Sashe 36
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
Tunda A Majeed yayi sallah asuba bai dawo gidan ba, direct gidanshi ya nufa tare da wasu masu aikin daya dauko dan sumai gyaran gidan, domin yace gwara ya dawo Zainab ta sameshi a nan dan yasan ba kunya ya isheta ba zata iya cewa itama zata biyoshi gidan Mum din nashi duk da yasan Tana shakkar Mum a gabanta bata wani abun, gidan yayi mugun kura da datti haka suka share gidan tare Da cire cottons din gidan suka sa wasu ko ina an gyara yayi fes2 komai dai yana Son gyara, A Majeed ya sallamesu da kudi masu yawa tare dayi musu godiya dan gidan ya koma kaman bashi ba,ga Gida har Gida amma duk yayi kura saboda tsaban kishi ta kori masu aiki, tsaki yayi tare da shiga toilet yayi wanka yasa kananan kaya tare Da feshe jikinshi da turare tako ina, baka jin komai sai kamshi Key din motarshi ya dauka ya nufi gidan Mum, bayan ya karasa yayi horn mai gadi ya bude mai gate ya shiga a falo yaga Mum ita daya Tana breakfast gaidata yayi tare da dan sosa kai dan yana son ya tambayeta aysha amma yana jin kunya kaman tasan abunda yake tunani tace ka duba aysha kuwa? Da sauri yace a'a ya jikin nata? Mum tace da sauki, sama ya haura, mum da kallo ta bishi harya bace mata, sannan taci gaba dacin abincinta, koda ya shiga dakin indo a zaune ya ganta amma tasa blanket ta rufe jikinta daka gani dai sanyi takeji, ganin ya shigo dakin yasa ta kawar da kanta gefe tare da tamke fuska, zama yayi kusa da ita, yana kallonta, juyar da fuskanta tayi ta dayan gefen, abun dariya ma ya bashi amma saiya dake hannunshi ya daura akan kafadarta ya janyota jikinshi, tare da sa dayan hannunshi a wajan wuyanta yaji da zafi, yace aysha ko zamu hspt ne kinga jikin naki har yanzu? Bata kulashi ba sai kokarin fara jan jikinta daka nashi tayi, Amma ya riketa da kyau ta kasa janye jikin a hankali yace haba my baby plz ki tashi in tayaki kishirya muje hspt kinma sha maganin ki kuwa? Ledan Maganin ya gani a gefe ya dauko tare da ciro maganin yaga bata sha ko guda daya ba tun wanda tasha jiya, kallonta yayi tare da fadin haba Baby ya zaki ki shan Magani? Taya zaki warke saketa yayi tare da tashi ya fita daka dakin, jim kadan sai gashi da breakfast, kallonshi tayi tare da kawar dakai tana mamakin irin abubuwan da yake mata wanda tasan tsaban yaudara ne kawai, jinshi tayi kusa da ita yana fadin gashi kici ko kadan ne, daure fuska tayi kalan ka barni dinnan, ganin bata da niyan amsa yasa ya saka mata Cup din a baki, da sauri taja baya dan tea din akwai zafi, hannu tasa a baki tana gogewa shi kuma duk ya rude yana mata sannu tare da fadin bansan zai miki zafi ba, wani irin kallo tamai wnda yasa yayi dan murmushi, tare da fadin gashi kisha toh a hankali, bata Musa ba ta amsa dan bata son yanda yake Mammane mata, kadan tasha sannan ya bata paper chicken kai ta girgiza alaman a'a, yace plz Baby kici kadan plz, kawar dakai gefe tayi ba tare da tace komai ba, magani ya dauko ya bata ta amsa Tana mai jin takaici dan bata san magani ko kadan sha tayi dan Tana ganin zai barta in tasha amma sai taga bashi da niyan tafiya, wayanta dake gefe yayi kara dauka tayi tare da fadin Hello, ban san mai aka fada mata ba naji tace ok gani nan Tana maganan ne irin namai ciwo, shiko A Majeed ido ya kura mata yana kallon ikon Allah, tashi tayi ta shiga toilet jim kadan ta fito ta dauki kaya a wardrobe ta koma toilet, bata dade ba ta fito hada ido sukayi taji gabanta ya fadi tunawa da tayi yanzu Fa mijinta ne dole saida yardanshi zata fita gashi emergency ake nemanta a hspt, kuma bata tunanin zata iya tambayan shi, zama tayi akan kujeran dakin tare da tamke fuska, kallonta yayi tare da fadin mai yasa kika zauna kuma? Ba fita za kiyi ba? Shuru tayi ba tare da tace mishi komai ba, tunanin irin yanda akace mutumin najin jiki ta farayi sai yasa har ta yarda ma zata fita duk da bata jin dadi, toh yanzu ya zanyi in fita? Nidai bazan tambaye shiba dan bana san wani abu Ya hadani Dashi ko kadan shiko A Majeed kallonta yake tayi dan yasan Tana jiran izinin shine kafin ta fita shi kuma yace bazai mata magana ba har sai ta tambaye shi, tashi yayi tare da fadin ban baki izinin fita ba har sai kin tambaye ni, dan haka in Kin shirya tambayan ina bukka yana fadin haka ya fita daka dakin......
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
185to190
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Dan murmushin takaici tayi tare da fadin what did he mean? Tsaki tayi tare da fadin abunda kake So inma bazan yiba, infact ma ai ba tarewa nayi a gidansa ba balle yamin wani iko da Isa, wayanta ne ya kara ringing ta duba taga daka hspt ne kin dauka tayi, harya tsinke, rasa abunyi tayi dan wlh bata ji zata iya ma mishi magana balle harta nemi alfarma a wajanshi, shuru tayi Tana nazari tace yes Mum, tashi tayi ta nufi dakin Mum amma bata ganta ba, gaba daya ta shiga damuwa, jin muryan Mum tayi Tana haurowa daka ji waya takeyi da sauri ta nufi hanyar, Mum na ganinta tace bari zan kira tare da kashe wayan, tace aysha ya jikin? Tace da sauki Mum, Mum tace ina zaki? Tace Mum a hspt ne aka kirani emergency, Mum tace keda bakya jin dadi aysha, Indo dai shuru tayi Mum tace toh kisa driver ya kaiki saiya jira ki gama ya dawo dake, tace toh Mum, tare da fita cikin jin dadi koh ba komai A Majeed zaisha mamaki tunda Mum ta bata izini ai bata da matsala, mota ta shiga driver yaja sukai hspt.