← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 59

Sashe 22

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mum da indo suna zaune suna fira,mum tace jibi dai za'a fara zuwa office, indo dariya tayi tare da fadin harna kosa in fara Mum na gaji da zama waje daya babu wanda na sani balle inje ziyara, Mum tace ai nima dai zaman naki Gida baya min dadi gwara ki fara aikin ko a can kya samo min siriki na, dai2 lokacin A Majeed ya shigo wanda yaji abunda Mum ta fada fuska tamke ya zauna bayan yayi sallama ciki2 mum ce kawai ta amsa amma ita indo cikin ranta ta amsa, wayanshi yake ta dannawa tunda ya gaida Mum bai kuma cewa komai ba, amma gaba daya hankalinshi na wajan Indo, Mum tace ya kamata kije kiyi shopping abubuwan da zaki bukata Dan nasan masu aiki suna bukatan kayan makeup dasu Turare sabo da shiga cikin al'umma, A Majeed Wanda tunda ya shigo baice musu komai ba sai yazu yace haba Mum miye nayin wani makeup dan mutum zai shiga Al'umma, gwara mutum ya zauna yanda Allah yayi shi bawai yaita ma fuska fenti ba sai mutum ya koma kaman aljani, yana fadin haka yai shiru tare daci gaba da danna wayanshi kaman bashi yayi wannan dogon zancen ba, Mum dan murmushi tayi tare da fadin ai kowa da irin choice dinshi naga wasu masu yin shafe2 din suke So dan sune suke ganin Sun waye, shuru yayi bai kuma cewa komai ba domin yasan Mum magana ta fada mishi, indo da tunda ya shigo falon take a takure tashi tayi tare da fadin Mum bari yau in shiga kitchen, Mum murmushi tayi cikin jin dadi tare da fadin kice yau za muyi dinner da abincin larabawa, dariya tayi wanda saida dimple dinta ya lotsa A Majeed wani irin sonta yake ji yana fisganshi ganin ta shige kitchen duk sai yaji ya takura da zaman, dan tsaki yayi wanda bai san ya fito ba, Mum ce ta daga kai ta kalleshi tare da fadin kai kuma lfya kuwa, yace lfya fuska a tamke irin na shifa asan abunyi Dashi, Mum tashi tayi tabar falon, ganin haka shima yabar gidan gaba daya cikin wani irin yanayi,tuki yakeyi yana tunanin ta hanyar da zai shawo kan Aysha wanda ya lura kaman baya gabanta dan yanda take nuna mishi kaman Dashi da babu duk daya wani iska ya furzar mai zafi tare da daukan wayanshi ya kira Abdul cikin murya irin na wanda baya san magana yace Kana ina? Abdul ya amsa da ina Kaduna dan tsaki yayi tare da kashe wayan, juya kan motarshi yayi ya koma gidan Mum domin in yana ganin indo yana shiga cikin nishadi ko ba komai ganinta na sashi cikin farin ciki da annashuwa, koda ya koma gidan bai shiga ciki ba wajan bukka ya nufa inda yaga wani littafi a wajan an rubuta the doctor, dan shuru yayi bayan ya karanta sunan tare da fadin kenan Dr ce yanzu, wani iri yaji tunawa da a asibiti zata fara aiki ranshi yaji ya baci dan yasan da mutane zata dinga hulda manya da kanana, gashi yasan babu wanda zai ganta bai loraba wani takaici ya kuma ji tunawa da yayi babu aure a kanta, kenan kowa yana da daman yi mata magana, ya dauki lokaci mai tsawo yana sakawa da kullawa jin kiran sallah magrib ne ya gane ya dade a wajan dan haka masallaci ya nufa yaje yayi alwala aka fara sallah, koda aka idar mutane sun fara fita wasu kuma suna nan zaune domin suna jira lokacin sallah isha'i yayi idan sukayi sai su koma gaba daya cikin masu jira harda A Majeed wanda yake ta faman addu'a akan Allah ya mallaka mai aysha a karo na biyu har aka kira sallah aka idar sannan ya fito ya shiga gida, a dinning yaga Mum da indo wacce take cikin wani doguwan riga Red material ne kayan saman ya kamata kasan kuma ya bude, ga dan kwalin kayan ta dan yafe kanta Dashi duk da babu makeup a fuskanta tayi kyau sosai kun san jan abu da karama mutum kyau ido ya bita dashi wanda ta dago suka hada ido da sauri ta kawar da kanta tare dajin haushin hada idon da sukayi, shigo murmushi ya sakar mata da suka hada idon zama yayi akan daya daka kujeran dinning din, Mum tace au dama baka wuce ba?yace eh har na tafi na dawo dan inyi dinner a nan, cikin ran indo tace inda tasan zaiji da batai girkin ba domin bata son duk wani abu da tayi yaci ko ya yaba wani abu nata dan haushi yake bata sosai..... Jin muryanshi tayi yana fadin aysha plz samin abincin ba indo ba harta Mum tayi mamaki indo kaman ba zata sa ba amma ganin Mum a wajan yasa ta tashi tare da zuba mai ta tura mai gabanshi ta kalli Mum tace Mum good night, Mum tace tun yanzu aysha Allah ya tashe mu lfya, daki ta wuce bawai dan tana jin bacci ba kawai dan kar taci gaba da zama da A Majeed ne yasa tabar wajan, koda ta shiga daki tsaki tayi tare dajin haushin zuba mai abincin da tayi, shigo tana barin wajan yaji ya kasa cin abincin danshi ba abincin yake bukata ba ita kawai yake son gani, irin kallon da Mum take mishi yasa ya fara cin abincin yaji dadinshi sosai, harya gama ya tashi tare da fadin Mum bari in tafi in Dad ya dawo a gaida shi, tace OK sannan ya fita da ido Mum ta bishi tana takaicin halin dan nata yau shekara nawa da aure amma har yanzu baida da ko daya, wanda ita koda yaushe burinta bai wuce ace taga jikanta ba,amma tunda haka yake so sai yaje yaita yi.

Indo ce cikin atamfa tayi kyau sosai saman kayan tasa kalan rigan likitoci, dan karamin gyale ta yafa a saman kanta, falo ta fito inda taga Mum tana zaune cikin shiri Mum tace yauwa sai kizo muje in kaiki domin in raka ki zuwa Office, indo tayi dariya cikin jin dadi sannan suka fita, driver ke tuki indo da Mum suna baya har katon asibitin da zata fara aiki, bayan driver ya faka suka fito duk wanda ya gansu zai ce indo yar Mum ce ta cikinta domin irin kyan da suke Dashi, har cikin asibitin suka shiga inda Suka je wajan wanda Dad yace su nema nan ya amshesu da murmushi tare da raka su har Office din indo din, office din babba ne ciki harda dan karamin gadon duba mara lafiya ga AC da TV dake manne sai kujeran zamanta da guda biyu na zama, office din dai irin na Dr babba, indo gefen hawan jini da sugar da zuciya ta karanta, sai yasa Office dinta yake da girma, Mum bayan ta gama gani ta mata murna sannan ta wuce tare da fadin driver zaizo ya dauketa inta gama, nan aka shigo ma indo da file na marasa lafiya babu bata Lokaci tace a fara shigowa, wani tsoho ne ya fara shigowa wanda kallo daya zaka mai ka gane mai arziki ne sai dai ciwo yasa duk ya rame, nan indo ta mishi umarni daya zauna bayan ya zauna tace maike damunshi nan ya fara mata bayani, tana rubutawa harya gama ta fara mai tambayoyi yana bata amsa, wanda yake fada mata dakyar yake tafiya kafanshi ya kumbura, tace yahau gadon dake dakin ya bude kafan ta gani, bayan ya zauna ya bude kafan taga yanda ya kumbura kuma guda daya, Magani ta rubuta mai tare da fadin idan ya kare ya dawo, fita yayi wani ya shigo haka taita duba mutane a ranan ta duba mutane sun kai ishirin, sai wajan 8 ta gama Wanda driver yazo ya dauketa sukai Gida suna shiga A Majeed na shigowa, ganin kayan dake jikinta yasa ya tamke fuska da sauri ya nufeta Kafin ta shiga ciki, tare mata gaba yayi tare da fadin aysha inason magana dake, shuru tamai ba tare data kulashi ba fuskanta a daure, ga kamshin turaren shi da yake tashi, haka shima ta gefenshi jin kamshin turarenta yake yi gaba daya ya fara kashe mishi jiki, cikin wani irin murya ya kira sunanta bata amsa ba sai daka kanta da tayi alaman ya matsa mata ta wuce ido suka hada wanda saida gabanta ya fadi da sauri ta kawar da kanta gefe ta juya da baya zata bar wajan dan bazata iya tsayuwan ba, riganta ya rike ta baya wanda yasa ta tsaya cak......

Taku Maryam obam😘

*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*

*NA*

*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*

*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*

*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*

*WWW.maryamobamnovels.com*

https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/

125to130

*DEDICATED TO....*

*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*

*NGD DA KIRANA DA KUKAYI AKAN LAFIYA BANYI POSTING JIYA BA DA MASU YIMIN MESSAGE DUK NA GODE LAFIYA NA QALAU SAI DAI CIWAN KAI DA YASA NI GABA TUN JIYA HAR YANZU DA NA DAURE DAN INGA NA FARANTA MA MASOYA NA RAI SOSAI NAKE JINKU KAMAN YANDA KUKE KAUNAR NOVEL DINA INA MUKU ONE LUV❤*
Chapter 22 · 0% Book details