Sashe 54
Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 5 min read
A kwana a tashi ba yuwa cikin indo ya cika wata tara Mum tace a dawo da ita gidan ta duk da baiso hakan ba amma babu yanda ya iya domin baya tsallake umarnin Mum, masu aikinta suke ta hada mata kaya ita kam Tana falo ita da gogan nata ya tamke fuska wai shi a dole baya so ta tafi, hannunta tasa cikin nashi tare da fadin my one plz kabar fushi kasan a gidan Mum zanfi samun kulawa sosai sannan idan Kana wannan fushin sai inga kaman bazan tashi bane inna zo haiyuwa da sauri ya toshe mata baki tare da fadin karki kara irin wannan maganan kin san bazan iya rayuwa ba tare dake ba, dan murmushi tayi tare da fadin haka zaka ce amma ni nasan zaka rayu ko bani danko yaranka zaka so ka rayu, yace aysha plz ki daina min wannan maganan bana son jinta, tashi muje in kaiki murmushi tayi kawai tare da tashi zata haura Sama yace ta zauna bari ya duba ko sun hada kayan haurawa yayi yaga sun gama hada komai yace Su fito Dashi sunkai komai mota sannan ta shiga gefen Zainab wannan ne zuwanta na farko, bayan sun gaisa indo tace Zan tafi gidan Mum nazo muyi sallama idan Allah yasa na tashi toh in kuma ban tashi ba ki rike min yara na amana dan Allah hawaye ne ya zubar mata a ido da sauri ta fita Zainab kam jikinta itama yayi sanyi, ta kasa ko motsi duk yanda takai da kin indo ba zata so ace ta mutu ba burinta kawai tabar mata mijinta, A mota ta sameshi yana jiranta ganin Tana hawaye yasa ya fara fada haba aysha wai miye haka ne mai yasa kike son tadar min da hankali ne plz ki barni haka inji da abun da yake damuna mana, shuru tayi Tana ajiyan zuciya ganin haka yasa ya fara rarrashinta tare da fadin aysha idan Mace zata haiyu bashi bane wai mutuwarta duk da yana da kyau mutum ya dinga Tuna mutuwa koda yaushe irin yanda kike yi yanzu baki san zaki Iya sa rayuwa na cikin wani hali ba aysha koh kin dauka son da nake miki wasa ne, wlh aysha ban taba jin son wata Mace ba kaman yanda nake jin sonki bana tunanin zan iya doguwar rayuwa ba tare dake ba Dan Allah aysha ki bar wannan maganan in baso kike ni in fara tafiya ba, shuru tayi ba tare da tace komai ba jiki ba kwari ya tada motar babu Mai cewa wani abu haŕ suka karasa gidan Mum, bude kofar tayi ta fita shima binta yayi a baya har cikin falon gidan mum na zaune ita da Dad suna fira sai gasu sun shigo mum tace sannu aysha ganin idanta a kumbure gashi yayi ja yasa ta gane tayi kuka tace aysha maiya faru dake haka, A Majeed yace Mum aysha nason sani cikin damuwa tun dazu take ta fadin wai kaman ba zata tashi ba shuru yayi yana hawaye da sauri yabar falon Mum da Dad suka bishi da ido Mum tace haba aysha ki daina fadin haka zaki tashi insha Allah dan murmushi tayi tare da gaida Mum da Dad suka amsa cikin kulawa sannan Mum tace ki zauna mana, zama tayi dakyar tare da tunanin halin da mijinta yake ciki yanzu, a yanda takeji Tana ganin kaman zaiyi wuya ta rayu domin ita tunda ta zama Dr tasan wahalan da mata ke sha wajan haiyuwa take tsoran ta haiyu gashi yanzu haiyuwa yanzu ko anjima ko gobe wani hawaye taji ya zubo mata tare da tausayin yaranta idan akace yau ta mutu bata raye wani irin rayuwa za suyi tunawa da tayi da rayuwanta na baya wanda maraici ne yasa ta haka,shiko A Majeed mota ya shiga amma ya kasa ja sai hawaye da yake ta faman yi sai driver mum ne ya kaishi Gida gefen Zainab ya nufa a falo ya ganta Tana hawaye Tana ganinshi tayi hugging dinshi Tana fadin komai dai lfya koh?wayanshi ne yayi kara dauka yayi yaga Dad ne yace son ka samemu asibiti aysha zata haiyu Da sauri yace toh Dad gani nan kallon Zainab yayi yace zani hspt aysha zata haiyu da sauri tace bari in dauko Gyale muje tare da sauri tayi daki jim kadan sai gata suka fita tare shine mai tukin kaman zai tashi Sama har suka karasa hspt din, koda suka karasa Tana labour room A Majeed gaba daya ya kasa zama haka Mum da Dad Zainab kam kuka takeyi domin ta tausaya mata bata so ta mutu, ta dauki lokaci mai tsawo Tana nakuda amma shuru Dr ce ta fito tace gsky sai an mata Cs dan bazata iya haiyuwa da kanta ba jikinta yayi weak, A Majeed akaba ma takarda yayi signing dai2 lokaciñ Yusuf da zaliha suka zo hspt din gnin irin tashiñ hankalin da suke ciki yasa suka zauna suma amma basu ce komai ba, an Fara shirin aikin indo tayi wani irin nishi mai karfi sai ga yaro ya fado lokaci daya kuma tayi wani nishin yarinya ta fado can kuma ta sake wani sai ga yaro ya kara fadowa lokaci daya kuma ta Saki hannunta komai nata ya tsaya cak.
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
240to245
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*
Taku Maryam obam😘
*💅 TAMBARIN TALAKA 💅*
*NA*
*MARYAM ALHASSAN DAN'IYA*
*🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝*
*{United we stand and succeed;Our ambition is to entertain & motivate the mind of readers}*
*Vote me on wattpat* *@maryam-obam*
*WWW.maryamobamnovels.com*
https://www.facebook.com/kainuwawritersassociation/
240to245
*DEDICATED TO....*
*NAFISA MRS DAN MALIKIN KAWO*