← Book details Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 59

Sashe 3

Tambarin Talaka Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wani makeken gida ne, naga motoci nata shiga, nima dai nace bari inje inga mai akeyi a ciki, motoci sunkai talatin a cikin gidan daka ganin alama taro akeyi a cikin gidan, dan haka nima na kusa kai, wani katon falo na gani fadan tsaruwan falon bata lokaci ne, jin magana nayi kasa2 dan haka na nufi inda nake jiyo maganan, subhanallah wani hadaddan Guy na gani kaman balaraban kasar dubai, wannan daka ganin shi ya hada jini da larabawa, daka gani meeting sukeyi, sun dauki wajan 30mnt sannan mutanan Suka fara fita, wannan Guy din na gani ya tashi ya haura sama wani naga ya bishi yana fadin majeed yaushe zamu je wajan mum ta kirani yakai sau goma, Majeed ya tsaya tare da kallon shi yana fadin kai, abdul wlh kana takura min tun dazu kake min mita ka bari in huta mana, yana fadin haka ya nufi wani daki, bedroom ne dakin babba ne komai na dakin brown ne yayi kyau sosai, rage kayan jikinshi ya fara yi, sannan ya shiga toilet, yayi wajan 30mnt sannan ya fito yana goge gashin kanshi da towel, saida ya gyara gashin nashi sannan yasa wata jallabiya ya kwanta, wayanshi yaga yana haske, tsaki yayi tare da daukan wayan lokaci daya yayi murmushi ganin sunan Mum ne a jikin screen din wayan, dauka yayi tare da fadin Mum cikin shagwaba yake magana, tace son kai nake ta jira, yace Mum am so tired wlh sai yanzu muka gama meeting, ga surutun abdul, Mum tace kai son Abdul dinne yake da surutu, yace eh Mum dazu fah muna hanyar zuwa nan wata yarinya tazo zata shiga mu kuma mun zo wucewa shine ta zubar da kayan kanta, shine wai mu tsaya a biyata, dan na hana driver shine yake ta surutu, Mum tace son ai gaskiya abdul yake fada maka, kaida na sanka da tausayi aiko bakai bane sila ya kamata ka tsaya ku bata kudin asaran da tayi , ganin Mum din kaman itama tana supporting Abdul yasa yace Mum bari in huta anjima zan shigo, murmushi kawai tayi tare da fadin sai kazo......... ku biyo ni domin jin waye majeed

Taku maryam obam😘

💅 TAMBARIN TALAKA 💅

NA
MARYAM ALHASSAN DAN'IYA

15to20

https://www.facebook.com/Maryam-Obam-Novels-441847396162695/

Abdul-majeed d'ane ga governor din Taraba state, mai ci yanzu wanda yake neman kujeran Sanata a halin yanzu, govn Muhammad mutum ne mai tausayi dajin qan na kasa dashi, govn muhd iyayenshi masu kudi ne gaba da baya, ya taso cikin kudi a kasar Egypt yayi karatun sa, inda a nan ya hadu da fatima suka fara soyayya fatima balarabiyar kasar Egypt ce, soyayya suke sosai lokacin da iyayenta Suka sani hankalinsu ya tashi sosai domin basu taba Kawo yarsu zata fada soyayya da wanda badan kasar suba, dakyar iyayenta Suka yarda akayi bikin ganin gudan yar tasu ta nace, haka akai biki na gani da fada, aka kawo fatima Nigeria taraba state,shekaransu biyu da aure Suka haifi abdul Majeed tun yana karami yake dakyau domin sak mahaifiyarshi zaka rantse mahaifinshi ma balarabe ne idan ka ganshi, ga gashi irin na larabawa da yake dashi gwanin ban Sha'awa, tun daka kanshi haiyuwa ya tsayama fatima, duk da abun yana damunta amma mijinta ko a jikinshi ,govn muhd bayan ya gama karatu ya fada siyasa dan abunda ya karanta ma kenan political science, tun daka Chiarman ya fara yaci zabe, yazo dan majalisan taraiya, ganin irin aikin da yake ma Al'umma yasa Suka ce ya fito takaran govn da farko yaki yarda amma ganin magiyan mutane yasa ya yarda cikin ikon Allah kuma ya haye, govn Muhd ya Kawo ci gaba sosai, wanda a yanzu yana neman takaran sanata, A Majeed tun yana yaro iyayenshi suka sangartashi domin shi daya garesu a London yayi karatu kuma a nan ya hadu da yar president mai suna zainab suka Fara soyayya, bayan sun gama karatu Suka dawo suka ci gaba da soyayansu a nan A Majeed yana da taimako da tausayi ga kyauta, bai dade da dawowa ba ya samu appointment daka CVN Central Bank of Nigeria, aka bashi mukamin mataimakin GM tun daka lokacin ya koma abuja da zama, yana yawan zuwa taraba sosai shekaranshi biyu akan mikamin akai bikinsu shida zainab bikin da aka kashe naira kaman babu gobe, Zainab mace ce mai nuna isa da gadara harta masu mata aiki tsoran yi mata laifi suke gata Tana da kishi sosai duk da bawai wani kula da mijin nata take ba, yau Tana can kasar gobe tana wancan kasar duk da abun yana damun A Majeed amma haka yake hakuri domin yana sonta sosai, zainab Tana da Kyau sosai Tana da diri mai kyau uwa uba ga kudi ga babanta president sai yasa take yin abunda take So, ga miji ta samu na nunama tsara domin A majeed namiji ne wanda duk wata Mace za tayi burin samu ga kyau ga kudi ga miskilanci idan kaga yana magana da dariya To shida iyayenshi ne ko abun kaunar shi zainab, amma bai cika magana ba, sai dai akwai kyauta da tausayi,zainab duk wani abu ta samu sai yasa take taka wanda taso, A Majeed yaso su zauna a taraba shida Zainab amma taki gidan daya gina a taraba in yazo a nan yake sauka harta meeting ma in yana Dashi a nan yake yi wani zubin abdul abokin a Majeed ne yaron abokin mahaifinshi ne abdul tare suke aiki a cbn abdul yana jure halin miskilancin A Majeed amma shi bashi da aure wannan kenan.

MUN DAWO KAN LABARI

A Majeed sai wajan 4 ya tashi, toilet ya nufa yayi alwala sallah yayi, sannan ya koma toilet yayi wanka, ya fito yana shiryawa cikin wata riga da wando masu kyan gaske, ya dauki lokaci yana gyara gashin shi, tare dasa Turare kala2, kamshi kawai ke tashi tako ina, kai tsaye ya fito falo abdul ya gani yana cin abinci a takeaway, A Majeed, ya tabe baki tare da fadin yanzu takeaway kake ci ba zaka bari muje gidan Mum ba, Abdul yace sai inyi ta jiranka yunwa ya kashe ni koh? A Majeed ya tabe baki tare da fadin inka ga dama ka fito muje, Abdul tashi yayi yabi bayanshi, A Majeed a baya ya zauna driver yaja motar Suka fita abdul kuma cikin motarshi ya shiga shima ya bisu a baya, kai tsaye wani dangareren gida naga Sun shiga ga sodoji da police makil a wajan gidan, harta cikin gidan ma security ne makil, bayan driver ya faka A Majeed ya fito shima abdul ya bude tashi motar ya fito nan security Suka Fara gaida A Majeed amma ko kallo basu isheshi ba danshi haushin gaisuwan ma yake ji, sai abdul ne ke amsawa, falon gidan yayi Bala'in tsaruwa sosai,wata mata wacce ba zata wuce shekara 45, amma kyan jikinta zaka dauka ba tafi shekara 30 ba, kana kallonta kasan balarabiya ce, Tana zaune akan makeken kujeran falon Tana shan fruit ganin gudan jinin nata yasa ta tashi da sauri tayi hugging dinshi tare da kamo hannunshi ta zaunar Dashi akan kujera kaman wani yaro karami, shi kuma sai kara shagwabe mata yake, abdul dai dariya yakeyi dan inda sabo ya saba da ganin irin son da Mum ke nuna ma dan nata, shi kuma yaita shagwaba kaman dan jariri, Mum tace son ya abuja cikin hausa tayi maganan amma zaka dauka da larabci takeyi, yace Mum lfya, yunwa nake ji, Mum tace tashi muje dinning sai a sannan ta lura da abdul dake ta dariya Mum tace Abdul Ashe tare kuke ban lura ba, ya aiki? Nan ya amsa da lafiya tare da gaida Mum din sannan Suka nufi dinning Mum ce tayi saving dinsu duka, A Majeed cin abincin yake kaman za'a dauke mai,mum kallonshi take tana tausaya mai domin ita dai matarshi bata da lokacin dafa abinci, sai masu aiki wani tym din kuma yaci takeaway indai abinci zaici cikin natsuwa toh yazo taraba ne, bayan Sun kammala Abdul ya mike tare da fadin mum zan koma abuja yanzu, Mum tace Abdul dare zai maka fa, yace wlh Mum ina da aiki sosai gobe, baby Boy ne yasa muka zo taraba wai anan za ayi meeting, A Majeed ya tamke fuska tare da fadin wlh abdul Ka rainani da yawa, kasan ni boss dinka ne wlh idan ka kara cemin Baby boy saina turaka maiduguri course, dariya abdul yayi sosai tare da fadin Mum bari in tafi, mum tace toh ina zuwa danna wani abu tayi kaman remote saiga wata tafito cikin riga da skirt baki kanta babu dan kwali, mum tace Kawo min bucket na dambun nama daya da cake, tace ok your excellence, ba tayi minti uku ba ta Kawo ita da wata, Mum tace Abdul gashi sai kayi taci Allah ya kiyaye hanya, ya amsa da ameen sannan ya Kalli A Majeed daya wani tamke fuska yace A majeed na wuce yace safe journey, sannan ya fita ,nan Mum da dan nata Suka zauna suna ta fira cikin So da kauna.

Indo dai Tana wajan da take Tana kuka, Abdul dake tafiya yaga kaman yarinyar dazu ce,da kayanta ya zube, kaman zai wuce dan bai tabbatar ba, har yayi gaba ya dawo baya, bayan yayi parking ya fito sai yanzu ya gane itace domin roban yana makale a hannunta, yace baiwar Allah lafiya kuwa, bata bashi amsa ba sai kuka da takeyi kanta na mata ciwo, yace ko kurma ce ke, nawa ne kayan naki, cikin sauri ta dago Tana fada mishi, tausayi yaji ta bashi kudin koh 3k bai kai ba, mota ya koma ya dauko 5k ya bata amsa tayi da sauri ko duba yawan kudin ba tayi ba, ta fara fadin ngd tare da rugawa da gudu dan taje gida yana kiranta amma ina tayi nisa.......

Taku maryam obam😘

💅 TAMBARIN TALAKA 💅

NA

MARYAM ALHASSAN DAN'IYA

🌈 KAINUWA WRITERS ASSOCIATION🤝

Vote me on wattpat @maryam-obam

WWW.maryamobamnovels.com

25to30

DEDICATED DIS PAGE TO...

MRS DAN MALIKI

UWAR GIDA SARAUTAR MATA💑 ALLAH YA KARA MUKU SON JUNA KEDA OGA
YA TSOLE IDON MAKIYA👏
Chapter 3 · 0% Book details