Sashe 21
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Indo suna falo suna breakfast harda dady, duk da tana jin kunyan dady amma yana janta a jiki kaman yarshi domin yana tausayama yarinyar, dady yace aysha yaushe za'a fara aiki ne? Kallon Mum tayi alaman tayi magana, Mum tace babu abunda zance gwara ki fada dariya sukasa, indo ganin Mum taki cewa wani abu, yasa tace dady koda yaushe a shirye nake, yace toh Alhmdlh na bada komai naki dama Office dinki na jiranki, indo tayi godiya, dady yayi gyaran murya tare da fadin aysha ya kamata ki shirya kije kiga Gida ki gaidasu koda kwana biyu kiyi musu, Mum tace hakane ya kamata taje taga yan uwanta nima abun yana raina, indo ji tayi kaman an soka mata wani mashi, bata kaunar zuwa garinsu abubuwan da Suka faru suka fara dawo mata, har yau sulaiman na ranta sai dai kuma tana son taji ko anji labarin yusuf, wannan tunanin yasa taji tana son zuwa, nan sukai ta dan fira, A Majeed ne ya shigo gidan idanshi nakan indo daure fuska tayi ganin ita yake kallo, Dad ya tashi tare da fadin zani majalisa yau akwai zama sai na dawo aysha ki shirya Monday sai ki fara zuwa office, A Majeed Dam yaji gabanshi ya fadi domin baya son ta fara aiki kar a mishi kwace amma yasan yanda zaiyi, bayan Sun gaisa da Dad din nashi ya wuce, zama yayi akan dinning din shima ya fara cin abinci, wayan indo ne yayi kara dauka tayi tare da fadin ina nan ina zani, dan murmushi tayi tare da fadin haba fatima ai Nigeria yafi dadi ina tare da Mum dina duk da larabci tale maganan wani kuma da turanci, A Majeed ido ya kura mata yana kallon ta yana mamaki, harta gama wayan, tashi tayi tabar wajan ido A Majeed ya bita Dashi yana mamakin irin yanda ta canza, wayan Mum ne yai kara ta dauka tare da fadin an Kawo ne?ban san mai akace mata ba tace gani nan zuwa, tashi tayi ta nufi dakinta jim kadan sai gata ta fito da Gyale ta kalli A Majeed bari inje in dawo yanzu bazan dade ba, yace ok Mum, bayan fitan Mum indo jin karan kaman an rufe Gate ta dauka A Majeed ne ya fita dan haka ta fito falon, tana sauka ta ganshi wani iri taji kaman ta juya sai taga hakan bai dace ba dan zai dauka ta damu dashi ne, mai makon ta zauna a falon saita nufi kofar fita wajan bukka taje da yake yana bayan gidan, dan kwanciya tayi akan kujera mai kaman lilo tana danna wayanta, jin kaman ana kallonta yasa ta tashi ta zauna ido suka hada kauda kanta tayi taci gaba da danna wayanta, zama yayi kusa da ita, kamshin turaren shi ya bugi hancinta, Tana so ta tashi tana gudun bashi dama domin idan yaga ta tashi haka zai dinga mata, daure fuska tayi, kiran sunanta yayi cikin wani irin murya kirjinta taji yana bugawa da karfi, aysha nasan nayi miki kuskure a....... Tashi tayi tabar wajan da sauri, A Majeed gaba daya jikinshi yayi sanyi wani irin sonta yaji yana kara shiganshi, itako dakinta ta shiga tasa kuka tare da Tuna abunda matarshi Dashi kanshi sukai mata wani irin tsanarshi taji yana shiganta jin an bude kofan dakin yasa ta rufe ido kaman mai bacci Mum ce ta shigo dakin domin ta dawo bata ga A Majeed ba, tana so taji ko ya tafi ne, ganin Indo tana bacci yasa ta koma tare da fadin toh ina ya nufa dan taga motarshi, ko data gidansu ya fita oho, shiko A Majeed kasa tashi yayi yana tunanin yanda zai shawo kan indo ya dauki lokaci mai tsawo a wajan Kafin ya fito yaja motarshi ya tafi,gida ya koma a falo yaga zainab ita da wata kawarta ko kallansu baiyi ba ya wuce Zainab tabe baki tayi kawarta dai bata ce komai ba sai kallon yanda Zainab take wani tabe baki takeyi ita kawar tana fadin inda ita take da wannan Guy din da anga luv, kawar tashi tayi tare dayi mata sallama ta wuce, Zainab daki ta wuce inda taga A Majeed zaune yana danna laptop tace wai A Majeed mai kake nufi kwana biyu kana ta wani shan kamshi, bai kulata ba yaci gaba dayin abunda yakeyi, ganin ya maidata Sauna yasa ta kwace laptop din ta jefar tace ni nafi karfin in dinga maka magana kana kyaleni, kana mantawa da ko wacece Zainab, dan murmushi yayi tare da fadin bani da time dinki fita yazo zaiyi ta tare mai hanya tare da fadin babu inda zaka sai da yarda na, shuru ya mata ba tare daya kuma cewa komai ba, ganin kaman rigiman take so yasa ya barta ya koma ya kwanta tana ta surutai tunani yake tayi very soon zanyi maganin ki kwata2 duk ta fitan mai a rai duk yanda yake sonta....
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
120to125
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Plz nayi mistake a page 115to120 sai nasa 110to115 ayi hakuri plz, yanzu sai a fara daka page 120to125
Zaune take a wajan bukka tana danna wayanta, daka gani tana jin dadin wajan, dan tsaki tayi tare da ajiye wayan ta kwanta akan kujeran lilo din dake wajan ido ta lumshe kaman mai bacci amma idonta biyu,ba komai take tunani ba illa halin da Abdul yake ciki, tare da tunanin ta yanda zata bi ta taimakeshi, domin Abdul yana daya daka mutanan da suka taimaketa wani irin zafi taji ranta na mata tuna irin wahalan da tasha da wanda bata fata koda makiyinta ne ya fada irinshi, kamshin turaren da taji yasa tasan A Majeed yazo wajan domin irin kamshin turaren shi taji, bata motsa ba balle ta bude ido, tayi wajan minti uku tana shakan kamshin ba tare data motsa ba, A Majeed wanda tun zuwanshi ya kafa mata ido yana kallonta yanda take kwance idonta a lumshe, wani irin yanayi yaji yana shiga mai wuyan misaltuwa, ganin idan yaci gaba da kallon nata zai iya shiga wani hali yasa yabar wajan cikin wani yana yi, tafiya yake amma kaman bayayi dan tafiya yake a hankali dan gaba daya jikinshi ya mutu, baiko shiga Gida wajan Mum ba yabar gidan, jin ta dade a haka kuma bata daina jin kamshin turaren ba, yasa ta bude ido amma bata ganshi ba, mamaki ta fara toh ina yake, kodai bashi bane yazo? Amma kuma kamshin shi naji, dan shuru tayi na wani lokaci can tayi tsaki tare da fadin koma dai shine ba damuwa na bane, jin kamshin turaren kaman yana kara mata yawa yasa tabar wajan dan bata son duk wani abu daya dan ganceshi, koda ta shiga ciki bata ganshi ba abun ya daure mata kai tare da tunanin mai yasa toh take tajin kamshin shi, tabe baki tayi alaman bai daman ba.