Sashe 31
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Mum bayan ta shiga dakin taga dady a kusa dashi yana dan mishi fiffita duk da akwai AC a cikin dakin, amma zufa yakeyi, cikin damuwa tace zafi yakeji? Wajan gadon ta nufa taga yanda yake zufa, hannu tasa a fuskanshi Tana share mai zufan fuskan nashi, tare da fadin son, idonshi dake lumshe ya bude, ya kura ma mum din ido, gabanta ne ya fadi ganin irin ramar da yayi lokaci daya, tace mai yake Damunka? Dad yace wannan wani irin tambaya ne fatima bayan kin san komai, tace dan Allah ka bari yaban amsa domin inaso inji da bakinshi kuma cikin hayyacinshi, Dad shuru yayi amma ranshi a bace yake dan gaskiya abun yana matukar damunshi wai tilon dan nashi ne yake kwance babu lafiya gashi yaki bari a kaishi asibiti, duk da ya bayyana matsalanshi amma Mum tana nunawa kaman bata damu ba, lallai komai ya samu danshi laifin Mum ne.... Jin muryan A Majeed ne ya katseshi da yake fadin Mum babu abunda yake damuna Just kawai ina son inbar kasar jibi shine kawai nake So, Dad yace son indai zaka cire komai a ranka a gobe ma zaka sami flight, yace yes Dad plz inason fita london, I need to rest for some month , Dad yace shikenan amma sai kamin promises zaka ga Dr a can? Yace I promise Dad, cikin jin dadi Dad din yace shikenan saika shirya,gobe 6 in d morning zaku tashi, inda badan dare yayi ba da yau zaka tashi, A Majeed yaji dadin hakan duk da zuciyarshi a tunkushe yake yana son ganin aysha ko zaiji dadi sai dai bazai nemeta ba dan Yana son yayi nesa da ita ko hakan zaisa ya Manta da ita, dan lumshe ido yayi yana mai jin zafi a ranshi, Mum kam kasa magana tayi gnin Dad ya fita daka dakin yasa ta kalli dan nata tace mai zaka ci son?kai ya girgiza alaman babu komai, Mum tace haba son ya zaka zauna kana ciwo kaki cin komai, plz tell me mai kke son ci? Yace aysha plz am o.... Bai karasa ba yayi shuru dan jin sunan daya kira Mum din nashi dashi, Mum dan murmushi tayi tare da tashi ta fita daka dakin, tashi yayi dakyar ya nufi toilet, ya dade a ciki sai gashi ya fito da towel a kanshi alaman dai yayi wanka, yana tafiya kaman babu jini a jikinshi domin gaba daya babu kwari a jikin nasa, jallabiya yasa, tare da zama akan gadon kayan aikin indo ya gani da sauri ya kawar da kanshi Dan baya son gninsu dan So yake ya manta da komai nata, duk da yasan hakan ba abu bane mai yuhuwa, kwanciya yayi ta baya yana ganinta a idonshi yana cikin haka Mum ta shigo dauke da tray a hannunta ajiyewa tayi akan Side drawer, tace son tashi kaci abinci koh kadan ne kaji? Tashi yayi yana kallon Mum sannan yace Mum bana jin yunwa, tace Abdul-majeed ka daina horar da kanka, wannan abunda kakeyi bashi zai kawo maka karshen wannan matsalan da kake ciki ba, kallon Mum yayi da sauri ta daga mai kai alaman eh, zaiyi magana tace mai Ya Isa haka tare da bashi Tea din data Kawo mai da snack, amsa yayi ya fara ci tare da tunanin mai Mum ke nufi, suna cikin haka Abdul ya shigo dkin hankali a tashe, ganin A Majeed din yana shan Tea yasa ya sauke ajiyan zuciya tare da fadin kama warke Ashe, karaso wa yayi ya gaida Mum, inda take tambayanshi kwana biyu yace wlh Mum naje Kaduna ne amma wannan karan anyi nasara komai ya daidaita yayar yarinyar Ashe wai Tana tsoran bata mai kudi ne saboda gudun wulakanci dakyar dai aka shawo kan matsalan, ni da farko ma nasha ko rikonta take Ashe yayarta ce, Mum tace toh Alhmdlh yanzu saura musha biki kawai, dariya yayi ba tare da yace komai ba, Mum fita tayi ta barsu,Abdul matsawa yayi kusa da abokin shi, yace kai Man irin wannan rama haka gskiya kaji jiki fah, wai maike damunka ne haka? A Majeed yace aysha, Abdul yace aysha kuma? Kai ya daga mai alaman eh, Abdul dariya yayi tare da fadin wai mai kake nufi ne? Kodai ka sami wata chicks ne, dan tsaki yayi kalan na mai jin jiki, kafin yace kana da matsala Abdul wace aysha nake nufi inba matata ba, abdul yace wannan yar kauyen? Cije baki A Majeed yayi tare da ajiye Cup din Tea din ya kwanta, Abdul yace haba Man magana zaka yi, A Majeed cikin murya irin name jin jiki yace, Abdul joke apart ina son aysha sosai duk wannan abunda nake ciki saboda sonta nake cikinsa, ban taba jin wani abu akan wata Mace ba kaman yanda nakeji akanta, Abdul nayi nadaman abubuwan dana mata duk da a lokacin wani abun bada san raina nake mata ba, dan Allah ka tayani bata hakuri dan nasan zata iya jin maganan ka, bance lallai saita soni ba amma ta yafe min,ta cire komai dana mata a ranta duk irin son da nake mata bazan matsa mata akan dole saita soni ba, dan bazan iya auren macen da bata jin wani abu a kaina ba, am not dat selfish, koda sonta zai kashe ni bazan matsa mata dole ba dat Why na yanke decision akan inbar kasar ko zan manta komai duk da nasan ba abu bane mai sauki, but I will try, domin gaba daya bata san ganina kaman yanda na fahimta indai nesa da ita da zanyi will make her happy, I will do anything just to c her happy .... Dan shuru yayi domin jin zafin da kirjinshi yake yi, Abdul ne ya tabashi tare da fadin karka damu Man zan mata magana and I knw baza tayi rejecting dinka ba, abunda naji dadi shine ka fahimci abunda Mum take nuna maka akan aysha din,wanda tun farko kaki ka fahimta saida lokaci ya kure but i will try inga komai ya koma normal insha Allah....... Toh fah ku biyoni kuji ynda zata kaya...
Taku maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
165to170
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Dan murmushin karfin hali yayi tare da fadin I wish so, abdul yace plz Man kabar maganan tafiyan nan, I promise zan Kawo ma karshen duk wani damuwanka, but saika tashi ka fara komai kaman da zaka sami aysha tunda naga ka fada sosai, wani irin kallo A Majeed yayi mishi tare da fadin bana tunanin haka domin she really hate me, abdul yace kiyayya na zama so ai kaima gashi ka gani tunda gashi ya faru akanka, lumshe ido Am yayi tare da fadin hakane but sai nake ganin kaman...... Abdul ya katse shi da fadin karka damu just kawai kayi Cancel tafiyan ka, A Majeed girgiza kai yayi tare da fadin No Abdul dole inyi tafiyan nan gobe, Abdul Shuru yayi yana tausayin abokin nashi, tashi yayi tare da fadin bari ni zan wuce sai gobe zan shigo, A Majeed yace flight din 6 zanbi zadai muyi waya kawai, abdul yace tare da kokarin fita daka dakin muryan A Majeed yaji yana tambaya ya wannan yarinyar da kake so da ta taraba dinnan, Abdul wani iri yaji amma saiya dake yace tayi aure, yana fadin haka yabar dakin, A majeed gaba daya ya kasa bacci sai juye2 yakeyi tare da tunanin indo wanda yayi kokarin ya cire amma ya kasa.
Haka itama ta gefen indo din sai kaiwa da komowa take a daki, tama rasa maiya kamata tayi, gaba daya kanta ya kulle zuciyarta ta tunkushe da tunani kala2 tama rasa maiya kamata tayi,wani hawaye taji yana zubar mata tare da fadin Allah sarki mahaifiya mai dadi yau inda mahaifiyata na raye da itace zata zamemin abokiyar shawara amma gashi yanzu na rasa mai bani shawara, kwanciya tayi akan gadon dakin tare da lumshe ido, magananta da yazeed ne yake ta dawo mata, a halin yanzu Tana da bukatan hutu wanda Tana ganin yin auren ne zai Kawo Mata Karshen duk wani wahala da take ciki, sai dai kuma Tana da bukatan ta auri wanda take so yake sonta, mai yasa nayi saurin amsa ma yazeed bayan banajin wani abu a kanshi, wata zuciyar tace haba aysha karki Manta da cewa kin amince mai kuma ya yarda da hakan, kodan abunda yama dan uwanki aiya kamata ki soshi, wani hawaye taji yana zubar mata yanzu idan na amince mishi A Majeed fah ya zanyi Dashi? Anya banyi butulci ba, zuciyarta taita tuno mata abubuwan da suka faru a baya, gskiya Mum uwace da babu irinta a kullum ina neman hanyar da zan saka mata da irin abubuwan da tamin na alkhairi a rayuwa na, nan zuciyarta tace inko hakane ki yarda da bukatan danta domin shine babban alkhairin da zaki mata sannan hakan zai sata farin ciki, kaita girgiza tare da fadin Mum hakan bazai sa taji dadi ba tunda ta nuna itama bata sona dashi, kuma ta fadamin hakan, lokaci daya kuma ta tuna maganan da taji Mum da Dad nayi inda Mum ke fadin nima harga Allah ina son aysha da A Majeed sai dai hakan bamai yuhuwa bane, kenan Mum tana sona Da A Majeed? Toh mai yasa ta nunamin a gabana bata sona dashi? Gaba daya kanta ya kulle tama rasa abunyi, ranan dai bacci barawo ne yayi gaba da ita.