Sashe 19
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
A kwana a tashi babu wuya indo ta gama idda, kuma tana zuwa makaranta ta kara kyau da girma sosai komai nata ya fito domin Mum Tana tsaye a kanta wajan gyarata da bata abubuwa masu gina jiki, farin indo na asali ya fito har wani sheki takeyi dan haske, gashi babu laifi tana jin turanci yanzu dan bada wasa take karatun ba, tun Mum da Dad na fishi da dan nasu har suka hakura sai dai tun daka ranan daya rabu da indo bai kuma ganinta ba, sai dai abun yana dan damunshi dan bazai taba manta sanda yaga kirjinta a waje ba har yanzu abun na idonshi ya kasa mantawa duk da kuwa lokacin ana cikin tashin hankali, Abdul yaji abunda A Majeed yayi ya kira indo ya bata hakuri sannan yayi fushi da abokin nashi sosai.
Wasa2 dai indo an kammala karatu anyi waec ta sami 8 credit, nan Mum ta fara mata kokarin fita zuwa Egypt Alhmdlh indo ta sami gurbin karatu a kasar masar wato Egypt inda ta sami medicine duk da indo taso ta karanci political science amma bashi aka bata ba, tare da Mum indo aka daga zuwa kasar misra, wai indo a jirgi first time in history😂 abun mamaki kuma batai kauyanci ba, kodan yanzu an waye ne oho, amma fah ta dan tsorata kawai ta dake ne irin ita Big girl din nan😁 koda suka sauka a kasar Egypt driver yazo ya daukesu nan iyayen Mum sukai ta murnan ganin yar tasu kaman zasu cinyeta dan murna, ummi tana ta jan indo jikinta domin taji tana son indo, haka shima baban ummi din da Mum ke kira da abba, nan sukaci Suka sha, ummi da turanci take ma indo magana dan bata jin larabci, kwanansu biyar suna yawo a Gari kafin Mum ta fara ma indo kuciba2 harta gama mata komai harda islamiya aka saman mata, washe gari driver din su ummi yakai indo ta fara lecture, haka idan ta fito zaizo ya dauketa in zata islamiya ma haka, indo an fara sabuwar rayuwa watan mum daya ta dawo Nigeria, Indo karatu take sosai babu laifi tana ganewa, tayi wata kawa balarabiya mai suna fatima suna shiri sosai indo tana dan jin larabci kadan2 duk da yawanci maganan da turanci sukeyi danko a islamiya ana hada musu da turanci, suna Waya da abdul jefi2.
A Majeed gaba daya ya kasa gane Zainab domin tunda indo tabar gidan rabon da wani abu ya shiga tsakaninshi da Zainab dan tace hala ma wai ya hada jiki da indo din karya shafa mata cuta, wai sai anje anyi gwaji, ganin yana cutuwa yasa ya yarda akayi duk da yana ta rantse mata babu abunda ya faru shida indo din amma taki yarda anyi test bashi da wani cuta, ta dan sakar mai amma ba sosai ba, gashi yanzu ta karo wulakanci sai tabar kasar tayi wajan wata daya bata nan, gashi idan ya mata magana ta inda take shiga ba tanan take fita ba, wata rana tayi tafiya watan ta daya da sati daya tunda ta tafi sau biyu sukai waya shima daka ta dauka sai tace tana aiki zata kirashi idan yaji shuru saiya kirata taki dauka, daka baya ma yaji wayanta a kashe, koda ta dawo ya mata magana wai ita fah Karya takura mata ta fara business ne, ranan hakurin A Majeed ya kare yace mata nifa mijinki ne ina da hakki akanki kin maidani kaman wani hoto, nifa mutum ne ba dutse ba, ina da Sha'awa,tabe baki tayi tare da fadin to ni mai ya dameni da Sha'awan ka? Idan kaji abun ya dameka basai kasha Magani ba, ranshi ya kuma baci yace tunda haka kikace ki sani bana zina kuma ba zaki sa in fara ba ina da bukatar Mace dan haka zan kara aure, wani uban ashar ta saki tare da fadin wlh baka isa ba, karka manta wacece ni, bari in fada maka wacece Zainab yar president babana ne na daya a kasar nan banga wata wacce zan iya kishi da itaba a cikin kasar nan ko wacce iyayenka sukai gigin hadaka da ita fita tayi ta barni, danma ranan mamanka ce ta kwace ta da tayi rayuwa a prison ita da iyayenta yanda babu mai kuma yimin shishigi, ina da kudi ina da ikon da zan hanaka auren ko wace Mace dan haka ka cire wannan abun a ranka ni Zainab ni daya ce matarka a cikin duniyan nan so you have to be very careful akan abunda zaka dinga fada,tana gama fadin haka ta wuce ta barshi zama yayi yana mamaki dama haka Zainab take? Sai yau ya gano abunda Mum take nuna mai lallai yaba Zainab dama da yawa, tunawa da indo yayi nan take yaji nadaman abunda yayi mata lallai wayewa da yawa Bala'i ne, yau yaga illan wayewa wanda gashi matarshi tana nuna kaman itace keda iko Dashi, tuna kalaman abdul yayi da yake cemai yafi son ya auri yar talaka wacce ko mai ya mata zatai godiya ta amsa hannu bibbiyu baya son macen data waye sosai, nan take ya Tuna da maganan Mum da take fadin na maka gata son amma ba zaka gane ba sai nan gaba,.hmmm muje zuwa
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
110to115
*DEDICATED THIS PAGE TO....*
*AYSHA BAGUDO INA YINKI IRIN TOTALLY DINNAN😍*
A Majeed ya dauki lokaci mai tsawo a zaune, tare da tunanin abubuwan da suka faru a baya, Zainab kam tana shiga daki toilet ta fada tayi wanka ta fito ta shirya cikin riga da wando tayi kyau sosai, zama tayi a dakinta Kana ganinta kasan ranta a bace yake tabbas in bata tashi tsaye ba A Majeed yana son ya nuna mata wuyanshi yayi kauri, dan murmushi tayi lallai wannan karan idan da gaske yake muddin ya kara aure sai tasa yayi dana sani, domin tana son mijinta kuma ita daya zata zauna Dashi, har yau tana ganin auren indo da aka bashi a matsayin an mata wulakanci a rasa wacce za'a bashi sai yar matsiyata har yanzu bawai ta kyale indo bane inda zata ganta koh tasan inda take dasai ta koya mata babban darasi yanda babu wata Mace da zatai gigin auran mata miji nan gaba, amma koh yanzu bata baci ba tana jira taga wace mace zai Kawo a matsayin mata inma dagaske yakeyi haka itama taita tunani.
Zabe yazo anyi zabe his excellency yaci zaben senator yanzu su Mum sun dawo abuja da zama, sannan mahaifin Zainab ya kara cin mukamin shi na president domin mutumin kirki ne mai tausayin talakawa, Zainab an kara fasowa gari tare da karo wani sabon wulakanci, yau tana can gobe tana can A Majeed tun yana magana har ya daina yasa mata ido, sai dai abu daya dake damunshi yanda zaiga indo ya bata hakuri akan abunda yai mata dan akwai sanda yaje wajan mum yana bata hakuri akan ta yafe mishi tace ta yafe mai duniya da lahira, yaji dadi sosai yai shuru na wani lokaci sannan yace Mum dan Allah ina zanga aysha?mum tamke fuska tayi tare da fadin ban sani ba, kamo hannun mum yayi tare da fadin Mum plz,mum tace ni bamma gane aysha da kake nufi ba, dan shuru yayi domin yasan Mum ta gane kawai dai so take taji daka bakinshi dakyau, yace Mum matar da kika aura min, Mum tace ban san inda take ba yanzu, may be ma tayi aure jin kalman tayi aure abun ya dan taba shi domin a yanzu yana ji zai iya zama da indo ko dan faranta ma mum da kuma irin hakurin yarinyar tashi yayi ya fita jiki a sanyaye Mum ta bishi da kallo tare da fadin Ai aysha yanzu tafi karfinka kaje ka karata da matarka wacce ta waye
BAYAN SHEKARA HUDU