← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 26 OF 59

Sashe 26

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

A Majeed idanshi ne ya kada yayi ja kaman garwashi ga kirjinshi na faman tafarfasa, gaba daya ji yayi zaman gidan ma ya isheshi domin magananta yake taji a kwakwalwanshi yana mai yawo, lumshe ido yayi yana mamakin irin son da yake mata Lokaci daya, hawaye ya fara zuba a idonshi tare da karayin nadaman abunda yayi mata, tabbas duk yanda kaga mutum karka taba wulakanta shi, domin baka san irin baiwar da Allah yayi mishi ba, tashi yayi dakyar ya fita daka gidan, security din gidan sunyi mamaki da suka ganshi dan sun san bashi da lfya gashi kuma yana tafiya dakyar, bude gate din gidan yayi, wani daka cikin security din yace sir where are you going in dis condition, bai kulashi ba dan bata shi yake ba, fita yayi daka gidan yana tafiya dakyar taxi ya tsayar dakyar ya iya furta mai inda zai kaishi, direct gidanshi aka kaishi zaro kudi yayi wanda bai san ko nawa bane ya bashi sannan ya karasa kofar gidan yana bugawa mai gadin gidan ya leko duk da dare ne akwai haske tako ina, ganin ogan nashi yasa ya fito da sauri yana fadin wlcm sir, baibi ta kanshi ba sai shigewa da yayi,dakinshi ya wuce direct ya fada gado yana hawaye kaman wani karamin yaro, tabbas Allah yakan jarabci bawa ta hanyoyi da dama, bai taba tunanin zaiso indo a rayuwanshi ba, sai gashi lokaci daya Allah yasa mishi azababban sonta tare da kishinta ada idan yaji labarin halin da masoya sukan shiga har haushi yake ji sai yaga kaman karya ne, sai gashi yau ya faru a kanshi, lallai ikon Allah ya wuce wasa, gaba daya ya kuma birkicewa ya koma abun tausayi duk saboda son wacce ya kira yar kauye wacce bata waye ba, gashi sonta na neman hallakashi, ido ya lumshe wanda hawaye ke zuba, tare da burin barin kasar ko zai dan sami sauki domin duk yanda yakai da sonta bazai matsa mata ba, tunda bata bukatar hakan, dakyar ya janyo wayanshi ya kira wata number, kana jin maganan shi kasan yana cikin wani hali, fadi yayi zan sami visa na London gobe nake So, ban san mai aka fada mishi ba ya jefar da wayan gefe tare da lumshe ido kanshi na mishi wani irin juyi.

Koda indo ta shiga daki itama kukan take tayi, wai mai yasa rayuwa yake zuwa mata a haka ne? Da farko nasha wuya wanda ban taba kawo wa zanji dadi ba, sai gashi nayi aure an kaini Gidan mijin da yake guduna yana kyamar nunama duniya ni matarshi ce, ya maidani baiwar kishiyata ya kirani yar aiki a gabanta tasa ni bauta kaman ba gobe, Allah ya kubutar dani daka gareshi mai yasa saida na fara jin dadin rayuwa na yake son fito min da wani bakon abu mai yasa hakan yake faruwa Dani ne...... Kukan da takeyi ne ya kara karuwa..... Dan shuru tayi yayin da wata zuciyar take ce mata haba aysha mai yasa zaki dauka da zafi haka aiko da zaki rama abunda ya miki bai kamata kiyi mai a cikin wannan yanayin ba, karki manta kefa doctor ce dan mai yasa zaki fadama patient dinki kalaman da zai kara samai wani ciwon da sauri ta tashi kaman an tsunguleta fita tayi ta nufi dakin da yake amma baya ciki dan zama tayi dan tana tunanin ko yana toilet jin ta dade a dakin bata ga ya fito ba yasa ta koma dakinta akan da safe zata dawo, koda ta koma kwanciya tayi tana ta juye2 sai tunanin da take tayi yanda zata Kawo karshen abun tun Kafin ya fito fili, lallai dole in fito da koma waye inyi aure duk da bata da burin yin auren a yanzu amma tana ganin hakan shine zai kawo Mata duk wani karshen matsalanta wanda A Majeed yake shirin tsokano mata domin indai harya furta abunda yake ranshi koda Mum bazata bada goyan baya ba, tabbas ita zata bada domin bazata taba gudun wani Abu na Mum ba, yanda take jin Mum babu wani nata da zaice yana son abu a wajanta ta kasa yi domin Mum Mace ce wacce babu irinta koda za'a samu sai ansha wuya, wani hawaye taji yana zubar mata a ido lallai ya kamata tasan abunyi.

Washe Gari da safe Mum ta shiga dakin da d'an nata yake amma bata ganshi ba, zama itama tayi dan tana tunanin ko yana toilet jin shurun yayi yawa yasa ta tashi ta nufi wajan toilet din, ganin babu alaman mutum yasa ta bude taga wayam, cikin damuwa take fadin ina yaje ne haka? Fita tayi a hanya suka hadu da indo tana kokarin zuwa dubashi tayi shiri da alama fita za tayi, Mum duk da tana cikin damuwa tace aysha fita za kiyi tace eh mum an kirani a hspt ne akwai wanda aka Kawo zan duba shi, Mum tace toh Allah ya taimaka, kinga A Majeed kuwa? Indo dan shuru tayi Kafin tace baya cikin dakinshi? Mum tace baya nan, indo taji wani iri amma saita daure tace kodai ya fita ne? Mum tace bari in kirashi shida yake jin jiki ina zashi kuma, kiran layin tayi akace switch off kallon indo tayi tace wayan ma a kashe indo taji wani iri musamman yanda taga Mum din nata, na cikin damuwa, toh ina zashi? Shida yake cikin wani hali ido ta lumshe gaba daya jikinta yayi sanyi, Mum ce ta katseta da fadin bari inje in tambayi security ko sunga fitan shi, tare sukai kasa ita da indo din tambayan security tayi ko sunga A majeed, bayan Sun gaidata ta amsa suke shaida mata jiya da daddare ya fita gashi kuma hjy kaman yana jin jiki sosai wlh, Mum shuru tayi amma ranta a jagule indo itama kasa magana tayi horn din da akeyi yasa aka bude gate din mai girma sanata ne ya shigo da mukarrabanshi, ganin matar tashi a tsaye ita da indo yasa ya fito yana tambaya koh lafiya? Nan Mum ta fada mishi abunda ke faruwa, kiran layin A Majeed din yayi amma a kashe, security dinshi ya tambaya ko akwai mai number din security din dan nashi? Wani yace yana dashi nan ya karanto ma senator bugu daya security din ya dauka tare da fadin Hello waye akan layi cikin turanci, Dad yace mahaifin A Majeed ne, cikin girmamawa kaman yana gabanshi yake gaidashi bayan Dad ya amsa nan yake tambaya koh A Majeed yazo Gida, yace eh amma gskiya sir yana cikin wani hali kaman bashi da lfya sosai wayan a speaker yake duk suna ji indo hawaye taji ya zubo mata da sauri tasa hannu ta goge hawayen Dad ya kashe wayan tare da kallon matar tashi bari inje inga halin da yake ciki, tace suje tare Dad yace ok Mum ta Kalli indo tace kije driver ya kaiki hspt din bari muje muga halin da yake ciki indo kafa babu kwari ta nufi mota driver yaja suma su Mum suka fita zuwa gidan dan nasu.

Koda indo ta karasa asibiti jiki a sanyaye ta shiga ciki, nan aka kawo Mata patient din da zata duba a kan keke kallon mutumin tayi cikin tausayawa tare da kallon wanda yake turashi din ganin yana mata murmushi yasa itama tamai tare da tunanin ina ta sanshi lokaci daya ta tuna da wanda ya biya mata kudin abinci dai2 lokacin wata mata ta shigo Office din daka gani matarshi ce bayanta wani saurayi ne ido indo ta kura mai da sauri ta nufeshi tana nunashi lokaci daya kuma ta rungumeshi wanda mamaki ya hanata magana sai kuka haka shima ta gefenshi yazeed dake gefe yana kallon ikon Allah tare da mamaki a ina tasan Yusuf ga zuciyarshi dake mishi zafi ganin irin runguman da tayi mishi ........

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

145to150

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Chapter 26 · 0% Book details