← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 4 OF 59

Sashe 4

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Murmushi yayi tare da fadin ko bakya son insan gidan kune? Kai ta girgiza alaman a'a, yace ok To muje, tace idan aka ganni dakai za'amin fada, yace ok ina ne gidan, tace dan Allah kar kazo wlh idan inna ta ganka sai anyi min duka, shide mamaki take bashi idan ta kira kalman duka, ganin yanda tayi kaman za tayi kuka yasa yace toh shikenan yanzu a ina zan kuma ganin ki? Tace idan na fito tallah, yace shikenan ki gaida gida, sauri ta farayi kaman zata tashi sama, wani yaro dake wasa a wajan amma yana da wayau yace kai kasan yarinyar can?yaron yace eh, nan ya tambaye shi ina ne gidansu, yaron yace muje in nuna maka, nan sulaiman yace suje, indo Kafin ta shiga gida saida tayi canji a chemist tasai Magani sannan tasha ta boye sauran canjin kar tani yau ma tace tabi wani, bayan ta shiga gida babu kowa a tsakar gidan dakin Tani ta shiga ta ganta a kwance, Tani na ganinta ta tashi tare da mika mata hannu, indo ta bata kudin, kirgawa tayi taga sun cika dai2 Tani tace amma yar nan kina da bakin hali, yau shine kika 'ki zuwa wajan da za'ayi miki juye ki samo min sababbin kudi, ita dai indo shuru tayi bata ce komai ba, nan Tani tayi ta sababi tare da bata wani tuwan dawan daya kwana biyu, amsa tayi dan baci ma za tayi ba dan a koshe take, dakinta ta nufa ta kwanta domin ta huta, maganin da tasha yasa zazzabin ya saketa, ta fara bacci Tani ta shigo taga tuwan a gefe ita kuma tana sharan bacci, Tani tace jar far uba, bacci ma kikeyi fita tayi sai gata da buta ta fara zuba mata Ruwa a jiki da sauri Indo ta tashi cikin tsoro ganin Tani yasa ta tashi tsaye tare da fadin yakuri inna dan Allah, Tani tace dallah rufemin baki shegiya maza fita kije kimin cefane, ta mika mata naira dari gashi ki siyomin wake gwangwani daya, tarugu na goma, albasa na goma farin magi guda daya kuma idan kika dade ni dake ne, kuma wannan tuwan ubanki ne zaici,?tace inna zanci kaina ke ciwo tani ta tabe baki, tare da mika mata kudi, bayan ta amsa ta sakar mata ran kwashi mai zafin gaske fita indo tayi tana hawaye tare da rike kan, kai tsaye inda aka aiketa ta nufa ta siyo komai ta dawo gida, ko zama ba tayi ba ta hada murhu domin daura abincin dare.

A Majeed ne a cikin katon office dinshi, yana danna wayanshi, Abdul ne ya shigo bayan yayi nocking, abdul yace kai A majeed yau wata rana, A Majeed yace mai kake nufi? Abdul yace naga yau ka dawo kuma gaka a Office kaida in kayi tafiya sai kayi kwana biyu baka leko ba, amma yau gaka a office, A Majeed yace kana da sa ido wlh Abdul ni mai ya Kawo ka ma, abdul yace babu komai kawai nazo wajanka ne, so nake muyi magana, A Majeed yace badai a office ba sai ka bari idan nabar office muyi maganan a gida, Abdul sanin halin abokin nashi yasa yace toh ba damuwa tare da tashi ya koma Office dinshi.

Kaman yanda A Majeed yace ma Abdul a gida za suyi maganan hakan ko akayi domin bayan A Majeed ya fito Abdul shima binshi yayi har gidanshi, bayan dukansu sunyi parking A Majeed ya fito, baiko kalli abdul ba yayi ciki, shima abdul din binshi yayi ciki, wani dangareren falo naga abdul ya zauna, irin falon larabawa, falon yayi mugun haduwa da tsari,wata ce ta fito tasa riga gown amma ya tsaya dai2 giwa irin dai kayan da masu aikin turawa ke sawa, ta ajiye ma abdul snack da drink, Abdul ko kallon abun bai yiba, shidai jira yake A Majeed ya fito suyi magana, A Majeed bai fito ba saida ya kwashe wajan 1hr Kafin ya fito cikin bakin jallabiya ba karamin kyau yayi ba, domin ya fito sak balarabe, kallon Abdul yayi tare da fadin ina jinka, abdul yayi ajiyan zuciya tare da fadin kasan ranan da zamu taraba a wajan wani kauye akwai yarinyar da tazo tsallaka titi mu kuma munzo har tayi bar..... Plz ya isa haka abunda kake son fada nake son ji ba labarin wata ba, Abdul yace A Majeed labarin akanta ne domin tana da halaka Dashi, A Majeed yayi tsaki tare da tashi yace idan akan yarinyar da baka santa bane baka ma san inda take ba, zakai min magana so u better change d topic, Coz bazan saurare kaba, Abdul yace A Majeed I know where she is wlh am in love with d girl, A Majeed yace what? Kana nufin kana sonta? Abdul yace haka nake nufi, A Majeed yace kai gaskiya kaban mamaki duk matan dake Nigeria wayayyu, masu class educated ka rasa wacce zaka ce kana So sai mai talla yar kauye, abdul yace A Majeed I luv her and am ready to marry d girl, yarinyar nan za tayi abunda wayayyar Mace ba zata iyayi ba, sannan waye wa da yawa yana sa kauyanci, bani da burin auren macen data waye sosai, nafi son inyi aure a karamin gida, ma'ana gidan da basu da hali, saboda duk abunda na Kawo mata she will appreciate it, amma idan yar babban gida ce tana ganin iyayenta masu kudi ne, komai za tayi ban isa in hana taba, duk munin abun sai dai inna gaji in saketa, sannan ita..... A Majeed yace enough plz ka cikani da surutu am so tired I need to rest, abdul yace ok na tafi, bayan Abdul ya fita A Majeed bedroom dinshi ya nufa tare da kwanciya ya dauki wayanshi ya doka ma Zainab kira, har ya katse bata dauka ba, ya kuma kira shima batai picking ba, tsaki yayi tare da jefar da wayan gefe, domin tun jiya yake kiranta taki dauka ya rasa dalili.

Mlm musa da Tani suna zaune akan tabarma, Mlm musa ya kunna yar Radio dinshi yana ji, suna dan fira jefe2 shida Tani abu na gefe Tana zaune, maganan siyasa ake tayi a Radio din, mlm musa yayi tsaki tare da fadin sai suyi ta maganan sunyi titi da gada, mu ina ruwanmu dasu, mu kawai su bamu abinci, Tani tace aifa kam domin indan talaka akeyi mudai "TAMBARIN TALAKA" RUMBUN SA, yaro ne yayi sallama, bayan Tani ta amsa yace wai ana kiran esha, Tani tace waye kuma asha, kai jeka tambaya wa ake nema, yaron ya fita sai gashi ya kuma dawowa wai indo ake kira, Tani tace wanene yaron yace wani ne a mota, Tani tace kodai Abu akace ka kira? Yaron yace indo akace in kira, tani ta kalli Abu dake zaune tana kumbura fuska tace ke tashi kije hala ke ake nema, tashi abu tayi ta dauko gyalenta duk ya kode amma ita gani take kaman sabo, indo dake d'aki tana jin komai gabanta sai fadi yake domin tunda Yaron yace esha ta gane sulaiman ne, Abu ce ta shigo tana kuka, Tani ta tashi da sauri tana tambaya lafiya? Abu tace tani dan mai gari ne fah, wai kuma wajan indo yazo, harda wani cemin wai sonta yake yi, Tani ta Saki wani uban ashar tare da nufa dakin indo......

Taku maryam obam😘

💅 TAMBARIN TALAKA 💅

NA

MARYAM ALHASSAN DAN'IYA

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝

Vote me on wattpat @maryam-obam

WWW.maryamobamnovels.com

30to35

DEDICATED DIS PAGE TO...

hafsat mamani
(Maman jawaheer)

Ina yinki sosai My darling sis much luv❤

Bude kofar tayi da karfi, indo ta tashi zaune dan tsoro, dakin duhu babu haske, Tani tace ina kike makira, ta kwala ma abu kira tare da fadin kawo min fitila, Abu ta Kawo Mata fitilan tare da haska fuskan indo, Tani tace dan ubanki a ina kika san yaron mai Gari? Indo tace inna ni wlh ban sanshi ba, kawai ya siya wainar rogo ne, Tani tace dan ubanki karya zaki min, indo tace wlh inn..... Tas ta fara marinta tare da dukanta tako ina, ni zaki ma karya, yar iska, dama shine yake lalata ki, shine ya biyoki har gida, Tani dukanta takeyi tako ina, saida ta mata lilis Kafin ta barta, tace wlh idan na sake ganin yazo gidan nan nemanki saina yanka ki yar iska, ta fita fuuuu, zama tayi kusa da mlm musa Tana fadin shima d'an mai garin in banda asara ya rasa wacce zaiso sai wannan makiran yarinyar, kalli Abu yarinya kyakyawa sai dai fari kawai wacan makiran zata nuna mata, mlm musa yace ai yarinyar nan yanda kika san mayya shegia ni dama ta mutu mu huta, Tani tace hmmm yar iskan sai taurin rai inda zata mutun aida nafi kowa murna wlh, Abu tace Tani nifa gskiya ina son yaron mai gari, tani tace bayan mayyar can yace yana so, Abu tace wlh Tani bazan yarda ba nifa shi zan Aura Kin ganshi ne dan gayu, gashi sai kamshi yake yi, ga mota, ni wlh Tani kisan yanda za kiyi in aureshi, Tani tace toh naji Abu na kwantar da hankalinki kaman kin aureshi kin gama, Abu ta wangale baki tana murna, indo na daki Tana kuka gwanin tausayi lokaci daya zazzabi ya kuma rufeta, babu abunda take tunani sai dan uwanta yusuf shine kawai yake sonta ta tabbata inda yana nan da yanzu yana ta rarrashinta yana bata hakuri, yanzu ko ina ina oho, yana da rai ya mutu duk bata sani ba, kuka ta kuma Saki mai ban tausayi,ta dauki lokaci tana kuka har dare ya tsala sosai bacci da yake barawo ne yai awon gaba da ita.
Chapter 4 · 0% Book details