan binta yayi da kallo tare da fadin sai yanzu na sami matar aure domin duk irin quality din da yake nema wajan Mace ya gansu a tare da ita wacce ko sunanta bai sani bah...
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
130to135
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Dan lumshe ido yayi tare da tashi wanda kamshin turarenta duk ya cika shi, motarshi ya shiga benz yaja yayi Gida, waye yazeed? Yazeed dane daya tilo wajan iyayenshi bawai ina nufin shi daya Suka haifa ba yana da yaya Mace wacce tana London ita da mijinta, sai shi da iyayenshi suke masifar So kasan cewanshi karami kuma namiji shine yake gabansu kullum babanshi Alhaji Ibrahim dan asalin sokoto ne, yana sana'an mai yana da gidajen mai da dama, yana da kudi sosai amma a abuja suke zaune, tun tuni suke fama da dan nasu yayi aure amma yaki yi Mum dinshi hjy Bilkisu har Yaran kawayenta take kawo mai amma yaki zaba, ganin haka yasa ta zuba mai ido, yana da burin auren Mace mai aji wacce tasan kanta, koh da yazeed yaje Gida tunanin indo yaita yi wanda abun yazo mai a bakon abu, dan murmushi yayi domin yasan bai taba ganin abu yana So ba bai samu ba, yazeed ba fari bane Ba kuma baki bane, chocolate colour kenan yana da kyau dai2 misali, koda indo ta koma Office kira ta samu daka Office din director inda za suyi meeting bayan Sun shiga nan aka fada mata ranakun da zata dinga zuwa Monday da talata, ran Monday da safe talata kuma da yamma hakan ya mata dadi ga kuma albashi mai tsoka, bayan an fito daka meeting dinne ta kira driver yazo ya dauketa bai dade ba yazo, Suka wuce Gida.